Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 67 of 99
*****
Bayan su Nana sun hallara a gaban Sultan, ta yi tozali da Giyaz a tsaye da sandarsa a bayan Hammad, sai da jikinsa duk rauni ya ƙara tsufa ya yi wani iri. Jikinsa sai hayaƙi yake yi ya zubo mata ido.
Sultan ya dubi Imam Zahradeen ya ce "Zahradeen me ka yi wa ɗan uwanka ne, ya ƙi magana, sunanka kawai ya furta ya yi shiru, a nan muka kwana tare da shi, ko sau ɗaya bai yi magana ba.
Imam Zahradeen ya haÉ—iye wani abu mai É—aci a wuyansa, yana tunanin ta ina zai fara bayani.
Nana ta ce "A je a zo da Sarkin baka gurin nan, idan ba haka ba Giyaz zai iya haddasa matsala"
Duk suka kalli Nana Imam Zahradeen ya ce "Waye hakan?"
"Ku zo da shi dan Allah, kar a samu matsala wani abin yake son aikatawa"
Ganin Nana na neman burkicewa, ya sanya Sultan É—aukko wayarsa ya É—an daddana, Hammad dai bai ce komai ba.
Imam Zahradeen ya ce "Kafin na ce komai, ina mai neman afuwarku a kan abin da zan faÉ—a, kuma ina neman afuwa da ni da waÉ—anda zan faÉ—a a cikin maganata.
Na ji daɗi sosai da sosai da ka neme mu a keɓantaccen guri kamar haka, ina roƙon ku rufa mana wannan asirin dan Allah"
Sultan ya ce "Zahradeen, ka tafi kai tsaye ka yi mini bayani, kana ta zagaye-zagaye daga mu sai mu a gurin nan"
Ya ƙarasa maganar yana kallon wayarsa, ya danna ya ce "Ku ba shi dama, shikaɗai ya shigo"
Sarkin baka ya shigo da sallama, ya risuna a gaban Sultan ya kwashi gaisuwa, ya juya ya gaida Imam Zahradeen, amma ya yi shiru yana kallon Imam Hammad da kuma Nana.
Sultan ya ce "Ga mai maganin an kira shi, ya aka yi?"
Sarkin baka ya ce "Uwar gijiyata, meyafaru da Giyaz ne?"
"Ƙaisar ya ce mini faɗa suka yi." Ta mayar da idonta kan Sultan ta ce "Allah ya baka nasara, ya ci gaba da maganar a gaban Sarkin baka, shi ma amintacce ne, idan ya fita Giyaz zai iya aikata masa wani abin"
Sultan ya ce "Waye Giyaz É—in ne?"
Sarkin baka ya ce "Aljanin da aka yi masa asiri da shi ne ranka ya daÉ—e"
Imam Zahradeen ya fara magana ya ce "Tabbas na san ni mai laifi ne, kuma duk hukuncin da za a yanke mini zan karɓa"
Ya É—an yi shiru sannan ya ce "Mahaifiyata, Gimbiya Bilkisu, sun haÉ—a baki da É—an uwanta, mai girma Tafawa, suka yi masa sihiri, aka haÉ—a shi da aljanin da zai bar garin da shi gaba É—aya.
Wallahi ban san sun yi ba, sai daga baya take gaya mini, saboda su na son ko ni ko Asadullah wani ya gaji kujerar Hammad. Na nuna mata rashin jin daɗina, ta ce mini aikin gama ya riga ya gama, muddin Hammad ya dawo Agadez sai ya haukace, ko ma ya rasa rayuwarsa. Shi ne na ɓoye lamba, na nemi Mahmoudu, a lokacin bai riga ya bar ƙasar ba, abin dai ya fara taɓa shi ne. Yanzun ma ba ni da yadda zan yi ne, amma ban so na tona wa mahaifiyata asiri ba"
Hammad ya sunkuyar da kai hawaye na zuba daga idanunsa, Sultan ya rikice cikin tashin hankali da damuwa ya ce "Yanzu Zahradeen amma ka ɓoye mini wannan abin baka gaya mini ba? Yanzu ƙiyayyar da mahaifiyarka take yi wa Hammad har ya kai ga ta nemi ta zauta mini ɗa ya bar gida?"
Zahradeen yana kuka ya ce "Dan Allah ka yi haƙuri Abie, ban san komai a kai ba, sai daga baya. Kuma gudun kar idan ya dawo ya samu matsala, shiyasa na ce kar ya dawo Niger"
Nana ta ce "Gidan tarihi, a gidan tarihin Agadez aka yi masa sihirin, kuma ba sihiri ɗaya ba ne, mutane daban-daban sun yi masa. Ranar da muka je cikin gidan tarihin tare da shi, na ji ƙamshin turaren Gimbiya Bilkisu a gurin. Sannan bayan ƙamshin turaren ta, na ji ƙamshin turaren wani ma.
Gaba É—aya suka É—aga kai, su na kallon Nana.
"Duk wanda yake ƙamshin nan, da alama yana ziyartar gurin, kuma wanda yake yi musu aikin sihirin a cikin gidan tarihin yake. Idan gidan tarihin nan babu kowa a cikin sa, to wannan mai gadin ne bokan da yake aikin, ko kuma ya san bokan da yake yi.
A rikice Sultan ya ce "Wane gidan tarihin wai, waye mai gadin?" Sai kuma ya rufe bakinsa, suka dubi Hammad a rikice, yadda ya runtse idanunsa yana zubar da hawaye.
Nana ta rikice ta tashi ta nufe shi, Sarkin baka ya ce "Kar ki taɓa shi, Giyaz ne yake zungurarsa, zai iya yi miki wani abin ya cutar da ke"
Ya tafi gaban Hammad, ya kama goshinsa ya din ga karanta Bismillah da suratul Fatiha, yana tofa masa a tsakiyar kansa.
Daga bisani ya ɗaga rigarsa ya ciro jakar nan da ya bawa Nana, ya ce "Idan baka tafi ka ƙyale shi ba, zan illataka da jakar nan kamar yadda Ƙaisar ya yi maka"
Nana rikicewa ta yi, duk da ba yau ta saba ganin abin mamaki ba, jakar da take hannunta, ta neme ta ta rasa, ta ganta a gurin Ƙaisar, yanzu kuma ta koma hannun mai ita Sarkin baka.
Ya kalli Nana ya ce "A gurin ƙamshin turaren wa ki ke ji?"
Nana ta yi shiru tana satar kallon Sultan, tana kuma kallon Zahradeen.
"Kar ki ji tsoron kowa, gaya mini" Ta ƙi magana tana jinjina yadda za su ɗauki abin.
Ya ce "Muje ki nuna mini gurin, ai babu abin da zai gagara da ƙarfin ikon Allah"
Sultan ya tashi a rikice jikinsa yana tsuma, idanunsa sun yi jawur saboda ya kaÉ—u da abubuwan da suka fito daga bakin Imam Zahradeen. Wani irin mugun tausayin Hammad ya mamaye masa zuciya.
Ya kalli su Nana ya ce "Yanzu can gidan tarihin za mu je kenan?"
N
Sarkin baka ya ce "Eh Allah ya baka yawan rai"
Imam Zahradeen ya ce "Ko a yi wa su Matawalle magana, a tafi da wani daga cikin su, ko hadimai"
"Bana buƙata" Sultan ya faɗa fuskarsa babu annuri, ba tare da ya kalli inda Imam Zahradeen yake ba.
Ya dubi Hammad da ya buÉ—e idanunsa, sai dai baya magana, dan tun da ya zo wa Sultan ya ce masa Zahradeen ne, bai sake yin magana ba.
Ya shafa kansa ya ce "Hammad, ka na ji na?" Ya jinjina kai.
"Ko zaka bi mu ne?" Ya girgiza kai.
"Ka na nan mu je mu dawo?" Ya É—aga masa kai alamar eh.
Ya girgiza kai ya ce "Ina Mahmoudu ne, ban ganku tare da shi ba, a nemo shi ya zo ya zauna da shi tukuna sai mu tafi"
Imam Zahradeen ya tafi ciro wayarsa, ya hau laluben lambar Mahmoudu. Sultan da ya kalli Imam Zahradeen sai ya ji ransa ya ɓaci, ya yi mamaki ya kaɗu matuƙa da jin abin da Gimbiya Bilkisu ta yi wa Hammad. Ga abubuwan da Tafawa ya din ga yi masa, da tursasa shi a kan yi masa abubuwan da yake so, da shi da 'yarsa amma hakan bai ishe su ba, suka nemi a ɓatar masa da ɗansa.
Sai da Mahmoudu ya zo, Imam Zahradeen ya ce "Imam Hammad ba ya jin daÉ—i ne, ka zauna tare da shi, zamu je mu dawo"
Tiryan-tiryan suka bi ta ɗakin da su Nana suke zaune, suka buɗe wannan ƙofar kamar yadda Nana ta yi musu bayanin ta nan suka bi, suka gangara har gidan tarihin.
Mai gadin na ganin Sultan, jikinsa ya hau tsuma ya zube a ƙasa tamkar zai yi masa sujuda yana kwasar gaisuwa. Sai dai gaba ɗaya ya rikice da ganin Sarkin baka.
Ko da suka shiga cikin gurin, kawai Sarkin baka ya bushe da dariya, duk suka tsaya suna kallonsa. Ya tsaya yana ƙare wa gurin kallo, yadda aka rarake dutse aka gina wannan gurin, mutanen zamanin da suka yi wannan aikin sun cancanci yabo.
Sarkin baka ya sake bushewa da dariya ya ce "Sarki a dawa Sarki a gida, Ni mai Duna ni mai Salamatu, ni mai Mairo 'yar Fulani. Ni ake yi wa inkiya biyu, Garba ga Baka ga Aska, na yi gadon gidanmu, na ƙwaci wanda ban gada ba, na fi 'yan na gada iyawa. Ni Abubakar Garba mai taƙama da ikon Allah. Na ga mutum na ga Aljan, na ga cuta na bada maganinta, idan babu na ce ba ruwan Garba. Ya buga ƙafarsa ɗaya ya ce "Uwar gijiyata, ƙamshin turaren wa ki ka ce kina ji?"
Nana ta sake kallon su Sultan, Sarkin Baka ya ce "FaÉ—i kanki tsaye, ba wanda zai yi miki abin da Allah bai yi miki ba"
Ta É—an sunkuyar da kai ta ce "Akwai wani Imam Omar, wanda ya kawo wa Imam Hammad ayaba tare da Yayan Asal"
"Ƙamshin turarensa ne?" Imam Zahradeen ya tambaye ta cikin zaƙuwa.
Ta ce "Ni tsoron faÉ—a nake, ba na son haÉ—a husuma ne"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.