Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 95 of 99

Ƙaisar ya jinjina kai kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce "Haƙiƙa nima tarayyata da ke na fuskanci abubuwa da dama game da rayuwa, kuma ina son baki wasu saƙonni da yakamata bil adam ku sani. Na ƙaru da abubuwa da dama ta ɓangarenki. Tabbas ba na cikin baƙaƙen aljanu, kuma ni musulmi ne, sai dai ban tsaya na fahimci addini yadda yakamata ba, gaba ɗaya na fi mayar da hankalina gurin burina, na sanin magunguna.
Na ji daɗin samun ahalinki, gurin amfani da su, domin baje kolin baiwar da Allah ya yi mini, sai da kash, Duniya ɗaya muke rayuwa da ku, amma tsarin taku rayuwar ya banbanta da namu da cikin ƙiftawar idanu zamani yake canzawa.
A lokacin da ki ka zo, nake farincikin samun cikakkiyar damar ci gaba da ayyukana, ashe lokacin ilimin addini ya daɗe da yawaita, duk da wasu sun rintse idanunsu daga kallon ilimin, su na aikata ɓarna fiye da ta sauran mutanen baya da suka rayu da jahilci.
Rayuwa tare da ke, ya ƙara haska mini juriya a cikin ƙaddara, da taka tsantsan da tsananta imani da Allah. Duk tsanani da zafin ƙaddarar da ka ke ciki. Sannan kasancewaka mutumin kirki, ko mai tsoron Allah baya canza ɗabi'ar duniya ta zama mai adalci a gare ka, ko hakan ya hana Allah ya jarrabe ka. Wasu lokutan jarrabawa ta fi tsananta ma a lokacin da ka fi tsananta addu'a.
Haka zalika idan Duniya za su taru domin su amfanar da kai wani abu, ba za su amfanar da kai komai ba, face abin da Allah ya rubuta maka, haka zalika idan za su taru domin su tauye ka da wani abu, ba za su tauye ka da komai ba face abin da Allah ya rubuta maka. Ban taɓa tsammanin tsakanin ke da mijinki wani ba zai mutu ba, saboda tasirin mugun tsafin da aka yi masa, ni kuma ga haushinki ina ji, ga burin Giyaz na ɗaukar fansa a kan ki.
Haƙiƙa wanda ya dogara da Allah, Allah ya isar masa, ko ba a zo wannan gaɓar ba, ni da kaina zan tafi na bar ki, na yi nesa da ke da zuriyar ki. Zan yi ƙoƙarin shafe duk wani tarihin abin da ya faru a tsakaninmu da zuriyarku, kar a samu wani ya fito daga tsatsona ya nemi sake ɗaukar fansa. Ni kaina zan tafi inda ba a sanni ba, saboda kar wataran na ji na karaya na nemi sake dawowa gare ku, na kasa cika alƙawarin da na ɗauka. Zan ci gaba da neman ilimin addini, zan ci gaba da rubutu, da kuma bincike mai zurfi a kan ilimin sarrafa tsirrai. Sai dai na yi miki alƙawarin zan rubuta labarinki da girmamawa, da alfaharin kasancewarki uwar gijiyata, na fito da kyawawan halaye da kuma ɗabi'unki ababen koyi. Tauhidinki, juriya da kuma gudun Duniya. Zan yi iya yi na na kare wannan rubutu tsawon ƙarnuka, domin ya zama misali mai kyau ga duk wanda zai karanta. Domin zan yi ƙoƙarin nesanta kaina da duk wani abu da zai sanya na shiga harkar bil'adama.
A ƙarshe ina fatan ki sanar da mutanenku, darussan da ki ka koya, a tsawon zaman da muka yi, sannan ki fahimtar da su aikata ayyukan jahilici da duk wani abu da kauce hanya, saboda kana iya shukar da ba za ta fito ba wataƙila sai shekaru masu yawa a gaba, a sanya wanda ba su ji ba, ba su gani ba girbe abin da ba su shuka ba, kamar dai yadda ya faru da ke. A ƙarshe ina yi miki kyakykywan fatan alkhairi, da fatan Ubangiji Allah ya sanya jarrabwoyin da ki ka shiga, su zame miki silar shiga aljanna, Allah ya raya miki yaronki da abin da za ki haifa a gaba ya shirya miki su. Ya baki zaman lafiya da kwanciyar hankali na har abada.
Ina kuma fatan halittun Allah su gane cewa, jinkirin amsa addu'arsu a gurin Allah, baya nufin Allah ba ya son su, kuma zafin ƙaddara da jarrabawa baya nufin Ubangiji yana ƙin ka, sai ka yi duba ga rayuwar annabawa da salihan bayi.
A ƙarshe ina roƙon dan Allah ki yafe mini,  dan na san muddin ba ki yafe mini ba, sai Allah ya saka miki cutar da ke da na yi, ba tare da wata halattacciyar hujja a kan shari'a ba."
Nana na kuka ta ce "Ƙaisar na yafe maka duniya da lahira Allah ya yafe mana gaba ɗaya, Ubangiji Allah ya albarkaci rayuwar ka ya sanya ka cikin salihan bayinsa. Ba zan taɓa mantawa da kai ba har abada"
"Nima ba zan manta da ke ba Asma'u jikar Lanti. Ina fatan za ki yi ilimi mai zurfi ki karanci fannin ilimin magungunan musulunci da na gargajiya "
Nana ta ce "Na yi maka alƙawarin haka. Amma daga nan ina zaka je?"

"Can nesa da Duniyarki, zan nemi ilimi sosai "

"Dan Allah ka tafi da Haula mana, tana matuƙar sonka da ƙaunar ka"

Ya miƙe tsaye yana murmushi, ta ga ya zama wani irin dogo mara misali. Ta ja da baya tana kallonsa. Ta din ga jin muryarsa a sama ya ce "Yi haƙuri, kar na tsorata ki, duk suffar da ki ke ganinmu a cikinta da ni da Giyaz, ba suffofinmu ne na halitta ba, idan muka fito muku a siffofinmu na halitta zaku iya rasa rayukan ku, ko ku zauce. Mu kan suffantu da abubuwa ne da idanunku za su iya kalla. Na gode sosai da sosai uwar gijiyata ina yi miki fatan alkhairi."

"Wayyo Allahana, shikenan ko ziyara ba zaka sake kawo mini ba. Tabbas a kan ka na yarda a sauran halittu akwai bayin Allah na ƙwarai, ba zan taɓa bari a raba ka da rayuwarka ba kai ma. Ina yi maka fatan alkhairi uban ɗakina, kuma ɗan uwana. Na san ba haka kurum Allah ya haɗa ni rayuwa da kai ba, duk da mu na da banbancin jinsi"

Kuka take yi iya ƙarfinta, Hammad yana riƙe da ita gam a jikinsa, sai mimmiƙewa take yi tana ci gaba da kiran Ƙaisar.

"Asmyna, ki yi haƙuri ki daina kukan nan haka" Ta buɗe idanunta a hankali ta kalli Sayyid, ta kalli dattijon malamin nan, ga su Sultan a gefe duk a cikin wani ɗaki. Ta fashe da kuka ta ce "Shi ma an kashe shi ko?"

Ya girgiza mata kai ya ce "A'a yarjejeniya kawai aka yi da shi, ya ce kun riga kun gama magana ma, ya yi miki alƙawarin ya tafi ya rabu da ke har abada"

"Shikenan ba zan sake ganin Ƙaisar ba? Ya cutar da ni, amma... Sai ta kasa magana ta ci gaba da kuka.
"Na sani, na san komai Asmy ki yi haƙuri, mu na da banbancin da ba zai yiwu ki ci gaba da rayuwa da shi" Haka suka din ga rarrashin Nana. Shi kansa malamin ruƙiyyar cewa yayi bai taɓa samun case mai rikitarwa kamar na Nana ba, domin shi kansa Ƙaisar sai da ya yi kuka ba kaɗan ba, kafin ya ƙara tabattar wa malamin ruƙiyyar nan cewar ya bar ta har abada.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.