Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 7 of 99

"Cika ta tafi" Sardauna ya yi maganar cikin bayar da umarni. A hankali ya saki hannunta, ta juya da sauri ta fice.

"Hammad, anya maganar Tafawa babu ƙamshin gaskiya a cikin ta, na ga baƙa ce kamar ma ba 'yar ƙasar nan ba ce? Meye haɗin ka da ita?"

Ya yi shiru ya sunkuyar da kai ya ƙi magana.

Sultan ya yi gyaran murya ya ce "Ina ga a bari zan yi magana da shi"

Nana kuwa tun da ta fita take kuka, tana zuwa babu kowa a falon, ta wuce ɗakinta ta tattare kayanta cif ta yi waje. Sauri take zumbuɗawa tamkar za ta tashi sama, tana tafe tana fatan Allah ya bata nasarar ficewa daga gidan, ba tare da dakarun Asal sun ganta ba su hana ta fita, kamar yadda suka taɓa yi mata aka hana ta fita daga gidan.
Sai dai ba ƙaramar tafiya ba ce ba, daga sashen da gidan Imam Hammad yake a cikin gidan zuwa shi kansa gidan.
Ta sha doguwar tafiya kafin fita babban gate.

Masu gadin ƙofar suka ƙare mata kallo ɗayan ya ce "Maraɗi za ki tafi ko? Ga mota can Imam ya ce a kai ki"
Ta girgiza cikin mamaki ta ce "Ba zan hau ba, ni ba can zan je ba"

"Idan ba za ki hau ba, ga wannan ya ce a baki" Aka miƙa mata envelope. Ba ta duba meye a ciki ba, ta karɓa suka buɗe mata ƙofa ta fice. Tana tafe tana waiwaye tana fatan kar a biyo ta a mayar da ita gidan nan.
Ta ƙudurce a ranta, tana zuwa gidan Nene za ta ɗauke Muhsin ta yi Nigeria.

Sai dai tana tafe tana kuka zuciyarta cike da takaici, yanzu dama duk tsawon wannan lokacin Sayyid ya gane ta. Amma ya bari take ta wahala saboda shi, ya ci amanarta bai yi mata adalci ba.
Ba ƙaramin gudu motar da ta hau take yi ba, amma gani take kamar ba a sauri.
Ta buÉ—e envelope É—in da aka ba ta kuÉ—i sabbi kar a ciki.
Sai wata takarda. "Dan Allah ki samu nutsuwa, za mu yi magana Asmy, kar ki yanke mini hukunci a yanayin da ki ke" Wani uban tsaki ta ja a fili. Tana furta "Ba ka yi mini adalci ba, ka cutar da ni" Ta yi maganar kaÉ—an-kaÉ—an.

Sun sha tafiya ba kaÉ—an ba a hanya, kafin su isa MaraÉ—i. Daga nan Nana ta nemi abin hawa zuwa garin da suke da Nene. Sai dai tana zuwa ta tarar da gidan a rufe, ga babu waya a hannunta.
Cikin matsananciyar damuwa ta shiga gidan su Ashura.
Ashura na ganinta ta hau tsalle ta rungume ta, Nana ta maze suka gaisa cikin yaƙe.
Suka din ga yi wa Nana maraba da zuwa, mutan gidan su na ta yaba yadda Nanan ta yi haske ta ƙara ƙiba.
Nana da gabanta ke tsananta faÉ—uwa ta ce "Nene fa, ko ta tafi gurin sayar da Abinci?"

"A'a Nene kusan kwana huÉ—u ba ta nan"

Gaban Nana ya faÉ—i, ta ce "Ba ta nan ina ta tafi?"

"Gaskiya ba na tunanin akwai wanda ta yi wa sallama, kawai dai gani muka yi ba ta nan"

"Babar Ashura, dan Allah ku bani aron waya na kira ta" Ta yi maganar cikin tashin hankali, muryarta na rawa.

Aka ba wa Nana waya, ta saka lambar Nene, wayar ta shiga, amma ba ta É—auka ba.
Nana ta kasa zaune ta kasa tsaye, ji take yi tamkar ta kurma ihu, gaba É—aya ta rikice, ta ji numfashinta yana fita sama-sama.
Da kyar ta iya daidaita nutsuwarta ta gabatar da sallolin da suke kanta.
Su ka kawo mata abinci, amma ta ƙi ci, ta yi musu sallama ta ɗauki kayanta ta fice.
Gidan Hajara ta nufa, inda suka kawo ta gidan Nene.
Hajara ta din ga murna ganin Nana, suka rungume juna cikin farin ciki, duk da Nana cikin tashin hankali take.

Hajara ta kawo mata Abinci, ta din ga jan ta da hira.
Nana ta numfasa ta ce "Na je gida gurin Nene, na tarar ba ta nan, ga babu waya a hannuna, ko za ki kira mini ita a wayarki?"

Hajara ta ce "Bari na kira ta"

Sai da aka kira sau biyu, sannan Nene ta É—aga.

Cike da rawar jiki Nana ta ce "Nene"

"Na'am Nana, ki na lafiya?"

Nana ba ta amsa ba ta ce "Nene na zo ba kya nan, na kira wayarki ba kya É—agawa ina ku ka tafi?"

Nene ta numfasa ta ce "Nana ina mai baki haƙuri, baban ɗan ya zo ya karɓi ɗan sa"

Cikin matsanancin tashin hankali Nana ta tashi tsaye ta ce "Nene waye baban É—an? Nene wa ki ka ba wa É—a na? Haka muka yi da ke Nene?"

"Dan Allah Nana ki yi haƙuri, nima fin ƙarfina aka yi, babu yadda na iya, masu garin ne"

"Nene ba ki kyauta mini ba, bamu yi haka da ke ba, dan zatin Allah Nene ki gaya mini inda É—a na yake, dan Allah Nene, ki yi mini rai ki bani É—a na"

Nene ta ce "Nana da zan cutar da ke, da ban zauna da ke tsawon wannan lokacin ba, yadda muka yi a rubuce, haka ya karɓi ɗan sa a rubuce da hukuma, idan na hana su matsala zan shiga"

Cikin rauni da hawaye Nana ta ce "Nene waye ya karɓe shi?"

"Imam Hammad Jalaludeen Agadez "

"Na shiga uku" Nana ta furta cikin matsanancin kuka da tashin hankali.

AREWABOOKS

Cikin tausayawa Hajara ta ce "Dan Allah Nana ki yi haƙuri ki daina kukan nan haka? Kuma wai me yake faruwa ne?"

Nana ba ta saurari Hajara ba, ta ci gaba da kuka, tare da lissafa yadda za ta ninka ta koma Agadez, ta ƙudurce a ranta gara ajalinta ya riske ta, a yi duk wadda za a yi ta karɓi ɗan ta, ko hakan zai yi silar tarwatsewar Agadez gaba ɗaya.', a kan ta tafi ta bar ɗan ta, a wannan gidan.
Bugun ƙofar gidan aka din ga yi da ƙarfi ana sallama.
Hajara ta tashi ta fita, ba a jima ba ta dawo, ta dubi Nana ta ce "Ki na da baƙi a waje"

Nana ta É—ago jajayen idanunta da suka kumbura saboda kuka ta ce "Suwaye?"

"Ki je ki gani, baƙinki ne dai"

Nana ta yinƙura ta tashi ta fita, tana jan ƙafafuwanta, mutum biyu ta gani cikin kaaki, sai ɗaya da rawani, ya rufe fuskarsa sinkif, ba ta ganin komai sai idanunsa, duk da hakan bai hana ta yi masa kallon sani ba. Ba ta tsaya takura wa kanta ina ta san shi ba, saboda matsananciyar damuwa da tashin hankalin da take ciki.
Cikin girmamawa ya ce mata "Barka da wannan lokaci"
"Yauwwa sannu" Ta furta da dasashshiyar muryarta.

"Imam Hammad ne ya aiko mu, ya ce mu tafi da ke"

Ta yi wa mai maganar wani irin mugun kallo ta ce "Ya aiko ku ku tafi da ni ku kai ni ina? Ba zan bi ku ba, babu in da zan je"

"Gurin yaronki za a kai ki" Sai kuma ta yi turus tana kallon su.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.