Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 6 of 99
Ya ce "Ba ke za ki bayar ba, ni zan bayar da kaina, ina fatan hakan ya zame wa Mummy darasi, ya kuma yi silar fitarta daga abin da take aikatawa"
Cikin kuka Jamila ta riƙe hannunsa ta ce "Idan ka yi haka ka kashe kanka fa kenan?"
"Jamila wa zan tunkara ya lalata Wannan abun asirin Mahaifiyata ya tonu tana Kungiyar asiri? Wane kallo ɗan uwanta zai yi mata? Ke idan aka ce ki na kungiyar asiri wane kallo al'umma za su yi miki ko bayan kin tuba? Ina roƙonki dan Allah ki rufa mata asiri kar ki gaya wa kowa wannan maganar" Ya ƙarasa maganar yana tashi tsaye, ya hau tattare kayan.
Rikicewa ta yi tana ƙoƙarin hana shi, amma ya ture ta ya ɗebe, ta riga ta yi masa bayanin duka yadda ake amfani da kayan. Dan haka ya buɗe alawoyin da ta yi niyyar zuwa ta ba wa Muhsin, ya saka a bakinsa.
Ya nufi hanyar fita ya dakata ya ce "Idan na rayu shikenan, idan kuma an yi amfani da jinin nawa, ki tabattar wa Mummy ni ne sadaukarwata na shekara, kuma ki roƙa mini ita gafara, da kuma na zama ni ne mutum na ƙarshe da zai rasa ransa a dalilin nan duniyarta, ta tuna inda na tafi ita ma za ta tafi" Jamila ta yi kuka da dana sanin gaya wa Abba maganar nan.
Yana zuwa ɗakinsa ya ɗau biro da takarda ya yi rubutu, ya caka alluran nan a jikin 'yar tsanar, kawai ya ga ta ɓace daga hannunsa.
Bai razana ba, ya saka hankicin a ƙasan fulonsa.
Bai yadda ya haɗu da Hajiya Sa'a ba, har dare ya yi yana ƙule a ɗaki, ya kwana a kan fulon da jan ƙyallen, wanda shi ma ya ɓace daga baya.
Jamila ta yi kuka tamkar ranta zai fita, dan faɗiwar gaban da ta ji ce ta tabbatar mata da cewa Abba ya aikata abin da ya ce, kuma ƙungiya sun shanye masa jini.
*****
Da ƙyar Abduou matawalle ya yi gyaran murya ya dubi Hammad ya ce "Yanzu Hammad har wuyanka ya yi kaurin da zaka din ga sa in sa da mu? Bamu san ka da haka ba, wannan ba halinka ba ne ba. Kuma ya zama dole a ladabtar da kai bisa nuna rashin ɗa'ar da ka nuna."
"Da na ce mahaukaci ne ai ba a yarda ba, yanzu ga haukan nan yana yi " Tafawa ya yi maganar a harzuƙe.
Cikin nutsuwa Imam ya ce "A cikin hayyacina nake, ina da É—a, ka gaya wa ko a ciki da wajen Agadez "
Sardauna ya dakatar da taron ya sallami kowa banda Imam Hammad, da Abdou matawalle sai kuma Sultan.
Sardauna ya ce "Na san maganganun Tafawa ne suka yi maka zafi ka ke wannan iƙirarin, amma wannan soki burutsun naka, babu abin da zai haifar sai ƙarawa wuta fetur. Kaf faɗin Agadez Asal ce matarka, kuma tun da ku ka yi aure ba ku haihu ba, ko ka na da saɗaka ne bamu sani ba".
"Allah ya taimaki Sardaunan Agadez, ni fa ba ƙarya nake yi ba, kuma ba soki burutsu nake yi ba. Ina da ɗa"
Matawalle ya ce "Wai wani irin ɗa a na zaune ƙalau? Yaushe Asal ɗin ta haihu ba mu sani ba?"
Ya girgiza kai ya ce "Asal ba ta haihu ba, ɗa na kuma ba shi da alaƙa da kowace mace a Agadez a ma Nijar gaba ɗaya"
Sultan da ya fara harzuƙa ya ce "Kai ba na son shashanci fa, zan ci maka mutunci yanzun nan, wane irin shirme ne haka? Ko sai ka gazgata maganar Tafawa cewa baka da hankali"
Cikin girmamawa ya ce "Tuba nake ranka ya daÉ—e, amma idan an bani dama zan yi bayanin komai".
Abduou matawalle ya ce "Mu na sauraren ka".
Ya ciro wayarsa a aljihunsa, ya daddana.
"Ga Balaraba can tana jiran ki, ana neman ki a gidan Sultan" Nana ta ajiye tukunyar da take wankewa, ta kalli Asal ta ce ana nema na kuma a gidan Sultan? Laifi na yi?"
"Idan kin je kya ji. Nima ban san me ki ka yi ba, Imam ne ya ce a kai ki"
Gaba É—aya sai jikin Nana ya yi sanyi, ta kammala abin da take yi a gurguje, ta shirya ta bi Balaraba.
Su na tafe ta ce "Mama Balaraba, ko kin san abin da na yi ake nema na?"
"A'a nifa Gimbiya ce kawai ta ce na raka ki? Amma idan kin san babu abin da ki ka yi, bai kamata ki ɗaga hankalinki ba, wataƙila Imam Hammad ne kawai yake neman ki"
Cikin sanyin jiki Nana ta ce "Kuma a gidan Sultan?"
"Eh wataƙila alkhairi ne, ko kuma girkin za ki yi" Duk da wannan kalaman na ƙwarin gwiwa, da Balaraba ta faɗa wa Nana, ita dai Nana ta ji ba ta gamsu da kiran ba.
Tun daga nesa aka dakatar da Balaraba, aka turo wani ya shiga da Nana.
Nana ta yi turus, bayan ganin manyan mutane har da Sultan a wajen, gabanta ya yi wata mummunar faɗuwa, suka yi mata wani irin kwarjini ta ja ta tsaya a bakin ƙofar tana rarraba idanu.
Su ma duk suka zura mata idanu, su na mamakin ita wannan da aka kirawo, me ya kawo ta nan.
"Ƙaraso mana" Sayyid ya yi maganar yana kallonta. Sai ta diririce ta kasa gaba ta kasa baya.
Da kansa ya fara takawa, yana tunkarar inda take, yana zuwa ya kamo hannunta, yana tafe tana bin sa a baya har zuwa tsakiyar gurin. Bai saki hannunta ba ya kalli idanunta ya ce "Ma Vie"
Gabanta ne ya yi wata irin mummunar faÉ—uwa, tsigar jikinta ta tashi, numfashinta ya fara fita sama-sama, jin abin da ya fito daga bakinsa tamkar almara.
"Ki shaida musu ni ba juya ba ne, ina da yaro"
Ƙoƙarin ja da baya ta fara yi, tare da son fizge hannunta tana girgiza masa kai.
Sardauna ya ce "Imam, wace ce wannan ɗin? Me ka ke ƙoƙarin yi ne haka?"
"Matata ce, ita ta haifa mini yaro" Ya ba shi amsar yana kallon Nana da idonta ya yi ja, ya cika da hawaye.
Cikin rashin fahimta Matawalle ya ce "Ta yaya, wace ce wannan É—in daga ina take?"
Hammad ya yi shiru bai ce komai ba, shi kuwa Sultan tuni ya karaya, bayan ganin asirin Hammad ya tonu na taɓin hankali sa saboda soki burutsun da yake yi.
Sardauna ya ce "Wai Imam kan ka É—aya kuwa? Ita wannan É—in daga ina ka samo ta, ta ina ta zama matarka?"
Matawalle ya dubi Nana ya ce "Ke Baiwar Allah, daga ina? Kuma mene ne alaƙarki da shi?"
Cikin ruɗewa da hawaye Nana ta ce "Ni babu wata alaƙa tsakanina da shi, aiki kawai Gimbiya Asal ta ɗaukko ni na yi mata, ni ban san shi ba"
Hammad ya girgiza kai ya ce "A'a Husnah, kar ki ji tsoro, ina tare da ke. Kar ki yi mini haka dan Allah"
"Dan Allah ka yi haƙuri ni ban san ka ba" Ta yi maganar kuka mai ƙarfi na ƙwace mata.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.