Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 71 of 99
Kamar zata tashi sama, haka Gimbiya Bilkisu ta faÉ—o turakar Sultan hankalinta a tashe, ko haÉ—iyar yawu ta kasa, saboda bushewar da bakinta yayi.
A nutse ya juyo ya kalle ta, bayan ya gama warware rawanin kansa.
Sai kuma ta tsaya ta kasa magana.
Can kuma ta ce "Sultan, wai da gaske zaka sauke wasu daga cikin Imam? Meyasa? Kuma ina fatan babu Zahradeen a ciki?"
"Idan da shi me za ki yi?"
"Amma dai ka san bai kamata abin da ka yi, kuma a kan me zaka sauke Zahradeen yana ɗan cikinka? A wancan karon ka naɗa ƙaninsa a matsayin shugabansa, sannan ka zo ka sauke shi ai muzantawar tayi yawa. Zai ma zama abin surutu a Agadez"
Cikin nutsuwarsa ya kalle ta ya ce "To shi ne me? Ai gara abin kunyar sauke shi daga Sultan, a kan tona muku asiri da ke da shi da ɗan uwanki Tafawa" Ya ƙarasa maganar cikin hasala. Sak ta yi tana ƙwalalo ido waje tana kallonsa.
"Kar ki kalle ni kamar ba ki san abin da ki ka aikata ba, Bilkisu kin cutar da ni, kuma kin cutar da kanki. Kin yi yinƙurin kashe mini mata sau biyu, saboda gudun tonuwar asirinku, yayanki ya yi uwa ya yi makarɓiya ya sanya muka rufe Mamman, waya sani ko a ƙarshe ma ke dai ki ka yi sanadin rayuwar tata? Sannan tilon ɗan da ta bari a duniya ki ka sako a gaba da jaraba, ke kina yi yayanki yana yi, gaba ɗaya Hammad bai ji daɗin rayuwarsa ba, saboda azaba da masifar sihiri da makircinki. Kuma idan ki ka kuskura ki ka buɗe baki ki ka musa mini, sai na tona miki asiri sannan ki bar mini gida. Allah ne ya tona muku asiri a silar matarsa ta Nigeria da ya aura, kuma bokan naku yana hannunmu, ya tabattar da abin da ya aikata.
Abu ɗaya zan duba na rabu da ke, 'ya'yan da na haifa tare da ke. Amma daga yau na haramtawa kaina ke har abada a matsayin matata, za ki yi zaman 'ya'yanki ne kawai. Kuma kar Zahradeen ya ƙara ayyana ni a matsayin mahaifinsa, kuma kar ya sake zuwa inda nake. Da ke da duk wanda ku ka aikata hakan, na bar ku da Allah. Faɗar abin da ku ka aikata tamkar tona wa zuriyarmu asiri ne"
A rikice ta ce "Dan Allah Jalaludeen ka tsaya ka ji...
"Ba zan ji komai ba, fice ki bani guri kafin na canza shawara" Yayi maganar yana yi mata wata irin gigitacciyar tsawa, babu shiri ta fice tana haÉ—a hanya.
Tafawa ne ya shigo falon hankali a tashe, ya tarar da Asal tare da Asadullah.
A fusace ya ce "Gidan uban wa ku ka tafi tun safe?"
Da mamaki Asad ya ce "Kai ka kira ni a waya ai, ka ce na zo na kai Asal Asibiti, tun lokacin muna Asibiti, ba ta da lafiya sosai.
Ya sharce gumin goshinsa ya ce "To, dara ta ci gida yau, Asirinmu ya tonu a fada" Gaba É—aya suka É—aga kai suka kalle shi.
"Eh, yau da bokan da yake yi mana aiki, na gidan tarihi aka zo fada, ya tona komai sunayenmu ne kawai bai kama ba. Kuma na san ya gaya wa Sultan komai, kuma duk a dalilin haukanki da dabbancinki Asal, haka kurum ki ka je ki ka jajubo masifa ki ka kawo ta har cikin gidan sarauta. Binciken da na yi, wannan yarinyar da ki ka kawo a matsayin kuku, ita ce É—in dai ta yi sanadin tona asirinmu. Dan haka sai ku shirya baki É—ayanku, dan ban san wane irin hukunci za a É—auka a kanmu ba.
Asal ta ɗora hannu a ka ta ce "Wayyo Allah na shiga uku, Abbu sai da na ce muku mu daina wannan abin, amma kai ka saka ni, Imam Asad ya saka ni, Imam Omar ma ya saka ni da Sardauna, ku ka saka ni a tsakiya wallahi ina son Hammad, idan na rabu da shi ba zan taɓa samun miji kamarsa ba, wallahi ina sonsa"
A fusace Asadullah ya ce "Ke rufe wa mutane baki, ke ta wani shashasha ma ki ke yi?"
"Kai ne shashasha, dan duk saboda gobenka aka lalata tawa, an cuce ni, komai zan yi yanzu Hammad ba zai taɓa yafe mini ba, balle ya saurare ni"
Tafawa ya dubi Asal ya ce "Asal kina da hankali kuwa? Kin san abin da ki ke faÉ—a kuwa?"
"Abbu na san abin da nake faɗa, shikenan bani da makoma, matarsa ta shiga kundin tarihin baƙar mace ta farko da ta auri Imam a Agadez, ni kuma zan shiga kundin tarihin matar da ta sanya hannun gurin tarwatsa rayuwar mijinta" Miƙewa tayi Tafawa yana kiranta, amma ko waiwayowa ba ta yi ba, ta fice daga ɗakin.
****
Alhaji Fatuhu ne ya yi sallama a falonsa, ga mamaki ya ga Fadila tare da uwargidansa Hajiya Suwaiba, suna zaune abin da bai taɓa gani ba.
Suna ganin shi suka zuba masa ido, Hajiya Suwaiba ta ce "Ka ce sai gobe in Allah ya kaimi zaka dawo?"
Ya ce "Eh, fasawa na yi na taho yau"
Fadila ta ce "Amma Daddy lafiya dai ko, Rauda kawo masa ruwan sanyi"
Suwaiba ta ce "Wai dan Allah Baban Rauda Meyafaru a Lagos É—in ne?"
Ya ce "Sai kun gaya mini, me ku ke tattaunawa ne, ganinku tare ya sanya ni farinciki"
Hajiya Suwaiba ta ce "Abokin nan naka ne ya zo gidan nan, wanda ya sai gidan nan, shi ne muke tattaunawa mu tattara É—an abin da ya yi saura, a nemo gida mu tashi, tun da mun ga alamar mutumin nan zai iya ci mana mutunci daga mu har kai."
Ya yi murmushi tare da jinjina kai. Cikin damuwa Fadila ta ce "Dan Allah Daddy ka gaya mana, meyafaru muna fatan dai ba wani abin ne ya kuma kunno kai ba"
Ya saki murmushi ya ce "Da baku ganni a haka ba, Alhamdillah an canza sabon controller na hukumar Coustom na ƙasa. An sakar mini kwantena Arba'i da bakwai a cikin kwantenonina, da na mutane da na haɗa na yo order kaya" A rikice suka buɗe ido, suna jin abin kamar a mafarki. Hajiya Suwaiba baki na rawa ta ce "Daddy, kenan suna sane suka kama ka kayan naka, ba wani laifin ka yi ba, yanzu kana nufin an saki kayan?"
Ya jinjina kai ya ce "An saki wasu daga cikin kayan, Allah ya karɓi addu'a" Gaba ɗaya suka rungume shi tare da yaransa, yana kuka su na kuka, babu abin da bakunansu ke furtawa sai tsantsar yabo da godiya ga Ubangiji Subhanahu wata'ala mai zaɓar wa kowane bawa abin da ya dace da rayuwarsa.
Baban su Nana ji yayi tamkar ya É—ora hannu a ka ya zunduma ihu, bayan da likita ya sanar masa abin da yake damun Jamila.
Duk da Mama ta roƙe si a kan su rufa musu asiri, amma ganin yadda Baban yake ta sintiri hankalinsa a tashe, an rasa takamaiman dalilin da ya sanya ake ta ƙara wa Jamila jini. Ya sanya ya yi wa Baba bayanin, cikin jikinta da ya zube ne, bai fita gaba ɗaya ba, ga jini ta zubar mai yawan gaske.
A tsorace Baba ya kalli Mama ya ce "Rabi, wane cikin? A ina Jamila ta samu ciki?" Ta tsuru-tsuru tana jin kamar ta kama Likitan ta yi ta gwara kansa a gurin.
"Rabi, dama abin da yake faruwa kenan ki ka ɓoye mini? Jamila da ciki? Kin cuce ni ba ki yi mini adalci ba, kuma ki ka ɓoye mini baki gaya mini ba ki ka nemi kashe ta da ƙwayoyi. Shikenan kanki ki ka yi wa, na fara zargin alhakin Nana ne duk yake bibiyarmu. Nana duk matsi da wahalar da ta sha a rayuwarta bata ɗaukko mini magana ba, ki ka yi mata sharri ki ka saka na amince na aura mata mutumin da ban san waye shi ba, an wayi gari shekara uku, babu ita babu ɗan uwanta, ke kuma naki 'ya'yan babu na mora daga mahaukaciya mai fama da aljanu sai lalattaciya. Abubuwan da ki ke yi wa Nana sharri da kuma yi mata gori a kai, duk sun kama ki a kan yarnki. Amma kanki ki ka yi wa Allah ya yi muku magani" Har ya gama maganar ya fita, ba ta sake iya cewa Uffan ba sai gursheƙen kuka da take yi. Jamila ma da ke kwance sai kukan da take faman yi.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.