Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 69 of 99
*****
Nana har wani irin jiri take yi, jikinta yana tsuma saboda tsoro da razanin da ta shiga.
Sultan ya ƙi kallon inda Zahradeen yake, zai ɗauki Muhsin ya tafi da shi, amma ya yi masa tsawa ya ce kar ya taɓa shi.
Gimbiya Bilkisu sam ba ta san me yake faruwa ba, da daddare ta shiryo ta zo sashen Sultan. Yana zaune a gefen gado ya yi shiru, ji yake yi tamkar kansa zai tarwatse.
Muhsin yana kan makeken gadon Sultan yana bacci, gani yake yi idan ya kawar da ido daga kan yaron, shi ma cutar da shi za a yi, wani irin matsanancin tausayin Hammd ya hana shi sukuni. Da ya rufe idanunsa ya tuna abin da ya gani, sai tsigar jikinsa ta tashi.
"Ranka ya daÉ—e, ko nan zan kawo maka abincin daren naka ne, barori sun shirya maka abinci tun É—azu fa" Bai yi magana ba, ta mayar da idonta kan Muhsin ta ce "Wannan kuma a ina ka samo shi?" Ta yi maganar tana nufar gadon.
Cikin tsawa ya ce "Kar ki kuskura ki taɓa shi" Ta razana ta ce "Sultan lafiya?"
"Fita ki bani guri"
Cikin rashin fahimta ta ce "Me yake faruwa ne?"
"Na ce ki fita ki bani guri, ba na ko ƙaunar ganinki, ki fita kafin na ɗauki mummunan mataki a kanki" Babu shiri ta juya ta fice, ganin yadda jikinsa har rawa yake yi, saboda tsananin ɓacin rai. Ta din ga mamakin mene ne ya tayar masa da hankali ne har haka, yake wannan fushin?.
*****
Nana kuwa tun da suka baro gidan tarihin, Sultan ya ce ta zauna a É—akin nan da suke, ta samu nutsuwa.
Da kyar ta samu ta iya yin salla.
Tana zaune ta yi shiru, ta ga an buɗe ƙofar ɗakin, Hammad ta gani ya shigo, ba ta yi zaton ganinsa ba ko kaɗan. Ta miƙe tsaye ya ƙaraso fuskarsa ya zauna a kusa da ita, ya jingina da jikin gado. Sai kuma ya ɗago ya kwantar da kansa a jikinta.
Nana ta ƙara janyo shi jikinta, ta ƙanƙame shi tana fashewa da kuka, wani irin tausayinsa ya mamaye zuciyarta.
"Ya aka yi ne rayuwata, kukan me ki ke yi" Ya furta a hankali yana ƙara shigewa jikinta.
"Sonka kawai nake yi" Ta yi maganar tana kuma ƙanƙame shi.
"Wannan kukan, ya fi kama da na wanda ake tausayawa, meyafaru ki gaya mini"
"Ba komai Sayyid"
"To idan dai kina so na sosai, É—an bani sanyin mana" Yayi maganar yana É—an shafa jikinta yana murmushi.
Jin da gaske kukan take yi, ya sanya ya ɗago, shi ma idanunsa jawur, jikinsa babu ƙwari ya ce "Ki gaya mini, ko wani abin su Sultan suka ce miki?"
"A'a"
"Mene ne?"
"Dan Allah Sayyid duk abin da za a ce maka Asal ta yi, ka yi haƙuri ka yafe mata"
Ya yi murmushi mai ciwo, ya ce "Me Asal É—in ta yi?"
"Na san sai Sultan ya gaya maka, amma dan Allah ka yafe mata"
Hammad ya ce "Ki na tunanin ban san komai ba ne? Lokaci ya yi da yakamata na huta"
Nana ta ce "Wataƙila akwai abin da baka sani ba, dan Allah ko ka sani ka yi haƙuri ka yafe mata"
Ya yi shiru ya sake kwanciya a jikin Nana, ta ƙara ƙanƙame shi, cikin matsanancin tausayawa.
*****
Sultan na kashingiÉ—e, yana sauraren Tafawa, da sauran 'yan majalissa, sun kafe kai da fata a kan lallai a san matakin da za a É—auka a kan Hammad, saboda yadda ya karya musu Al'adar masarauta.
Sultan ya ɗago ya numfasa cikin ƙasaita, kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce "Amm kamar yadda kowa ya sani, Agadez ta gaji Al'adu da ƙa'idoji daban-daban, wanda wasu an samar da su ne, tun zamanin jahiliyyah kafin zuwan addinin musulunci, ina ga lokaci ya yi da yakamata mu kama addininmu, mu yi watsi da duk al'adun da muke ganin su na kawo mana koma baya.
Saboda haka a matsayina na Sultan mai ci na wannan lokaci, na soke wannan Al'ada a ƙasar Agadez. Baƙaƙen buzaye za su samu 'yanci, farin buzu ko buzuwa na da cikakken 'yancin auren duk wata ƙabila ko kalar fatar da yake son aure. Matar da Imam Hammad ya aura, bincikenmu ya tabattar da halattaccen aure suka yi, kuma mun karɓe ta. Hakazalika za mu bayyanawa duniya ɗan da ya haifa tare da matarsa ta Nigeria.
97
1k ne via 0069685771
Aisha Adam stanbic
08081012143
Gaba É—aya 'yan majalisar suka waiwayo suna kallon Sultan.
Tafawa ya ce "Jalaludeen wannan wace irin maganar banza ce, dan me zamu bar gadon al'adun da muka gada daga iyaye da kakanninmu saboda son zuciyarka da ƙoƙarin bawa ɗanka kariya? Babu wanda zai lalata mana dokokinmu da al'adunmu. Dole a hukunta Hammad dai-dai da abin da ya aikata"
"Mutanen farko ma, gadon iyaye da kakanni ne ya halakar da su. Daga lokacin da muka gaji al'adun, zuwa yanzu me al'adar ta haifar mana bayan tarin ɓarna kashi-kashi? Kuma ina bayar da wannan umarni ne a matsayina na Sultan, shugaba a Agadez ba magana nake yi ba a matsayin ɗan uwanku ko abokinku ba, duk wanda ya ɗaga murya ko kawo abin da ba shikenan ba, zan hukunta shi dai-dai da abin da ya aikata"
Matawalle ya ce "Amma Allah ya baka yawan rai, yanke wannan hukuncin haka kai tsaye, baka tunanin zai sanya wa talakawanka wasi-wasi da kawo tashin tashina a tsakanin masarauta da kuma jama'ar gari"
Sultan ya numfasa ya ce "Lokuta da dama, gyara baya buƙatar lallai sai ka yi wa wani daidai, ko kuma sai kowa ya soka, ya yarda da kai mai gaskiya ne ko me kirki ne.
Haka zalika zan sauke wasu daga cikin Imam Imam na ƙasar nan, zan yi wa dokokin Agadez garambawul da gudunmuwar dokokin ƙasar Niger, domin kowane ɗan Agadez ya samu cikakken 'yanci kamar sauran ɗan ƙasa ba tare da al'ada ta tauye wasu daga cikin 'yancin da suke da shi ba a ƙasar nan.
Sai dai na san da yawa ba zai yi muku daɗi ba, za a ga kamar na yi rashin adalci saboda Hammad ɗana ne, amma kafin ku ce haka, bari mu yi komai a buɗe tare da ku". Ya kalli wani dogarinsa, ya ce "Ina da baƙo a mararrabar fada da hanyar cikin gida, ka ce ya iso"
Duk suka yi tsuru-tsuru su na jira.
Ba a jima ba, dogarin ya dawo tare da Sarkin baka sai kuma wannan mai gadi a ɗaɗɗaure da igiya tamau kamar ɓarawo.
Wanda ba su san me ake ciki ba, suka yi ƙuri su na jiran jin ba'asi, wanda abin ya shafa kuma cikinsu ya ɗuri ruwa.
Sarkin baka ya risuna ya yi gaisuwa a fada, cikin shigarsa ta hargi ya shigo hakan ya ƙara sanyawa duk aka zuba masa ido.
Sultan ya kalli Sarkin baka ya ce "Yi musu bayani"
Sarkin baka ya kalle shi ya ce "Duk da na san, sun sanka amma ka yi musu bayanin waye kai"
Ya sunkuyar da kai ya ce "Mai gadin gidan tarihin Agadez"
Sarkin baka ya ce "Kuma me?"
"Boka da nake yi wa wasu daga cikin manyan Agadez aiki"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.