Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 46 of 99

Asal ta din ga kuka tana ba shi haƙuri, dan ba ta yi zaton zai ma rufa mata asiri na kwanakin da ya yi ba.
Daga ƙarshe ya ce "Tashi ki je babu wanda zan gayawa"

"Dan Allah da gaske?" Ya tsare ta da ido, sai kuma ta nutsu ta ce "Na gode sosai da sosai, ba zan sake ba in sha Allah"

"To ban guri zan kwanta"
Ta ce "Dan Allah" sai kuma ta yi shiru.

"Mene ne kuma?"

"Dan Allah wace ce wadda ku ke waya da na shigo?"

Kawai ya kwanta ya share ta. Yana jin yadda take kuka, ya hau baccinsa, saboda haryanzu yana jin ɗacinta, a kan yadda ya iya danne abin da yake ransa ya yi wa iyayensu biyayya, amma ita fuskarta a tasa ta gaya masa, ba ta son sa ba ta ƙaunarsa.
Kasancewar ya saba baccinsa shikaɗai a ƙaton gadonsa, ya sanya shi ƙoƙarin yin juyi, amma ya ji kamar an yi masa dabaibayi. Asal ce a jikinsa tana ta bacci. Ya yinƙura zai ture ta saboda yadda ya ji shi wani iri saboda rashin sabo. Amma ta hana shi hakan."Ke ni fa kin matse ni, ki koma ɗakinki mana" Ta yi masa shiru duk da tana jin sa. Ƙarshe dai asancewar su 'yan Adam lafiyayyu, ba su bujirewa abin da gangar jikinsu ta buƙata ba.
Tun daga lokacin Asal ta ɗan nutsu, musamman da take tsoron, kar wataran ya faɗi abin da ta yi masa. Duk da ba daina tsiyatakunta ta yi ba, idan ta bushi iska tana yi. Shi kuma baya son duk wani dalili da zai sanya a ga gazawarsa ko ya yi ƙorafi a kanta.
Hankalin mahaifiyarta ya koma kan ganin Asal ta samu juna biyu, saboda zigar da Gimbiya Bilkisu take yi mata, a kan lallai ita ma ta yi ƙoƙarin ganin, 'yar ta ba ta zama abar morar Tafawa da ɗansa ba kawai. Dan ta san dole idan Asal ta haihu ta jiƙa musu aiki.
Shi ma ɓangaren Hammad, sai Allah ya jarrabe shi da matsanancin son 'ya'ya.
Gefe guda Tafawa bai fasa sanya Asal, yi wa Hammad binne-binne ba. Sai dai babban abin da yake ba shi mamaki shi ne yadda abubuwan ba su fiye tasiri a  kansa ba, har kiran Asal yake ya ƙare mata zagi, ya yi zaton ko ita ce ba ta yin aikin dai-dai, duk da wasu lokutan tana tsoron asirinta ya ƙara tonuwa.
Aka tafi shekara ta shida da aure, a lokacin ne Hammad haƙurinsa ya fara ƙarewa, saboda haihuwa yake so, kuma ba dan komai ba shi kawai yaran yake so. Duk Imam ɗin ƙasar su na da aure da 'ya'ya amma shi shiru. Ya ce wa Asal su je Asibiti a duba ko lafiya, amma ta ce ba za ta je ba, ya kaɗa ya raya ta ce ba zata ba.
Ya ce mata tun da haka ne, shi aure zai yi, ko ya mallaki kuyanga, dan saboda azabar kishinta ya sanya babu ruwansa da barorinsa.
Tun da ya faɗi haka ta hau rashin lafiya, Sultan ya je duba ta, ta din ga yi masa kuka a kan ya roƙi Hammad kar ya yi aure, yayi haƙuri tana addu'a ta san za ta haihu wataran.
Bata taɓa tunanin ta fara son Hammad har haka ba, sai da ya yi zancen aure, dan har iƙirarin kashe kanta ta yi. Tafawa ya samu Sultan har da kukan munafunci a kan ya saka baki, kar ya rasa Asal, ya rarrashi Hammad.
Ganin yadda Asal ta gigice, ya sanya Sultan ya din ga rarrashinta, ya samu Hammad ya ce "Hammad, na san kana yi mini biyayya, kuma kai mutum ne mai haƙur da juriya, dan Allah ina son ka sanya a ranka, rashin haihuwa jarrabawarku ce. Kuma ba a san me Allah zai yi nan gaba ba, dan Allah ka yi haƙuri da batun auren nan, kuma ka daina yi mata zancen haihuwar nan, saboda a samu hankalinta ya kwanta."

Karo na farko Hammad ya buɗe baki zai yi magana, amma Sultan ya dakatar da shi ya ce "Baka saba haka ba, kar ka fara a wannan karon, kai mai haƙuri ne, a wannan karon ma ina son ganin tasirin hakan a gare ka" Ya haɗiye yawu mai zafi, idanunsa suka yi jawur. Ya din ga zuwa Asibiti shikaɗai aka duba shi aka ce masa lafiyarsa ƙalau.
Asal kuma ta ci gaba da yi masa kuka da magiya a kan ya yi haƙuri su ci gaba da addu'a, ta san wataran za ta haihu, amma ya bar maganar ƙara aure, dan da gaske idan ya yi aure sai ta kashe kanta. Ya so ya yi mata magana a kan to ta bari su je Asibiti, amma ya tuna abin da Sultan ya ce masa, dan haka a dole ya ja bakinsa ya yi shiru ya ci gaba da addu'a.
Duk wanda ya yi alkhairi fatansa ya yi masa addu'a Allah ya ba shi haihuwa mai albarka, duk inda ya ji maganin haihuwa, da ya yadda da ingancinsa, sai ya karɓo ya kawowa Asal. Shi kansa Sultan abin ya dame shi, ba yau ba gobe cikin yi wa Hammad addu'a yake, ganin yadda yake ruɗewa idan ya ga 'ya'ya, duk wanda ya haihu a masarauta muddin ya ji labari, sai ya yi masa kyauta mai tsoka ya ce shi ma a yi masa addu'a.
Matawalle ya samu Sultan ya ce "Anya ba ka ganin kamar an cutar da Imam Hammad da yawa, da an bari ya jarraba auren wata matar mu gani ko Allah zai sanya a dace"

Sultan ya girgiza kai ya ce "In sha Allah zai ga daidai a rayuwarsa. Ina jin tausayin Asal ne, gaba ɗaya hankalinta a tashe yake, amma a ɗan ƙara haƙuri a ci gaba da addu'a. Kuma ka san mahaifinta ba ya raina abin magana, yanzu sai abin ya zama na surutu.
Ita kanta Asal abin ya dame ta, mussaman ganin yadda Hammad ɗin yake damuwa da lamarin 'ya'ya, sai dai baya yi mata maganar. Tun da ƙananan shekaru, Hammad ya haɗu da larurar hawan jini ake ta fama.
Asal ta ƙara shiga tashin hankali, ganin yadda ake ƙara yi wa Hammad tayin matan aure, ga shi matan ma farmaki suke kawo masa, saboda yadda siffofin kamala da cikar zati ke bayyana a tattare da shi. Su kansu kuyangin gidan su na neman su zama mallakinsa.
Sai dai a ransa ko zai yi kuyanga, baƙaƙen nan yake so ba farare ba. Duk ya kawar da kansa saboda Asal.
Wataran ya fito zai fita, wata hadima ta risuna cikin girmamawa tana gaishe shi ya ce "Sa'ada na daina ganinki kwana biyu"

"Allah ya taimake ka, na yi rashin lafiya ne"

"Subhanallah, ai ban sani ba, kin rame sosai da sosai. Maza ki je a duba ki, kuma ki ci abinci sosai, kin fi kyau lokacin da ki ke da ƙiba, Allah ya sauwwaƙe" wasu lokutan Hammad akwai raha, saboda a cewarsa hakan zai ƙara masa kusanci da hadimansa, shi ba ya son wannan tsoron nasa da suke yi.
Ta risuna cikin girmamawa tana murmushi ta yi masa godiya. Aikuwa ta sha bala'i a gurin Asal, ƙarshe ta kore ta daga sashen girke-girken gidan, zuwa wani abin daban.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.