Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 82 of 99

Ummi ta ce "Wallahi Uwani, Nana ta sha wahala, da shi sosai da sosai, Allah ya nuna ikonsa. Kuma shi ma ya yi halacci"

Uwani ta ce "Ba kaÉ—an ba, Allah dai ya ba su zaman lafiya"

Imran ya ce "Dan ma ba ku ji wahalar da ta sha a Niger É—in nan ba, da yawon nemansa" Nan Imrana ya gaya musu abin da ya sani. Yaya Atine ta ja baki ta yi shiru.
Uwani ta ce "To Isa, ina fatan ya zame maka izina, akan abubuwan da ka aikata wa yarinyar nan. Kuma ya zama dole a kira mahaifiyarta a sanar da ita komai, kuma a yi shirin tafiya da ita gurin bikin nan, dan ba za ka ci gaba da wannan jahilcin ba"

Imrana ya ce "To ai a Bauchi muka kwana, an je har gida an kai wa Umma lefen ta gani, an yi mata godiya sannan muka taho nan yau"

Uwani ta ce "Ikon Allah, haihuwa mai rana" Duk yadda Mama ta so ɓoye ɓakin cikinta abu ya ci tura.

Can gidan Umman su Nana, ta yi sujuda babu adadi na tsantsar murna da farinciki. Iliyasu kansa bakinsa ya ƙi rufuwa, amma ko kallo bai ishe ta ba. Dan ta wani fannin guduwar Nana, sauƙi ya sama mata, dan tun da ya san ya yi sanadin ɓatan Nana, duk abin da take yi masa baya cewa uffan.

"Mai Jidda kin ga ikon Allah ko? Ashe ta wani fannin gara da Nana ta je neman mijin nata, da tana zaune a nan babu lallai su haÉ—u. Allah sarki rayuwa"

Maijidda ji ta yi kamar ta make shi, ya ga abin Duniya, jikinsa sai tsuma yake yi.

*****
Asal na zaune ta damƙe wayarta iya ƙarfinta, saboda ganin hoton katin gayyatar bikin taron bikin Hammad da matarsa, da kuma naɗe-naɗen sarauta.
Hasna ta ce "Asal, ki ajiye wayar nan ki samu ki saka wani abu a cikinki mana" Ta girgiza kai hawaye na gangarowa daga idanunta.
Ji suka yi an buɗe ƙofar ɗakin, suka ɗaga baki ɗaya. Hammad ne ya shigo, jikinsa sanye da shiga ta alfarma. Ƙamshin turarensa ya mamaye ɗakin baki ɗaya.
Hasna ta risuna cikin girmamawa tana gaishe shi. Asal kuwa ta sunkuyar da kanta, zuciyarta na tsananta bugawa cike da tsoro da fargaba, saboda ba ta taɓa tsammanin ganinsa ba. Kuma ba ta san me yake tafe da shi ba. Da yatsunsa biyu ya yi wa Hasna alamar ta fita ta ba su guri.

Ayshercool
08081012143
100
LITTAFIN KUÆŠI NE, A BIYA KUÆŠIN KARATU KAN A KARANTA.
0069685771
AISHA ADAM STANBIC
08081012143

Asal ta sunkuyar da kanta ƙasa, ji take yi tamkar ƙasa ta tsage ta shige, saboda matsananciyar kunyarsa da take ji.
Ya ƙarasa ya zauna a gefenta, ya ce "Me ya same ki haka?" Ba ta ɗago ba, ta girgiza masa kai.
Shiru ya wanzu tsakanin su, babu wanda ya yi magana. Ya ce "Tun da ba za ki yi magana ba shikenan" Har ya yinƙura, ta riƙe rigarsa ta ce "Sakina ka zo ka yi ko?"

"A'a, dama ai ni ban kore ki ba, na dai ba ki zaɓin zama da ni ne, amma na ga kamar ke da mahaifinki, kun fi gamsuwa da na sauwwaƙe miki."

"Dan Allah Hammad ka yi haƙuri ka yafe mini, na san laifukana ba za su ƙirgu ba, sai a wannan karon Allah ya tona asirina"

Yayi murmushi ya ce "Ba zan yi miki dole ki zauna da ni ba, muddin kin san zuciyarki haryanzu tana son Omar" Wata irin É—agowa Asal ta yi a razane jin abin da ya ce.
"Hmm Asal kenan, duk tsawon zaman da na yi da ke, babu abin da ban sani ba, kar ma ki yi zaton ko wani ne ya gaya mini. Saka mini magani da duk wani nau'i na ƙoƙarin illata ni da ki ke yi, duk na sani, kuma ina kallonki. Ba domin babu yadda zan yi da ke ba, sai domin ina jin tausayinki, kuma ke ƙanwata ce"
Zamowa ta yi ƙasa cikin kuka ta riƙe rigarsa ta ce "Wallahi na yi nadama Hammad, na san ko ba ka ce mini komai ba, Hakkinka ba zai bar ni ba. Amma ba laifina ba ne ba, ka sani dan Allah ka yi haƙuri ka yafe mini, kar ka sake ni. Wallahi ina sonka"
"Dama ai ban ce zan sake ki ba, mahaifinki ne ya nemi hakan, kuma nima na so aikatawa amma na duba idan na yi haka, ba ki da wata kyakykywar makoma, bayan gama lalata rayuwarki da aka yi. Kuma ba na son asirinki ya ci gaba da tonuwa a idon Duniya. Uwa uba Nana tana ta yi mini magiyar kar na rabu da ke. Na so samarwa kaina cikakkiyar nutsuwa da rayuwa da wadda bata harin komai daga gare ni sai alkhairi, amma ban san me Allah zai yi mini a sanadin yafe miki ba. Asal zaki koma ɗakinki bisa sharaɗi, dan ta ni ko yanzu ki ci gaba da duk abin da ki ke yi mini, bai dame ni ba; amma muddin ki ka yi wani na yinƙurin cutar mini da matata ko ɗana, wallahi sai na ɗaure ki, ɗaurin rai da rai ma kuwa. Ba zan taɓa yin wasa da duk wani abu da ya shafe su ba, dan haka zaki amince da babu ruwanki da duk wani abu da ya shafe su, balle a zo ga batun cutarwa"
Wani abu raɗaɗi ya tsirga wa Asal,  wai ita ake gindaya wa sharaɗi a kan Nana. Sai dai babu yadda ta iya ta jinjina masa kai ta ce "Na amince"

Ya ce "Ki yi tunani da kyau, kar ki saɓa abin da ki ka ce daga baya, na ɗauki mataki ki ji haushina"

"Na tabattar da na amince"

Ya ce "To shikenan, tashi" Sai dai ƙafafuwanta suka yi mata nauyi, ta kasa tashi, saboda haryanzu tana jin nauyinsa, kenan har soyayyar da suka yi da Omar ya sani, amma ya ƙyale ta a gidansa.
Babu tsammani ta ji ya saka hannu ya ɗago ta tsaye. Ya ce "Na saka an ɗan yi mana gyara a gida, zan canza miki komai. Har cikin zuciyata na yafe miki, na san wasu abubuwan ba laifinki ba ne, kuma ko dan kusanto da Nana gare ni da ki ke yi yakamata na yafe miki. Allah ya sanya kin yi tabbataccen tuba" A duk lokacin da ya ambaci Nana, sai ta ji baƙin ciki kamar ya halakka ta. Ya sumbaci goshinta, ya mayar da ita kan gadon ya zaunar da ita, ya ce "Allah ya baki lafiya" Daga haka ya juya ya fita. Wani irin kuka ta saka, gaba ɗaya alamu sun nuna, a yanzu baya ganin mutuncin komai idan ba na matarsa da ɗansa ba. Ƙarara a idonsa da mu'alarsa ake iya karanto tsagwaron son da yake yi wa Nana.

Duk da yadda Sultan ya yi watsi da Imam Zahradeen, amma bai yi zuciya ba ya yi uwa ya yi makarɓiya a kan shirin gudanar da bikin ɗan uwansa.
Tuni baƙi suka fara hallara, aka ɗauke Nana daga cikin gidan Sultan, zuwa estate ɗin da yake mallakin masarauta, da galibi ake saukar baƙi a can. Estate ɗin da sunan Hammad aka saka masa, wanda a nan ta fara zama tare da Asal da ƙawayenta a ɗaya daga cikin gidajen.
Nana ba ta yi zato ba, ba ta yi tsammani ba, kawai ta tarar da mahaifiyarta da ƙannenta su Walida.
Gaba É—aya Nana ta yi wata irin rikicewa, jikinta ya hau tsuma.
Maijidda da kanta ta tashi ta nufi Nana cikin farinciki. Nana ta faɗa jikinta ta rirriƙe ta, cikin dashewar murya ta ce "Um.umm.Umma! Umma ki yi haƙuri dan Allah"
Maijidda ta ce "Shhh, kar ma ki kawo wannan zancen, ni yanzu lokacin farinciki ne da murna, dan haka kuka ya ƙare. Abin arziki da farinciki ne ya tara mu. Ni dai na gode wa Allah da ya sanya ina da rabon sake ganinku cikin kwanciyar hankali da kuma ƙoshin lafiya"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.