Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 31 of 99
"Yanzu kin yarda da nake gaya miki ruhinmu a haÉ—e yake? ÆŠaya ba zai iya rayuwa babu É—aya ba"
"Ba wannan nake son ji ba, haryanzu akwai wasu abubuwa ɓoyayyu da ban gama fahimta game da kai ba"
"Komai zai warware a hankali, za ki fuskanci komai rayuwata, amma ba na nufin cutar da ke ta kowace fuska, amma sannu a hankali za ki fahimci abin da ki ke kokwanto a kai."
Ta buɗe idanunta tana ƙarasa jin sautin muryarsa a cikin kunnuwanta. A kan gadon ta gansu tare, fuskarsa na kallon ta ta, yana ta yi mata numfashi a fuska a hankali, wanda hakan ya ƙara dagula mata lissafi dan kuwa ita ta san a zahiri abin ya faru, amma ya rikiɗe ya juye ya koma kamar mafarki. Ga shi yanzu Ƙaisar ba cikakkiyar lafiya ce da shi ba, balle ta ce ko shi ne yake wujijjigata, hakan ya ƙara hargitsa mata tunaninta.
Ta tsura masa ido, kamar a fuskarsa za ta gano gaskiyar abin da take fata.
"Meyafaru?" Sautin muryarsa ya doki dodon kunnuwanta.
Ba ta ce masa komai ba, ta zame jikinta ta juya masa baya, tana ta tufka da warwara a zuciyarta. Sake matsawa ya yi kusa da ita, sai dai wannan karon bai yi magana ba, sai dai jin manufarsa, ya sanya ta zabura da sauri tana ƙanƙame jikinta.
AREWABOOKS
Ƙanƙance idanun ya yi, kasancewar fitilar ɗakin a kunne take, ya din ga bin Nana da kallo, yadda ta tsuke fuska ta sanya hannayenta tana kare jikinta.
"Nana" Ya kira sunanta kamar yadda ake kiranta. Sai ta ji wani iri gaba É—aya babu daÉ—i, ta kalle shi a tsorace.
"Me yasa?" Ya furta a hankali. Ba ta ce komai ba ta sunkuyar da kanta, tana ƙoƙarin matsawa kaɗan.
"Matata ce fa ke? Da gaske kin daina so na ko?"
Ta ce "Ko ina sonka, ba zai yi mini wani amfani ba. Kuma a da ne nake da cikakken 'yanci a matsayin matarka, a Duniyar da nikaÉ—ai ka ke kallo. Wannan duniyar kuma ka yi mini nisa, a yanzu ma na san da na gama amfani za a sallame ni, sake yadda da kai shi ne ganganci mafi muni da zan sake aikatawa"
Ya ɗan fesar da wata iska daga bakinsa ya ce "Ki yi mini alfarma ki bani dama, na san tun da ki ka yadda ki ka sake dawowa kina so na, idan ba kya so na ba za ki yarda ki sake zuwa inda nake ba." Ya riƙo hannunta yana murzawa a hankali ya ce "Ba kya yi mini kwatankwacin son da nake yi miki. Kar ki hukunata ni da abubuwan da ki ke gani a zahiri kawai"
A ɗan ƙufule ta ce "Ka ke son dai wadda ka ke so, ga matar so can kana da ita, wadda al'adarku ta amince ka so ka zauna da ita. Ai ni ina ga sai dai a saka ni a cikin bayi saboda baƙi da muni" Ta ƙarasa maganar tana tashi zaune. Shi ma tashi zaunen ya yi ya ce "A'a ai ni ban faɗi haka ba, ina da farar amma, nake ta bin ki ina lallaɓa ki. Dan Allah ni dai ki yi haƙuri, daga ni har ke mun yi kawar juna, wallahi ba ƙaramin kawaici nake yi ba kasancewata da ke a guri ɗaya" Baki buɗe take bin sa da kallon mamaki da rashin sanin abin yi.
Cike da son tura masa takaici ta ce "Idan ba ka ce ba, amma ai a gabanka ta bautar da ni, ta wulaƙanta ni. Ba ƙaramin tozarta na yi ba da abubuwan da matarka ta yi mini ba. Ka je gurin halattacciyar matarka, da ahalinka suka san da zamanta, ba ni matar ɓoye ba"
Ya ce "Haka ki ka ce?"
"Eh" ta furta cikin tsiwa. Ya zuba mata ido yana kallonta, shi wani irin kyau mata ƙara masa, zuciyarsa har wani harbawa take yi da sauri kasancewarta a kusa da shi. Shi kansa ba zai iya cewa ga adadin abin da yake ji a kanta ba.
A ransa ya ce "Ba komai ki yi yadda ki ke so, kin cancanta" A zahiri kuma sai ya sauka daga kan gadon, ya nufi hanyar fita.
A É—an ruÉ—e ta sauka daga kan gadon ita ma tana faÉ—in "Ina zaka je?"
Bai yi magana ba ya ci gaba da tafiya, bayansa ta biyo da sauri tana faÉ—in "Sayyid ba ka da cikakkiyar lafiya fa, ina za ka je?"
Ya rufa ta a cikin ɗakin, ya tafi. Ta jijjiga ƙofar amma ta ji ƙofar a rufe. Ta koma ta nemi guri ta zauna jikinta a sanyaye tana tunanin, kar wani abin ya same shi.
*****
Tun da É—an da ke cikin Shukura ya faÉ—o Duniya, ta fara ganin duhu, saboda wani irin bleeding da ta din ga yi. Matar da ta kawo ta Asibiti, gaba É—aya a ruÉ—e take, saboda tun da ta haÉ—u da ita ba ta yi magana ba. Ga shi ta kawo ta Asibiti har ta haihu ba ta yi magana ba.
Likitan ya ba ta shawarar ta kira jami'an tsaro ta sanar musu, saboda kar a je wani abu ya faru da ita.
*****
Doctor Sharif kuwa tun da ya farfaɗo ya tashi da shanyewar ɓarin jiki, saboda tashin hankalin yadda ya ci karo da gawar 'yarsa cike da tozarci.
Duk da maganarsa ba ta fita sosai, amma ƙoƙari yake yi ya tambayi ina matarsa, ya jikinta. Amma aka ce masa tana samun sauƙi, sai dai abin da bai sani ba shi ne, bayan tafiyarsa gurin 'yan sanda Allah ya yi mata cikawa.
*****
Matawalle ne tare da Sultan suke tattaunawa, fuskar Sultan fal damuwa yake faɗin "Na rasa abin da na yi wa Tafawa a rayuwa, da yake nuna wa jinina wannan ƙiyayyar haka, abin da ba zan taɓa yi masa ba"
Matawalle ya ce "Ai dama ba halinku É—aya ba sam, ka kwantar da hankalinka mu bi a sannu, in sha Allah zamu samo mafita. Amma kwana biyu yaya ka ke ganin jikin Imam É—in?"
Ya ce "Jikinsa da sauƙi, ana samun ci gaba, sai dai ba ya magana sam. Jiya da yau nima ban shiga ba, ba na son yawan zarya da nake yi musu, kamar yarinyar a tsorace take da mu. Amma na yi mamakin yadda ta iya sarrafa shi ya dawo hayyacinsa."
Matawalle ya ce "Allah ya baka nasara, ni fa ina jin tsoron a sake samun matsala"
Sultan ya ce "Matsalar me fa?"
"Kar a je wani abu ya faru, kana ganin yadda muke fama, ake tunanin yadda za mu ɓullo da lamarin bayyanawa Duniya ɗan gurin Imam Hammad da bayanin da za mu yi a gamsu. Yanzu kuma mun bar shi ya keɓe da ita idan aka kuma samun matsala fa?"
Sultan ya ɗan yi murmushi ya ce "Sai mu karɓi ƙaddara, mu jira ta sake haihuwa. Amma ba na tunanin wani abu ma zai iya faruwa, tun da ba cikakkiyar lafiya ce da shi ba. Kuma mai maganin da aka je ɗaukkowa ne ya ɗan yi balaguro, yana ƙarasa warwarewa za a raba su daga ɗakin, mu ga me ya kamata a yi mata"
Matawalle ya ce "Haka ne, Ubangiji Allah ya ba shi ingantacciyar lafiya.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.