Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 28 of 99
Ta sake cewa "Ka gama rama sallolin ne?"
Ya girgiza mata kai, ta ce "To shikenan, bari na ƙara maka kayan marmarin, zuwa da safe sai ka fara gwada cin abinci" ya jinjina kai ta din ga ɓare masa ayaba yana ci, tana ba shi ruwa yana sha. Sai da ya yi mata nuni da ya ƙoshi.
Ta tashi ta tafi banɗaki domin ta yi alwala ta ji mararta ta ƙulle. Ta tsuguna ta yi fitsari kawai ta ga fitsarin haɗe da jini. Ta shi ta yi cikin tsoro, ta gyara jikinta sai dai ta kasa gane jinin Al'ada ne, ko kuma na ɓari? Tun da dai ya ce mata tana da ciki. Ta kintsa jikinta ta fito, tun da ta fito idonsa a kanta, ta ƙaraso tana cewa "Sayyid, ka ce ina da ciki, yanzu kuma na ga jini ya zo mini, period ne ko ɓari?" Ta yi maganar tana tsare shi da ido, cike da son tabbatar da abin da take zargi.
Kawai ta ga yana murmushi. Cikin rashin fahimta ta ce "To ka yi mini bayani ko da hannu ne, zan gane. Dan Allah cikin ne da ni da gaske ɓari na yi? Ko kuma ba ni da komai dama?"
Ya ci gaba da murmushi yana ƙanƙance idanunsa yana kallonta, kamar ba mara lafiya ba.
Ji suka yi ana bubbuga ƙofa, ya tsuke fuska kamar ba shi ne yake murmushi ba. Mahmoudu ya shigo da kwanukan Abinci. Mamaki ya kama Nana yadda ya iya zuwa da duku-dukun nan.
Ya ƙaraso suka gaisa da Nana, ya kalli Hammad ya ce "Wai ya na ga daga jiya zuwa yau kamar ba kai ba. Ko dama rashin lafiyar ta ta ce?"
Hammad ya É—auki fulon hannunsa zai kai masa duka, amma ya kauce yana dariya. Sai mamaki ya kama Nana, dama yana wasa da Mahmoudu haka? Kodayake ko da suna Nigeria, su na hira amma ba sosai ba, a nan ma tun da ta fara ganinsu tare, duk maganar da zai yi masa cikin girmamawa yake yi masa. Amma kuma yanzu ta ga yana zolayarsa.
Mahmoudu ya ce "Gimbiya ya jikin nasa, duk da daga haka ma Alhamdillah na ga alamun sauƙi a tattare da shi"
Nana ta ɗan ɓata fuska ta ce "Dan Allah ka daina ce mini gimbiyar nan."
"Wallahi dole a ce da mijin Iya Baba Nana, babu wadda ta dace da wannan sunan a kaf Agadez idan ba ke ba. Ya jikin naka?" Ya ƙarasa maganar yana kallon Imam Hammad.
A sanyaye Nana ta ce "Ai maganar ba ta dawo ba tukuna sai a hankali"
"Ikon Allah, kenan dai da gaske bayan tafiyata ya ci gaba da irin wannan ciwon, ni fa na zata tun da muka tafi bai sake yi ba. Amma Nana yaya abubuwa suka kasance ne bayan tafiyata, na san akwai tarin abubuwa marasa daɗi. Na san zuciyar musulunci ce ta sanya ki ke saurarenmu a yanzu ma, amma ki yi haƙuri. Har Nigeria aka je aka kama mu tare da su Sule. Sannan aka zo aka matsa ni da azabtarwa sai da na faɗi inda yake. Aka je gidan da ku ke gadi, ba kwa nan. Na raka su gidanku ina tsoron ya san yana da mata saboda gudun kar a cutar da ke. Ƙaninki ne ya gaya mini inda ku ke. Lokacin da aka je da ni shikaɗai muka tarar a gidan ba kya nan. Wallahi har aka ɗaukko shi sunanki kawai yake kira, yana ba zai tafi ya bar ki ba. Babu halin na faɗi cewa ya yi aure saboda na san hukuncin hakan a masarautar nan. Ga shi aka rufe ni a kurkuku da zargin ni ne na sace shi na kai shi Nigeria saboda ra'ayin kaina. Amma duk abubuwan da suka faru Nana ba su faru dan ni da Imam mu zalunce ki ba, dan Allah ki yi haƙuri"
Tamkar ya sosowa Nana abin da yake yi mata ƙaiƙayi, da dannewa kawai take yi, ta fara hawaye.
Ba Mahmoudu da ya É—aukko maganar ba, shi kansa Imam Hammad sai ya rikice gaba É—aya.
Mahmoudu ya ce "Dan girman Allah ki yi haƙuri, da na san maganar nan, za ta ɓata miki rai da ban ɗaukko ta ba, ki yi haƙuri"
Ta jinjina kai kawai, dan ita kanta ba ta san cikakken dalilin kukan ba, ta san dai tana buƙatar yin kukan ne ta samu afuwa a zuciyarta.
Yau Sultan ne kaÉ—ai ya zo duba Imam, sai dai ya ji daÉ—in yadda ya gan shi. Ya tarar har ya ci abinci ya yi wanka ya canza kaya, sai dai ba magana.
Ya kalli Nana, ƙasan zuciyarsa yana yaba wa ƙoƙarinta da ƙarfin halinta. Ya ce "Kuma zai yi magana, na ga haryanzu bai ce komai ba"
Nana ta sunkuyar da kai ta ce "Zai yi in sha Allah, sai dai wasu lokutan ya kan jima bai ce komai ba, kafin maganar ta dawo"
Sultan ya jinjina kai cike da gamsuwa, ya ce "Muna godiya sosai da sosai. Ko akwai wani abu da ku ke buƙata?" Nana ta girgiza kai alamar a'a.
"To shikenan, idan akwai wani abu, ki sanar da Mahmoudu ya gaya mini. An je za a taho da mai magani ya zo ya duba shi, idan kuma abin ba zai yiwu ba zamu kai shi Asibiti" Nana ta jinjina masa kai kawai.
Inda Allah ya taimaki Nana, akwai pad a cikin kayanta, sai dai yanayin gurin babu gurin discarding pad É—in. Cikin ikon Allah kuma ba ta zubar da jinin sosai.
****
Sultan na zaune a sashensa, ya gama ganin wasu baƙinsa, aka yi wa Asal iso, ta shiga gurinsa.
Bayan sun gaisa ta ce "Abie dama na zo ne ina son duba jikin Imam"
Sultan ya gyara zamansa ya ce "Yarinyar kirki, Imam Hammad yana cikin yanayin da ba zai so a cika kawo masa ziyara ba. Dan haka mu na son ya samu hutu ne, kafin lokacin da za a samo mai maganin da zai duba shi"
Cikin damuwa Asal ta ce "Ko sau É—aya ne Sultan, jiya kwana na yi ina mafarkinsa, ina cikin damuwa ne"
Ya ce "Na ga alamun hakan a tattare da ke, amma ki yi haƙuri ba za ki samu ganinsa ba, zuwa lokacin da zai samu afuwa sai ki gan shi har ma ku koma gida ma"
Ba dan Asal ta so ba, haka ta haƙura ta tashi ta tafi. Tana kan hanya kiran Tafawa ya shigo wayarta.
"Yaya ake ciki?" Ya tambayeta ba tare da amsa gaisuwar da ta yi masa ba.
Ta ce "Yau ba a bani damar ganinsa ba, Sultan ya ce mini jikinsa ya yi zafi, dan haka ba zan samu ganinsa ba. Dole na jira zuwa lokacin da za a samo mai magani ya duba shi"
"Ya dai tabatta haukan yake yi ko? Lokaci ya yi da zan bankaÉ—a abin nan, yadda Sultan zai kunyata daga shi har É—an nasa"
Asal ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, ba hauka yake yi ba, rashin lafiya...
"Ke yi mini shiru, abin da na yanke dole haka za a yi, kar ki sake ki sake yi mini musu" Ya katse ta yana yi mata tsawa da dole ta sanya ta yin shiru.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.