Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 22 of 99

Sultan ya sauke wani irin nannauyan numfashi ya ce "Gaskiya na ji daɗi sosai da yadda ka rufa wasu abubuwan a gaban su Matawalle duk kusancina da su, akwai abin da ba zan so su sani ba. Amma ya aka yi ta san yana Agadez ta zo, nifa ina jin tsoron raɓa ɗa na da wanda zai cutar da shi"

"Allah ya taimake ka, neman Imam ne ya sanya ta baro Nigeria babu wanda ya sani ta taho da tsohon ciki Nijar. A hannun mahaifiyata ta zauna. Duk da ba komai na sani ba, bayan na baro Nigeria, a bakinta za a ji komai. Amma Umma ta ce mini, ta gaya mata rashin lafiya ya yi sosai bayan an É—auke mu daga Nigeria"

Sultan ya jinjina kai ya ce
"Kuma haryanzu baka san waye ya ɓoye lambar yake kiranka ba?" Ya girgiza kai ya ce "Ban sani waye ba, lokacin da aka rufe ni an karɓi wayata, da aka dawo mini da ita ma, ba a sake kirana ba"
Sultan ya É—an yi shiru sannan ya ce "Shikenan, amm zan yi magana da Matawalle, a je a taho da ita, idan ma an mayar da ita Nigeria ne, duk inda take a Nigeria a nemo ta. Amma ko waye yake kiran nan naka, yana da masaniya a kan abin da ya same shi. Amma shikenan"
Mahmoudu ya É—an yi Jimm, yana tsoron a gano Nene ta É—auke ta, dan kuwa ba ya tunanin an sake waiwayar Nana tun da aka ce a je a killace ta, dan da tuni sun farga an baza nemanta, ko dan kar ta je ta faÉ—i cewa ita matar Hammad ce. Sultan ya sallame shi ya tashi ya tafi.
Sultan ya dafe kansa ya yi shiru, saboda yadda al'amura suke ƙara rincaɓewa. Duk tarin yaransa babu wanda yake tausayi kamar Hammad. Kuma yana burin Hammad ɗin ya gaje shi, amma shi ne wanda jarrabawa kala-kala take bibiya.

*****

"Nene, wai wannan naman da nake ta ci kashi-kashi na mene ne, ni gara ki bani hatsi kawai"

Nene ta ce "To mijinki ne ya turo kuÉ—in ciyar da ke, kin ga kuwa dole na baki ingantaccen abinci."

"Ni k ƙyale masa kuɗinsa, kawai lokaci nake jira idan ba ki yi wani abu ba, na je duk bala'in da za a yi, a yi a bani ɗa na, kan na basu mamaki wallahi. Dan ko zan mutu sai na raba su da shi"

Nene ta ce "Ba ma za ki mutu ba. Za ki karɓi Muhsin, ki koma ɗakin mijinki Gimbiya, ina jinjina lamarin Ubangiji Nana, ashe duk wahalar da ki ka sha, duk zaman da muka yi Gimbiya ce ke Nana"

Nana ta ɓata fuska ta ce "Dan Allah Nene ki daina, sai na ji wani banbarakwai, ni Sayyid nake so, ba Imam Hammad ba, ko kaɗan ba na sha'awar wannan gidan. Azabar tension ɗin da na sha a baya ma ta ishe ni, yanzu hutu nake buƙata"

Nene kawai dariya tana girgiza kai, ta ce "Yaro man kaza, Nana na taɓa soyayyar nan fa nima, ba za ki yi mini wani alaye ba. Amma ni da ke mun sha banban. Allah ya zaɓa abin da ya fi alkhairi ".

Nana ta yi shiru, gaba ɗaya magungunan da Nene take bata, bata taɓa kawo na mene ne ba.
Gaba ɗaya tana kwance ta kasa bacci, sai juye-juye take yi, a jikinta take jin yanayinta ya ƙara canzawa fiye da yadda take a baya. Dama lallaɓa rayuwarta take yi a hankali.
Shiru ta yi tana tunanin ko wani hali Muhsin yake ciki?. Sai kuma ta tuna ta ji wayar da Nene ta yi da Mahmoudu a kan cewa, an sanya wa Hammad takunkumin fita. Ta tafi tunanin tun daga wane lokaci ya gane ta, amma ya share ya nuna kamar bai santa ba.
Guntun tsaki ta ja, ta juya zata gyara kwanciyarta. Ta fara jin wannan ƙamshin na ɗakin nan da take ganinta tare da Sayyid yana ratsa hancinta.
"Ina fatan ba da ni ake wannan tsakin ba?" Ba shiri ta buÉ—e idonta, kamar yadda ta yi tsammani a É—akin ta gan su sai dai ya rame sosai da sosai.

Tsiwa ta so yi masa, sai kuma jikinta ya yi sanyi ta ce "Ba ka da lafiya ne?"

"Lafiyata ƙalau, kewarki kawai nake yi, shi ya sanya rame"
Ya tashi zaune ya matsa kusa da kta da ita ya rungumota jikinsa ya ce "Ma vie komai zai wuce in sha Allah, amma kar ki yanke hukuncin haƙura da ni, ba zan iya jurewa ba, ruhina da gangar jikina sun yi mugun sabo da ke, sabon da ba zan iya misalta miki ba" Ya yi maganar yana kwantar da kansa a kafaɗarta. Duk da wata zuciyar na azalzalarta da ta ture kan sa daga jikinta. Amma ya sake riƙo hannunta cikin sanyin jiki ya ce "Ki yi magana ko na ji daɗi mana"

"Sayyid, ci gaba da rayuwa da kai ba zai haifar wa tawa rayuwar É—a mai ido ba, zaren ba kalar yadin ba ne, kuma sama ta yi wa yaro nisa"
"Ban ma gane me ki ke nufi ba, ni duk wata rayuwa da zan yi. Nutsuwata da kwanciyar hankalina na tattare da ke Ma vie" Ta yi masa shiru daga bisani ta ce "Ni fa gaskiya ka yi mini nauyi, ka É—aga ni"

Ya yi murmushi ya ce "Lokacin da ki ke so na, ba kya jin na yi miki nauyin, lallaɓa ni ki ke yi. Asmy"

"Na'am"

"Yanayin akwai zafi sosai, ina buƙatar sanyi"

"Ko fifita ba zaka samu ba, balle wani sanyi"
Sai dai tamkar a zahiri, haka ya ci gaba da lallaɓa Nana, da daɗaɗan kalaman da sai da ta manta da fushin da take yi, ta saki jikinta da shi. Babu tsammani Nana ta farka tana ta ajiyar zuciya. Ta tashi ta zauna ta jingina da bango. Jin yanayinta abin da ya faru ta yi tamkar a zahiri ba mafarki ba.
Ta daÉ—e ba ta yi mafarki makamancin wannan ba. Tana son sanin ainihin abin da yake faruwa take ganinsu a wannan É—akin.
Mararta ta ƙulle ta kifa kanta a kan gwiwoyinta, ta tsorata da ramar da ta ga ya yi, jikinta ya ci gaba da bata yana cikin damuwa.
Ga abubuwan da ta gani a cikin gidan game da shi. Ƙarshe dai kasa komawa bacci ta yi, ga tunanin Ƙaisar da shi ma ba ta san halin da yake ciki ba.

Wayewar garin Allah, haka Nene ta sake zubowa Nana kajin nan da ɗuminsu sai ƙamshi suke yi.
Nana tana ta lissafi da son yin gwajin ciki, domin tabattar da maganar Sayyid, dan sai da ta yi mafarkinsa jiya sannan ma ta tuna. Sai dai tana jin tsoro, ga shi tana jin Kunyar Nene balle ta gaya mata. Yaushe ma za ta fara bayanin ta na da ciki, cikin da ba ta san ya aka yi ya faru ba?.
Tana cikin É—aki tana cin naman nan, ta jiyo muryar Nene na waya.
Mahmoudu ka kiyaye ni da batun Nanan nan fa"

"Dan Allah Umma ki yi haƙuri, zamu shiga matsala sun farga Nana ba ta nan, yanzu haka nemanta ake yi"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.