Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 93 of 99
Ya ce "Haka suka ce mini a gidansu, Asibiti muke zuwa ganin likita"
Nana ta ce "Gaskiya yakamata a yi mata na islamic ma"
Nan ma Nana ta daÉ—e tare da su, sosai Shukura ta ji daÉ—in zuwan Nana, ita kanta Yusra ta ji daÉ—in zuwan nasu.
Nana ta yi wa Shukura alkhairi, suka yi musayar lambar waya, ta tashi suka tafi.
Daga gidan su Yusra, kasuwa suka je, Nana ta yi wa su Jamila sayayya sosai da sosai. Su na tafe a hanya Nana ta ce "Jamila, to kuma da gaske kin iya kasuwancin saye da sayarwar da Hajiya Sa'a take yi, ko kuma ba kasuwancin ku ke ba gaba É—aya?"
Jamila ta ce "A'a tana kasuwancin, na iya"
"To jari nake son baki, ki je ki fara kema, na yi magana da Nasiru ma, da makaranta nake son ya koma, amma ya ce; shi gara na ba shi jari, zai fara sayar da omo da sabulai da ake yi a kasuwa. Dan Allah Jamila idan kin fara Allah ya sanya albarka, ki kula da iyayenmu. Kuma duk abin da ku ke buƙata muddin bai fi ƙarfina ba, ki yi mini waya tun da Alhamdillah inda nake babu abin da zan ce wa Allah sai godiya. Kuma na san ba wayona ko dabara ta ce, ta sanya Allah ya kai ni inda nake ba. Kuma Allah bai tsame ni ya yi mini wannan ni'imar dan ya fi sona ba. Kuma ina fatan a cikinmu Allah ya ƙara ɗaukaka wani, sama da inda nake ni a yanzu" Jamila har da kuka, tare da bawa Nana haƙurin abubuwan da babarsu da su suka yi mata a baya.
"Jamila, idan Allah ya yi wa mutum ni'ima, idan ya yi gaba ba ya waiwayen baya, idan ba alkhairi zai kalla ba, ki manta komai ya wuce kamar ba a yi ba".
Jamila ta yi ta nuna wa Mama kayan da Nana ta saya musu, da batun jarin da za ta bata, amma ta kwaɓe baki. Nana ba ta damu ba, ta yi wa Baba ɗinke-ɗinke.
Gaddafi ya shigo, ya ce "Nana, mun yi waya da mijinki, ya ce bai same ki ba. Ki shirya jibi in Allah ya kaimu, jirgin ƙarfe goma za ki bi, zuwa can Egypt ɗin"
Nana ta ce "Kai da wuri haka, na É—auka za a kai irin kwanakin nan"
Gaddafi ya ce "To ai abin da yake naku ne manya, kuna da alfarma a ko ina, ga shi nan har an yi an gama"
Baba ne ya kalli yadda Mama ke yamutsa fuska, a hasale ya ce "Wallahi Rabi idan ba ki yi wasa ba, baƙin ciki ne zai kashe ki. Duk da abubuwan da ki ka din ga yi wa yarinyar nan, ga shi kina ta cin arzikinta da ke da 'ya'yanki, ba ta yi muku baƙin ciki ba, amma da ta motsa, ta yi wani abin alkhairi ko wani abin alkhairi ya same ta, sai ki kwaɓe baki ko ki kushe"
"Ni kar ka yi mini sharri, me na yi wa Nanan, Allah na tuba me Nana take da shi, da zan yi mata baƙin ciki?"
Baba ya ce "Eh batabda komai, sai abin da yake tukunyarki ki ke ci kika yatsins fuska saboda baƙin ciki"
Takaici ya ishi Nana, ta tashi ta bar gurin.
****
Nana tamkar idanunta su faÉ—o, saboda rarraba idon neman Sayyid. Sai kalle-kalle take yi kamar ma dai a tsorace take.
Fararen fata da baƙaƙe, sai kai wa suke yi suna komowa.
"Kamo ta nan" Yayi maganar yana rungumota, ta zabura a tsorace.
Ya yi dariya ya ce "Matsaoraciya kawai, sai rarraba ido ki ke yi"
"Shi ne zaka tsorata ni, da na yi ihu fa?"
"Sai a yi miki dariya" Yayi maganar yana jan karan hancinta.
Ya miƙa mata hannu suka gaisa, ya ce "Ya mutanen Nigeria su na lafiya?"
Ya ce "Lafiya ƙalau Alhamdillah, su na gaishe ka"
Ya ce "Ma sha Allah, in sha Allah da mun dawo, zamu sake zuwa tare, na gaishe su"
Ya riƙe hannunta, suka shiga taxi suka tafi.
Katafaren Hotel ne, suka sauka a ciki, gaba É—aya Nana jin ta take yi, kamar ba ita ba, kamar mafarki take yi.
Ya yi order Abinci, aka kawo mata, ta yi wanka tayi salla.
Abinci kawai ya iya bari ta ci, ba tare da bata damar hutawa ba, ya ce sai ta biya shi kwanakin da ta yi a Nigeria ba ta nan.
Nana dai da ya ishe ta, kawai ta hau kuka, ya lumshe idanu yana ƙare mata kallo.
Ya yi murmushi ya ce "Ke yanzu dan Allah ba ki ji kunya ba abin da ki ke yi mini?"
"Kai dai za ka ji kunya, haba daga zuwana?" Ta yi maganar tana hawaye.
Ya tashi zaune yana leƙa fuskarta, fafur taƙi kallonsa, ƙoƙarin kare fuskarta take yi, amma yaƙi bata damar hakan. Ya ce "Ni fa zuwan nan namu da biyu, honeymoon muka zo"
"Wane honeymoon, wanda ka yi a Agadez bai ishe ka ba, sai ka dame ni, daga zuwana ni dama ban zo ba"
Hammad ya ce "Gaskiya na Agadez bai ishe ni ba, na fuskanci ƙanin Yarima da rigima ya zo, lokacin Yarima ai ni ake lallaɓawa ina jan aji. Idan kuma ba haka ba, mutum ya musa na tuno wa mutum abin da ya aikata" Murguɗa masa baki ta yi, tana goge hawayen fuskarta. Shi kuwa ya saka ta a gaba, ya din ga yi mata dariya.
Sai da suka shafe kwana uku, da zuwa, har sai da Nana ta manta da abin da ya kawo su, sai dai ta ci abinci Hammad ya yi rigimarsa.
Kwana na huÉ—u suka bar garin da suka sauka, suka tafi garin da malamin yake. Kafin su bar garin, sai da ya zagaya da ita ta ga gari sosai da sosai.
A can garin ma da suka je, a Hotel suka sauka, sai dai a wannan karon ta tarar da Sultan da Matawalle su ma duk su na Hotel É—in kowanne É—akinsa daban amma.
Sultan kamar ya ga 'yar cikinsa, ya din ga tambayarta ya ta baro 'yan uwanta da iyayenta.
Washegari da safe suka hau mota, suka tafi gidan mutumin.
Balarabe ne, sai dai yana jin turanci, tun da suka je gaban Nana ya tsananta faÉ—uwa.
Ya yi musu kyakykyawar tarba, sai dai Nana ko buÉ—e bakinta ta kasa yi, balle ta gaishe shi.
Ya kalli Nana cikin harshen turanci, ya ce "Sannu da zuwa"
Ta sunkuyar da kai ta yi shiru, ta ɓangaren Hammad ma, jikinsa sai tsuma yake yi.
Da larabci suka din ga tattaunawa, Sultan da mutumin, tana iya fahimtar abin da suke faÉ—a amma ba duka ba.
Ya miƙe tsaye ya kalli Hammad, ya ce ya biyo shi, da shi da Sultan.
Nana ta koma gefe ta rakuɓe, ta din ga tunane-tunanen da ita kanta ba ta san daga ina take yin su ba.
Gaba É—aya ba ta cikin nustuwarta, ba ta kuma iya tantance abin da take ji. Wani irin sanyi ya din ga ratsa ta, sannu a hankali ta din ga jin wani irin ihu mara daÉ—in ji.
Ta saka hannu biyu ta toshe kunnuwanta, ta din ga jin tamkar ana ɓarar da kaya, ko ana kokowa da wani irin abu mai nauyi.
Har azahar ta yi, Nana ba ta ga fitowar Hammad ba. Aka bata ruwa ta yi alwala ta yi salla, aka kawo mata abinci, amma ta kasa ci, hankalinta a tashe ba ta ga Hammad ba, ga kuma yanayin da take ji a jikinta mara daÉ—i.
Sai wajen la'asar, sannan aka fito da Hammad, Sultan ya riƙo shi idanunsa a lumshe.
Hankalin Nana ya tashi, ta miƙe tsaye tana faɗin "Lafiya meya same shi?"
Sultan ya ce "Babu abin da ya faru, ki kwantar da hankalinki zai wartsake in sha Allah"
Dattijon nan shi ne mai maganin, ya fito ya jagorance su har wani É—aki.
A ciki aka kwantar da Hammad, sai ajiyar zuciya yake yi, jikinsa yayi jawur hatta gashin kansa a hargiste, rawaninsa ma da babbar rigarsa a hannu Matawalle ya fito da ita. Ta din ga mamakin, yaya aka yi haka? Me aka yi masa ya fita daga hayyacinsa haka. Sai warin wasu mayuka yake yi, da ta gaza gane kowane iri ne.
Su Sultan suka fita yin salla, Nana ta ƙarasa kusa da Hammad, ta taɓa shi, ta shafa gashin kansa ta ce "Sayyid, Sayyid ka na ji na kuwa?"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.