Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 92 of 99
Ya yi murmushi ya ce "Bayan kin tafi kin bar ni, kewa duk ta dame ni. Jina nake yi kamar maraya. Tabbas Nana ke rayuwata ce, ina roƙon Allah ya bamu jinkirin rayuwa mai amfani tare da ni da ke masoyiyya"
"Amin ya hayyu ya ƙayyum. Ni kaina duk da ina farincikin ganin yan uwana, amma ina kewarka kai da Yarimana"
Hammad ya kalli gefensa da larabci ya ce wa Muhsin "Zo ga Ammi, zo ka gaishe ta"
Muhsin ya matsa kusa da Hammad ya kalli screen ɗin wayar, ya kwaɓe fuska kamar zai yi kuka ya ce "Ammi ki dawo"
Jikinta ya yi sanyi ta ce "Haba yarimana, kar ka yi kuka ka ji, da wuri zan dawo ba zan iya jure ganin ka yi kuka ba" Ya jinjina mata kai.
"Wai zuwa ka yi ka É—aukko shi?"
"Eh mana, karɓo shi na yi aro, muka taho gida, tun jiya ma yana gurina"
Kamar ta yi magana sai ta fasa. Ya ce "Ki kwantar da hankalinki, ban kai mata ɗanki ba, amma dole zan kai shi ta gan shi, ko da kuwa ba ta ƙaunarsa, amma zan yi hakan ne idan ki na nan. Ki zama cikin shiri daga kowane lokaci wataƙila ta nan Nigeria za ki tafi Egypt mu haɗu a can"
"To ai saura kwana uku na taho"
"Eh, za a jinkirta tahowar ne, gara ki tafi ta Nigeria."
Nana ta ɗan langaɓar da kai ta ce "To ai ni ban san ya ake abubuwan ba, kuma idan na zo ina zan yi?"
Yayi dariya ya ce "Idan kin je ba ɓata za ki yi ba, ni zan je na taho da ke"
Sun daɗe su na waya, sannan ta ajiye ta shirya. Tun da Nana ta zo gidan nan abinci mai rai da lafiya ake ci sau ukun nan, kuma duk abin da aka girka har maƙwabta ake kaiwa. Mama ga shi tana cin arzikin nata amma baƙin ciki kamar ya yi ajalinta, da ba 'ya'yanta ne a wannan daular ba.
Gaddafi ma da yake ta shirin aure, shi ne yake kai komo gurin shirin tafiyar Nana Egypt.
Ta gama shirinta, suka fita da Jamila, Baba har mamaki yake yi yadda Nana ta shiga cikin su take rayuwarta, domin shi Jamila tsoro ma take ba shi. Ita kuwa Nana abubuwan tashin hankalin da ta gani a rayuwarta, ba ta ɗauki wata ƙungiyar asiri da Jamila ta shiga da Muhammad ba.
Su na ta sallama a falo babu kowa, can ƙasa-ƙasa suka ji an amsa. Nana ta yi shiru tana tunanin kamar ya san muryar.
Yusra ce ta fito tana amsa sallamar. Tana ganin Nana ta ruɗe ta tafi ta rungume ta, "Ƙawata kece? Ina ki ka tafi ban sake ganinki ba, kowa na yi wa maganar ki, sai a ga kamar shirme nake faɗa".
Cikin mamaki Nana ta ce "Ƙawata me ki ke yi a gidan nan kuma?"
Cikin zaƙuwa ta ce "Ai Sagir ya dawo da ni tuntuni"
"Ma sha Allah, Alhamdillah ya gida ina Hajiya da Siyama?"
"Su na Abuja"
"Ƙawata kin canza kamanni, kin yi kyau kin ƙara ƙiba tubarkallah, ina mijinki buzun nan?"
"Yana Agadez. Ni gidan wata Shukura aka kwatanta mini kuma na zo na ganki"
"To ai ita ma gidanta ne, ba Maman Haidar ba? Mijinmu É—aya bari na kirawo miki ita, ba ta da lafiya ne ma"
Ta juya ta nufi wata ƙofa, Nana ta din ga mamaki.
Jamila ta ce "Ita wannan É—in a ina ki ka santa?"
"Gidan da muka yi gadi, a gidan suke"
Mintuna kusan goma sha biyar, sannan Yusra ta fito, rungume da jariri a hannunta, ga Haidar ya zama saurayi Sagir kuma ya riƙo Shukura tana takowa a hankali.
Nana ta miƙe tsaye, ganin Shukura ta rame sosai ta yi duhu, tana ganin Nana ta fashe da kuka. Cikin sanyin jiki Nana ta nufe ta tana "Faɗin Subhanallah"
"Nana kin gani ko? Ki ka ce mini mafarki ba gaskiya ba ne ba, ni ga shi ya zama gaske Daddy ne ya yi amfani da É—ana ya yi tsafi, Mummyna ta mutu, ya kashe Yusuf ya kashe mahaifiyarmu da babban yayanmu. Nana ban yi dacen uba ba"
Sagir ya ce "Shukura meye haka wai? Wannan ba sirrinki bane da yakamata ki ɓoye ba?"
"Babu abin da zan ɓoye, Nana ta riga ta san komai"
Nana ta rungume Shukura tana kuka ta ce "Kina nufin Yusuf da Hajiya Amina sun mutu? Tayaya mafarki ya zama gaske? Waye ya gaya miki da gaske ya bayar da jaririnki, ba gaskiya ba ne"
Tamkar za ta shiÉ—e ta ce "Wallahi gaskiya ne, shi ya gaya mini da bakins, bayan ya saka an sace ni, da niyyar ya sake kashe mini jaririna"
Jikin Nana ya yi wani irin sanyi, ta tuna Ƙaisar ya ce mata aljanu na iya nuna wa mutum abu a mafarki saboda su haɗa faɗa. Sai dai ga shi abin ya tabatta. Ta rasa tausayin wa za ta fi ji ne? Fadila ko Shukura?
Haka nan ma ta din ga rarrashinta tana ba ta haƙuri, tana tuna yadda ita ma Alhaji Zailani ya sako ta a gaba. Yanzu duk daɗewarsa a duniya, duk tara kuɗin da burin tara arzikin ya tara ya tafi ya bar shi a banza, ga tonon asiri da mummunan ƙarshe, waɗanda ya bari da za su iya yi masa addu'a duk ya bar musu mummunan tabo a zukatansu, da babu lallai su iya yafe masa balle ya samu addu'a.
Ta kalli Haidar ta ce "Ka gane ni Haidar?"
Ya yi murmushi ya ce "Eh Anty Nana ce"
Sagir ya ce "Amma baka gaishe ta ba?"
Ajiyar zuciya da Shukura ta yi, ya sanya Nana mayar da hankalinta kanta, Nana ina ji a jikina nan kusa zan mutu nima, nauyin da ƙirjina yake yi mini da numfashi da nake yi da kyar, na san nima nawa ajalin ya zo. Ki zama shaida idan na mutu kar a ba wa kowa ɗana sai Yusra. Da fari na ɗauki mugun kishi na saka a raina, amma daga bisani abin da Yusra ta yi mini na alkhairi na tabattar da ba kowace kishiya ce kishiya ba, Yusra tana da kyawun zuciya"
AREWABOOKS
Cikin tashin hankali Yusra ta ce "Ka ga zata ci gaba ko?"
Sagir ya ce "Dan Allah Shukura ki daina maganar nan, kina ganin ba ta da cikakkiyar lafiya, tun da ba ta so ki daina dan Allah"
Nana ta matsa kusa da Yusra da tuni manyan idanunta suka tara hawaye, ta kalli jaririn hannunta, ta ce "Wannan naki ne?"
"Na Maman Haidar ne"
"Ma sha Allah"
Kawai Yausra ta miƙa wa Nana hannu tana murmushi. Nana ta kama hannun nata. A take ta ji jikinta ya yi sanyi.
"Haula" Ta furta a hankali.
"Ina yi miki barka da Gimbiyar Agadez, mai É—auke da abin al'ajabi"
Nana ta ce "Haryanzu ba ki rabu da ita ba dama?"
"Ke kin sanmu akwai alƙawari, ina yi miki fatan alkhairi" Ta zare hannunta daga na Nana.
Nana ta dubi Sagir ta ce "Kana nema mata magani kuwa? Ko kaima ka fi yarda da ciwon Asibiti ne yake damunta?"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.