Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 32 of 99

Sultan ya amsa da "Amin"

Hammad bai sake dawowa ba sai bayan sallar asuba. Da ya shigo ma bai kai ko kalli inda Nana take ba.

"Ina kwana" Nana ta gaishe shi tana satar kallon sa, amma ya yi mata shiru bai amsa ba.
Gaba ɗaya sai ta ji babu daɗi shirun da ya yi mata. Ya je gaban mudubi yana gyara gashinsa, ta ƙarasa gaban mudubin ta ce "Kawo na gyara maka?"

Ya harare ta, ya share ta ya ci gaba da taje gashinsa.

Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin aka yi, ya ajiye comb ɗin, ya kalli Nana ta je ta ɗaukki hijjabinta ta saka. Ya ƙarasa ya buɗe ƙofar.
Mahmoudu ya shigo da kwanukan Abinci.
Ya gaida Hammad, ya É—aga masa hannu. Nana ta gaishe shi ya ce "Ni yakamata na din ga gaishe ki, uwar gijiyarmu. Ya mai jiki?"

Nana ta ce "Asma'un dai. Mai jiki da sauƙi Alhamdillah ina Nene?"

"Tana nan ƙalau, ga saƙon ki nan in ji ta, ina ta lallaɓata ta dawo Agadez, na ajiye ta a gidana amma ta ƙi" Ya yi maganar yana nuna wa Nana flask.

Nana ta ce "Dan Allah idan ka koma idan za a bari na ganta, ka ce dan Allah ta taimaka ta zo na ganta, Kodayake da an sallame ni daga nan, gurinta zan je ta ce za ta raka ni gid.. sai dai sauran maganar ba ta fito ba saboda harar da Sayyid ya yi mata.
Mahmoudu ma ya kawar da maganar, ya koma yi wa Hammad magana da yarensu. Hammad ya yi shiru yana saurarensa. Ba ta san me suke tattaunawa ba, amma da alama abin da suke tattaunawar ya ɓata masa rai. Ya tashi ya ɗaukko biro da takarda ya fara rubutu.
Sai gaban Nana ya faɗi, zuciyarta ta fara raya mata ko takardar saki yake rubuta mata. Ya gama rubutunsa ya miƙa wa Mahmoudu, suka fita tare.

Ta yi ajiyar zuciya ta buÉ—e flask É—in da Nene ta bayar a kawo mata. Nana ta yi murmushi ganin naman kaza cikin flask É—in, ta ce "Nene so take sai na fashe saboda girma"

Ba ta sake ganin Hammad ba, sai da daddare, da yaje ya yi wanka, ya canza kaya ya nufi hanyar fita. Nana ta ce "Sayyid wai yau ma nikaÉ—ai zan kwana a É—akin nan? Amma ka san É—akin nan tsorata ni ake yi"

Ya ce "Me zan zauna na yi miki, zan iya ɓata miki rai idan na ci gaba da zama a ɗakin nan, gurin matata zan tafi" Ya yi mata maganar a gadarance. Ƙifta ido kawai ta yi idanunta suka yi jawur. Sai a lokacin ya yi dana sanin abin da ya gaya mata, biyo bayan tuna matsanancin kishi da take da shi.
Ji yayi kamar ya bata haƙuri, ya koma ya zauna, amma ya yi jarumta ya fice. Sai dai tun da ya fita abin duniya ya dame shi. Tausayin Nana ya mamaye shi, ya sa dole ta yi kishinda Asal kuma ta ji haushin sa, mussaman yadda Asal ɗin ta din ga yi mata isa da iko, da nuna mata ita ba komai ba ce ba.
Tun da ya fita Nana ta kasa zaune ta kasa tsaye, wani abu mai raɗaɗin gaske, ya soke mata a ƙirjinta zuwa wuyanta. Duk da ta saba ganinsu guri ɗaya, tana kishin hakan amma na yau ya yi mata ciwo nesa ba kusa ba.
Bacci ɓarawo ne ya ɗauke ta, sai dai wannan mummunan mafarkin, na halittun nan, suka din ga bin ta, gaba ɗaya baccin ya gaza yi mata daɗi.
Kafin Asuba ta farka da wani irin zazzafan zazzaɓi da ciwon da kai.
A inda ta yi salla ta kifa kanta ta kwanta, zuciyarta cike da damuwa, ga jikinta babu daÉ—i.
Ji ta yi an danne ta, ta buɗe idonta ta ga Muhsin ya ƙanƙame ta. Tashi ta yi zaune a rikice tana faɗin "Muhsin ɗina"
Ya ƙanƙameta, ita ma ta rungume shi tana wani irin murmushi tamkar ta mayar da shi cikinta.
Ta ɗaga kai ta ga Hammad a gefe, yana karyawa. Muhsin ya tashi daga jikinta, ya je gaban Imam ya ɗaukko dabino, ya dawo ya saka mata a baki, ya sake komawa ya ɗaukko ya kawo mata. Ta saka hannu ta karɓa tana jin wani irin tasirin alaƙa ta tsakanin uwa da ɗa.

Sayyid ya É—auki Muhsin, ya ajiye shi a kusa da shi, yana ba shi Abincin. Ya waiwaya ya kalli Nana ya ce "Naaa" ya din ga nuna mata kusa da shi, wai ta zo ta zauna ta ci.
Sam Hammad bai nuna ya san tana gurin ba. Amma duk da haka yanayin ya yi mata daɗi mara misatuwa, yau ga mijinta ga ɗanta a guri ɗaya. Kuma alamu suka nuna mata, a zaman da Muhsin ya yi da su, akwai alaƙa mai ƙarfi a tsakaninsu. Dan duk ƙyuyar Muhsin ba ta ga alamar yana yi masa ba.
Ƙarshe ta yi shiru tana kallonsu, ya shirya cikin jallabiya fara ƙal, ya shirya Muhsin da kansa, sai dai ga mamakinta ba ta ga ya naɗa rawani ba, ya saɓa ɗansa a kafaɗarsa ya yi waje. Ƙasan zuciyarsa kuwa raya masa ya din ga yi ya rungume ta, ya ji damuwarta, yana da abubuwan gaya mata da yawa, amma ya daure ya share ta.

Sultan yana zaune, yana saka hannu a wasu takardu, tare da Tafawa da Sardauna. Aka shigo aka nema wa Tafawa iso. Gaba É—aya suka shiga mamakin me ya kawo shi a daidai wannan lokacin.

Bayan sun gaisa ya ce "Na samu takardar kiran da ka yi mini ne, shi ne na amsa kiran.

Cikin mamaki Sultan É—in ya ce "Ni É—in kuma?"

Tafawa ya ce "Amma saƙonna samu har gida aka kai mini takarda"

Sultan ya ce "Ai ni ba zan aika maka da takarda dan ina neman ka ba, amma da mamaki"

Tafawa ya ce "Ikon Allah, to waye ya aikata hakan?"

"Ni ne" Imam Hammad ya amsa ya na ƙarasa shigowa gurin.

Ayshercool

87
LITTAFIN KUÆŠI NE, KI BIYA KAN KI KARANTA 08081012143

Ƙwalalo manyan idanunsa Tafawa ya yi, ganin Imam Hammad ya fito gashinsa a buɗe, saboda hakan abu ne mai girman gaske, mussaman ga shugaba kamarsa,hakan kuskure ne.
Ba wannan ya fi kaɗa shi ba ma ɗan ƙaramin yaron da yake hannunsa ne ya fi tafiya da tunaninsa. Ya girgiza matuƙa gaya da ganin yaron.

Su Sultan ma sak suka yi, su na mamakin yaushe ya Hammad ya samu sauƙi har haka, har bakinsa ya yi wannan buɗewar? Ga uwa uba wautar da ya yi na zuwa da Muhsin ba tare da an gama shirya yadda za a kare hakan ba.

Imam Hammad ya nemi guri ya zauna, cikin girmamawa ya gaishe su, bai damu da jiran su amsa ba. Ya dubi Tafawa ya ce "Mai girma Tafawa, ina fatan ban yi laifi ba, kasancewar a ƙarshen wasiƙata, ban sanar da cewa ni nake nemanka ba, ba Sultan ba. Na zaɓi saka gurin haɗuwar ya zama nan ne, saboda sai ya fi dacewa da abubuwan da suke bakina.
Kun aika da takarda Majalisar Sultan, sannan an aika da wata majalissar Imams. Duk da kwana biyu ba na samun sukunin zaman majalisar. Na gayyace ka nan ne domin warware maka duk wani abu da ka ke son sani, ba kai ba duk sauran wanda suke son sani ma. Ba sai mun ci gaba da wahalar da shari'a ba. Kamar yadda na gaya maka wannan shi ne ɗa na Muhsin, ina da ɗa, kamar yadda na din ga jaddada maka, ka din ga ganin kamar shaci faɗi ne, wanda nan gaba kaɗan zan bayyana wacece mahaifiyarsa ba na son mu zurfafa a kan wannan bangaren dan abu ne da ya shafe ni. Abu na gaba kuma ana cewa ba ni da cikakkiyar lafiya ba zan ci gaba da gudanar da shugabanci ba. Haka ne, yakamata na matsa gefe na samu cikakken hutu da nutsuwa kamar yadda ku ka buƙata. Sannan kuma babu zobena na tambari a hannuna. Ina mai farincikin sanar da kai cewa daga yau, na sauka daga kan muƙamina na shugabancin majalisar Imam. Ba iya wannan ba ina san a cire ni daga cikin Imam da ake sanya ran a cikinmu ne za mu gaji sarautar Sultan shi ya sanya na fito maka haka babu rawani. Ka na damar maye gurbina na Imam ko ma shugabancin majalisar Imam ɗin baki ɗaya, ko kuma ka ɗora Imam Asadullah na muddin hakan zai sama maka farinciki da kwanciyar hankali. Ka bar mu mu huta da ni da mahaifina. A ƙarshe ina ƙara gabatar maka da ma petit Hammad wato Imam Muhammad H.J Agadez wato Muhsin" Ya yi maganar yana murmushi tare da shafa kan Muhsin.
Ya sake kallonsa ya ce "Idan babu sauran magana, za ka iya tafiya, ina muma fatan ka fahimci abubuwan da suka shige maka duhu game da ni"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.