Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 21 of 99

*****

Mahmoudu ne ya iske Sultan a gurin shan iskarsa da yamma. Kasancewar shi ma ba shi da iyaka a shiga da fita a gidan Sultan, saboda Hammad, dan haka ganinsa ba wahala yake yi masa ba.
Sai dai yau kasancewar Sultan shikaÉ—ai ne, ya fi sakin jiki da shi.

"Barka da wannan yammaci Sultan"

"Barkanmu dai Mahmoudu, kuna lafiya?"

Ya amsa da "Alhamdillah. Alfarma nake nema daga gare ka Sultan"

"Ina sauraren ka"

"Dan Allah a yi mini izini na ga Imam Hammad ne.

Sultan ya numfasa ya ce "Hammad babu lafiya. Ta so muje ka gani"

Ya tashi cikin ladabi, ya bi bayan Sultan. Suka yi tafiya mai nisa a sashinsa, can cikin wani É—aki suka je ya buÉ—e masa É—akin.
Cikin damuwa ya ce "Mahmoudu ya tabatta Hammad hauka yake yi, haukan ma irin wanda ban taɓa ganin kalarsa ba. Na ce ko a Nigeria da ku ka zauna ya yi irin wannan? Yanzu idan ka je kusa da shi zai iya shaƙe ka, tsawon wannan lokacin bai ci abinci ba, a haka kawai yake"
Cikin tashin hankali ya ce "Yayi ciwo daban-daban, amma ban ga ya yi irin wannan ba, ina kyautata zaton mutum É—aya ne ya san matsalolinsa ciki da waje, ya san bakin zaren wannan ciwon nasa"
"Wane ne? Mahmoudu ba ma son asirinmu ya tonu fa"
"Da asirinmu zai tonu da tuni ta tona, sai dai a zo da Mahaifiyar Muhsin"

AREWABOOKS

Cikin rashin fahimta Sultan ya ce "Ban gane me ka ke nufi ba?"

Cikin girmamawa ya ce "Matarsa da ya zauna da ita a Nigeria, saboda ni kaina na fuskanci wasu abubuwa masu ban mamaki a tsakanin su, bayan sun yi aure." Ya yi maganar yana kallon inda Imam Hammad yake ta mimmiƙewa yana kakari, kamar ana yanka rago.
Cikin damuwa ya ce "Yanzu tun wancan lokacin a haka yake?" Sultan ya jinjina masa kai ya ce "Ko ruwa bai sake sha ba, hankalina a tashe yake. Ga Tafawa ya sako ni gaba a kan Imam Hammad sosai da sosai; Yanzu dai mu je ka yi mini bayani gwari-gwari na fahimta"

Bayan sun fito, suka zauna tare da Mahmoudu.
Mahmoudu ya numfasa ya ce "Idan ban manta ba, bayan mun dawo daga bikin buÉ—e gidan cin abincin Imam na MaraÉ—i, mun dawo ka sanar masa da batun tafiya Damagaran ya wakilceka a taron sarakuna da za a yi a Zinder. Ba zan manta ba an kai ruwa rana sosai a kan tafiyar.
A tsukin lokacin ya kan gaya mini cewa, shi gaba ɗaya ji yake yi baya ƙaunar zaman ƙasar nan, yana jin kamar a cikin wani bala'i da masifa yake. Da fari na zata da wasa yake yi, amma sai na fuskanci da gaske yake a lokacin. Na ce masa mu sanar maka ko ɗaga tafiyar za a yi, amma ya ce mini a'a kar na gaya wa kowa, baya son ya ɗaga wa kowa hankali.
Tare muke kwana da shi a cikin gidan nan, muna shirin tafiya , kawai ya ce mini na same shi a É—aya gidan nasa na kusa da gidan tarihi da yamma, mu yi tafiyar. Na ce masa mu tafi tare amma ya ce mini a'a.

Haka kurum bayan tafiyarsa hankalina ya ƙi kwanciya.
Kawai na kira shi na ce masa yana ina? Ya ce mini ya tafi zagaye can wajen gidan adana kayan tarihi na Agadez. Kawai na hau raƙumi na bi shi.
Sai dai na je gidan adana kayan tarihi na tarar bayanan, aka kira ni da ɓoyayyiyar lamba, aka ce mini an san Imam Hammad nake nema, ya bi cikin sahara. Ba tunanin komai na kewaya bayan gidan inda Sahrar nan take.
Na yi tafiya ta kai ta awa huɗu, saboda ina ganin sahun raƙumi a gurin. A tsakiyar sahara na ci karo da Imam Hammad cikin fita hayyaci a sume. Abin ya bani mamaki, na ciro shimfiɗa a jikin raƙumina, na yi na kwantar da shi na dudduba jikinsa na ga babu wata alama ta ciwo. Na jira ya farfaɗo ko na ɗauke shi mu koma gida.
Cikin ikon Allah ya farfaɗo, na ce masa meyasa ya taho cikin sahara haka? Ko ba shi da lafiya ne?" Ya yi mini shiru. Na ba shi ruwa ya karɓa ya sha.
Na ɗora shi a raƙumina ina mamakin yadda yanayinsa ya canza.
Muka doshi dawowa, sai dai muna nufo Agadez ya din ga wani irin ihu, ya faɗi a cikin sahara daga kan raƙumin ya din ga burgima yana kururuwa. Na sauka na riƙe shi ina tambayar ko lafiya? Amma ba ya iya magana sai ihu kawai.
Hankalina ya tashi na rasa yadda zan yi da shi. Da mun nausa cikin sahara sosai sai ya yi shiru da mun nufo gida, sai ya rikice. Na rasa yadda zan yi ga yamma tana yi. Ba zai yiwu na ɗaukko shi na taho da shi yana wannan kururwar ba kowa yana ganinsa. Kawai aka kira ni da ɓoyayyiyar lambar nan aka ce, kar na dawo Niger da Imam, idan ba haka ba zai yi hauka tuburan ƙarshe ya rasa ransa gaba ɗaya. Na tambayi waye amma ba a bani amsa ba a ka kashe wayar.
Na din ga mamakin waye wannan ya kira ni haka? Kasancewar na ga alamun gaskiya a abin da aka faÉ—a, da na juya da shi yake rikicewa, kawai sai na nufi Nigeria da shi cike da fargaba da zullumi.
Akwai abokan hulaÉ—armu na Nigeria, da muke kasuwancin asuwaki da dabino wanda da yawa ba su san waye ni ba, kuma ba su san Imam ba, kawai sai na neme su a waya. Aka ci gaba da kirana da wannan lambar ana gargaÉ—ina kar na saka a masarauta a san da abin da ya samu Imam Hammad, saboda za a ce dole sai an dawo da shi, idan aka dawo da shi kuma zai rasa hankalinsa da rayuwar sa.
Haka na ɓad da kamanni da ɓoye waye Imam, na shiga da shi Nigeria muka fara neman magani. Sai ya shafe sati bai yi magana ba, ya manta waye shi gaba ɗaya.
Sai dai aka ɓoye lambar asusu, aka din ga turo mini kuɗi cikin asusuna, na ci gaba da harkar safarar dabino zuma da asuwaki tsakanin Nijar da Nigeria, ina tsoron taɓa kuɗin da ake turo mini saboda ban san na waye ba.
Sai dai duk gurin masu magungunan da muka je, sai su ce mu yi haƙuri ba za su iya ba shi magani ba. Mun je gurin masu magunguna daban-daban amma bamu samu magani ba. Ya manta komai nasa da ya shafi Agadez.
Na samu wani gida da abokan hulÉ—ata suke gadi, muka shiga cikinsu.
Zai yi wanka zai ci abinci zai yi salla, amma ba zai yi magana ba sai jefi-jefi. Idan kuma abin ya juyo ba ya ko cin abinci ba ya magana. Sai dai gaba ɗaya al'amuransa sun ƙara rikicewa, ya din ga abu kamar yana gane-gane. Kwatsam aka kawo mahaifiyar Muhsin, ita kuma za ta din ga aikin rainon yaro. Duk lokacin da ya ganta ya kan ƙure ta da idanunsa kamar yana ganin wani abu a tare da ita. Sai da na taɓa tambayarsa ko ya santa ya ce mini a'a amma tana da wani abu da yake nema domin ya tuna waye shi.
Tsawon wannan lokacin ban taɓa gaya masa waye shi ba, saboda fatana ya tuna da kansa kuma kar na yi wani abu, da asirinmu zai tonu ko a cutar da shi.
Kwatsam! Ban san abin da ya faru ba, muka tarar da ita a sume a cikin ɗakinmu, daga ita sai shi. Babu alamun ya yi mata wani abu na cutarwa, sai dai an ce abinci aka bata ta kawo mana ta suma a ɗakin. Mahafinta ya ce ba zai yadda ba ya ce sai ya aure ta. Ba zan ɓoye maka ba Sultan mahaifiyar Muhsin yar masu ƙaramin ƙarfi ce. Aka din ga dambarwa babanta ya ce sai dai Imama ya aure ta. Ina ta lallaɓawa ina bayar da haƙuri, amma ya ce na biya masa sadakin.
Ba ni da ikon yin jayayya da shi, dole aka É—aura musu auren. Sai dai mai kirna a wayar nan ya kira ni, ya sanar mini da ya san batun auren da aka yi wa Imam Hammad.
Tun bayan aurensa da ita, ya fara samun sassauci, ya dawo yana magana, wasu daga halayensa suka canza. Yana kishinta fiye da kima, yana sakin jiki da ita ya yi hira da ita, ya yi wasa da ita abin da ba ya yi ma a rayuwarsa ta nan.
Na sani akwai abin da ta din ga ɓoye mini game da zaman da take yi da shi, duk da nima ban bayyana mata waye shi ba. Amma na san ciwon nan yana motsa masa, duk da na yi mata bayanin ciwon nasa amma iya abin da na sani. Sai dai har aka je aka ɗauke mu daga Nigeria bata taɓa nuna mini yana yin wani abu na irin wannan rashin lafiyar ba. Dan haka ko dai tana da maganin ciwon sa, ko kuma rufa masa asiri ta yi."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.