Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 23 of 99

"Su neme ta, me ta yi musu?"

"Babu abin da ta yi, Sultan ne yake son ganinta"

"Sultan, ita ma za a yi mata abin da aka yi mini É—in ne?"

"A'a Umma dan Allah ki yi haƙuri dai, babu wanda ya san inda take. Ni na ce musu na san inda take, yanzu masalaha suke nema. Wallahi an kasa gane kansa gaba ɗaya. Yau kwana na tara kenan yana sume ko ruwa bai shiga cikinsa ba. Dan Allah ki gaya mini kuna ina?"
Gaban Nana ya yi wata irin faɗuwa, ta miƙe tsaye tana sauraren me Nene za ta ce.

"Zan neme ka zuwa anjima, sai na yi magana da ita, idan ta kama sai dai ku bi ta can Nigeria gurin iyayenta, ku roƙo alfarmarsu, ku ɗaukko ta"

"Umma, Nigeria kuma ta koma? Shikenan mun kaÉ—e."

Ta ce "Ka dai saurare ni na ce" Ta kashe wayar. Tana shiga É—akin ta ga Nana a tsaye.
Nene ta ce "Za ki je kenan?" Nana ta yi shiru tana kallon idon Nene.

Nene ta yi murmushi ta ce "Ai ba zan hana ki ba. Ban sani ba ko daga nan ki karɓo takardar sakin naki. Ki haɗa abin da ki ke buƙata, zan kira shi na gaya masa su zo su ɗauke ki" Jiki a sanyaye Nana ta ce "Kina ganin idan na je, ban yi wauta ba ko kuma tarko suka yi mini ba?"

Nene ta ce "Sam, ba na tunanin hakan, ba za a haÉ—a kai da Mahmoudu a yi miki haka ba. Ina yi miki fatan nasara."

Nana ta ce "Nene mu tafi tare mana"

Nene ta girgiza kai ta ce "A'a wace ni, ni da mijina bawa ne, ba sa ƙaunata ba sa son ganina. Ai ke ciwon ido ce, babu yadda suka iya da ke. Mussaman da yake Muhsin a tsakanin ku."

Nene ta yi ba ta ƙwarin gwiwa, Nana kuwa addu'a take yi, da fatan Allah ya sanya ba Giyaz ne ya ci gaba da azabtar da shi ba.

Bayan la'asar sai ga Mahmoudu a wata hamshaƙiyar mota zai ɗauki Nana. Nene ta yi masa kashedi sosai da sosai a kan ya ji tsoron Allah, kar a haɗa kai da shi, a cutar da Nana. Ya yi wa Nene alƙawarin hakan. Nana ta ɗauki kayanta Nene ta raka su har bakin ƙofa, tare da yi wa Nana fatan alkhairi.
A motar Mahmoudu ya ci gaba da ba wa Nana haƙuri ya ce "Idan mun je, kar ki nuna musu fusata ko jin haushin sun ƙwace miki ɗa sun kore ki, bamu san abin da Allah zai yi ba idan mun je tare da ke. Wataƙila rashinki ne a kusa da shi da abin da aka yi miki ya sanya shi a wannan halin. Nana kwanan Hammad takwas ko ruwa bai shiga bakinsa ba, yana sume kawai. Ki yi haƙuri da abubuwan da suke faruwa mu je mu gani ko Allah zai sanya a dace." Nana ta jinjina masa kai, ƙasan zuciyarta tana addu'a.
Ta wata hanya da bata taɓa sanin da ita ba, duk da gidan ba ƙaramin gida ba ne, suka bi. Ya yi parking gurin babu kowa an ƙawata shi da wasu irin dakakkun kujeru na gini da fulawoyi.

Su na bin wata ƙofa suka shiga, sai ga su a sashen Sultan. Nana ta yi shiru ta ga yadda aka yi wa ƙasa ado da dukiya, kamar ba za a mutu a bar ta ba.
Tsahirtawa ta yi da tunanin nata, bayan ganin mutanen da a yanzu ta tsani ganinsu, tun bayan yin ƙarfa-ƙarfar rabata da ɗanta. Sun kame a kan kujeru cikin manyan kayansu da rawani, sai dai sun sauke rawanin fuskarsu tana iya gane kowanne a cikin su. Tuna abin da Mahmoudu ya gaya mata, ya sanya ta daidaita nutsuwarta, ta tsuguna a gabansu ta ce "Ina wuninku" Suka yi shiru ba su amsa mata ba.

Mahmoudu ya ce "Barka da yammaci za ki ce musu"

Ta ce "Barkanku da yammaci, na same ku lafiya?"
Matawalle ya ce "Alhamdillah, sai ki ka ji mun sake neman ki ko?"

Ta ce "Eh, ina fatan ba wani laifin na sake yi ba?"

Ya girgiza kai ya ce "Ba ki yi laifi ba. Alfarma ma muke nema a gurinki"

Ta risuna ta ce "To, Allah ya bani ikon yi"

Ya ce "Kafin nan zan tambaye ki. Ke ce ki ka rayu da shi a Nigeria a matsayin matarsa bayan barinsa Agadez. Shin ko yana yin rashin lafiya mai kama da taɓin hankali, bayan larurar da ya yi na manta ko shi waye?" Nana ta ɗan ɗaga kai sannan ta mayar ta sunkuyar. Ta girgiza ta ce "A'a bai taɓa yi ba" Gaba ɗaya sai suka yi shiru su na kallon ta.

Sardauna ya ce "Ki na nufin bai taɓa wani na larurar rashin lafiyar ƙwaƙwalwa ba?"

Nana ta ce "Eh sai matsalar zuciya da ya yi fama da ita"

Sardauna ya ce "To idan haka ne, babu amfani kawo ta kenan, tun da babu wani haske da za ta iya bamu, ko wani abu da za ta iya yi"

Nana ta risuna ta ce "Dan Allah ina son a bani dama, ko sau É—aya na gan shi, dan Allah"

Sardauna ya ce "A'a, babu buƙatar hakan"

Sultan ya yi shiru yana nazarin fuskar Nana, daga bisani ya ce "Duk da haka, mu je ta gan shi, ko da wani abu da za ta iya yi a kai, ko abinci a samu ya ci"

Matawalle ya ce "Gimbiya Asal ma ta gaza yin wani abu, balle ita?"

Sultan ya miƙe sannan suka tashi. Su na gaba Nana da Mahmoudu su na baya.
Ɗakin kansa an rage hasken fitilun cikinsa, hanyar da suka bi zuwa ɗakin ba zaka taɓa cewa akwai wani ɗaki a gurin ba.

Daga nesa Nana ta hango shi, yana kwance a dunƙule guri ɗaya. Gashin kansa ya baje a ƙasa. Sardauna ya kunna fitilun ɗakin haske ya gauraye ɗakin.
Ziiiiiiiiii ta fara jin wannan sautun, na turnuƙewar ƙurar sahara. Ta tattare nutsuwarta guri guda, ta din ga ambaton Allah. Kawai ta nufe shi. Sardauna zai yi magana Sultan ya hana shi, dan ba a yi wa Nana iznin zuwa inda yake ba.
Ta durƙusa a kansa, ta ga an ɗaure masa hannayensa, jikinsa ya yi jawurr ga wannan hucin zafin da take iya ji, fiye da yadda sauran mutane idan sun raɓe shi suke ji.
Ta hau kiciniyar kwance masa hannunsa. Wata irin miƙa ya yi tana gama kwance masa hannun. Ya miƙa hannunsa wuyanta, da wannan kalar idanun nasa mai ban tsoro. Cikin jarumta da dakiya, ta riƙe hannun nasa ta ce "Sayyid, nice. Ka saurari sautin muryar. Asmy ce ka ayyana addu'a a cikin ranka ko ba zaka iya furtawa ba." Bakinsa ne yake karkarwa yana son ya yi magana.

Ta ce "Ka yi shiru, kar ka yi magana" Ya yi wani yinƙuri ya fizgota jikinsa da ƙarfi.

Ayshercool
08081012143

84
LITTAFIN KUÆŠI NE, KI BIYA KUÆŠIN KARATU KAN KI KARANTA. VIA 0069685771.AISHA ADAM STANBIC
08081012143

Gaba ɗaya suka yi cirko-cirko suna kallon ikon Allah. Tamkar matafiyin da ya shafe tsawon lokaci yana tafiya a sahara ba tare da ci ko sha ba, haka cacumar Nana da wani irin gigitaccen ƙarfi. Haka nan Nana ta ji jikinta babu ƙwari sosai.
"Habu ku bamu guri" Nana ta furta cikin ƙarfin hali tana ƙoƙarin riƙe hannunsa.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.