Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 34 of 99
"Ni ba biyana za ka yi ba, ban yi dan ka biya ni ba, ni kawai su bar mini kai, kuma su dawo mini da Muhsin mu rayu tare" Ta yi maganar tana kuka.
Ya yi murmushi idanunsa na cika da hawaye, ya ce "An bar miki ni, halak malak. Hammad naki ne rayuwata" Ya yi maganar yana haÉ—e bakinsa da Nana.
Babu tsammani aka banko ƙofar ɗakin, Nana ta yi wata irin zabura, shi kuwa cikin nutsuwa ya waiwaya ya ga waye wannan ya shigo musu babu neman izni.
Da Asal ya yi tozali, jikinta na wata irin tsuma take bin su da kallo. Ta nuna Nana da yatsanta bakinta yana wata irin rawa, jikinta ma karkarwa kawai yake yi, tamkar ana kaÉ—a mata gangi.
Ba ta taɓa tsammanin abin da za ta gani ba kenan, ko a hasashe da tsammani ba ta taɓa hasko ganin Nana tare da mijinta ba. Kasamcewarta baƙar fata da ba ƙabilarsu ba.
"Ham..Ha.ha...Hammad!" Ta faɗa cikin wani irin ƙaraji mai razanarwa.
Bakin Asal ne ya ci gaba da rawa, dan da fari ma kanta gaba É—aya kullewa ya yi, ta manta wace ce ma Nana.
Ita da ta zo tambayarsa ba'asin ina ya samu É—a, sai ta riski abin da ya fi maganar da ta zo da ita tashin hankali.
Hankali kwance Nana ta gyara rigarta, ba tare da abin da ya faru ya É—aga mata hankali ba.
Ja da baya Asal ta fara yi, numfashinta na fita da kyar, jikinta na wata irin kyarma. A sukwane Imam Hammad ya diro daga kan gadon ya nufe ta, cikin tashin hankali bai so Asal ta san alaƙarsa da Nana ta wannan sigar ba. Amma ya san babanta shi ne ya lalata komai.
"Kar ka taɓa ni, kar ka ƙaraso inda nake Hammad. Ka yaudare ni ka zalunce ni, dama rashin lafiyar da ka ke yi ƙarya ka ke yi? Ka haɗa kai da mahaifinka ne dan ku yaudare ni ku cutar da ni? Lalata da wannan ƙasƙantacciyar ƙazamar matar? Na zaɓo ta a matsayin kukunka dan kawar da kanka daga kalle-kallen wasu matan, ashe yaudarata ka ke yi? Tun tsawon lokacin da ta gudu na neme ta na rasa, a she a nan ka ɓoye ta ku ke lalata."
Cikin azama Hammad, ya danƙo hannun Asal, da take ta fizge-fizge ya danna ƙofar ya datse ta. Ya kalli Asal ya ce "Ki nutsu cherié zan yi miki bayani, ni ba lalata nake yi da Asmy ba"
Cike da baƙin ciki take kokowar fizgewa cikin ƙaraji ta ce "Idan ba lalata ku ke yi ba, me ku ke yi? Tsawon wannan lokacin da ba ta nan, ashe ku na tare ka ji kunya ba ka ji daɗin halinka ba. Ke kuma 'yar iska mazinaciya wallahi sai na ƙasaƙantar da ke, sai na saka an kashe mini ke a kashe banza"
Nana ta ce "Point of correction my dear, ba da kukun mijinki ki ke magana ba a yanzu, kuma ni ba mazinaciya ba ce ba. Ki dai nemi wani sunan ki kira ni da shi"
Ya kalli Nana da ta tsuke fuska ya ce "Ma vie dan Allah ki yi shiru, mu warware matsalar nan a hankali"
AREWABOOKS
Daskarewa Asal ta yi jin sunan da ya kira Nana da shi, wanda shi gaba É—aya ya manta, saboda yadda sunan ya shiga bakinsa ya zauna.
"Hammad gaskiya ne abin kunnuwana suke jiye mini? A gabana? Hammad" Ta furta tana ajiyar zuciya mai ɗauke da nannauyan baƙin ciki da tashin hankali.
Damƙar hannun Asal ya yi, ya buɗe ƙofar suka fita tare.
Kokowa ya shiga yi da Asal, yadda take kai masa duka, tana fizge-fizge.
"Asal, ki tsaya ki saurare ni, kar ki ji wa kan ki ciwo mana"
"Ba zan saurare ka ba, ba na buƙatar duk wasu kalaman yaudara da ƙarya da za su fito daga bakinka. Me ya rage bayan abin da na gani? Da girmanka da mutuncinka ka ɓoye kukunka a sashen mahaifinka kana zina da ita, ba ka ji daɗin halinka ba" Kalaman Asal sun yi wa Hammad zafi nesa ba kusa ba, da kyar ya haɗiye wani yawu mai zafi ya ce "Ni ba zina nake yi ba, idan ba ki tsaya kin saurare ni ba, ki ka fita ki ka yayata abin da ba shikenan ba za ki cutar da ni dan kin yi mini ƙazafi"
Kallonsa take yi, tana jinjina girman yadda ya ƙware a iya wasa da hankali, ta ci gaba da ƙoƙarin fizgewa, amma ya riƙe ta gam.
"Hammad ka gama raina mini hankali, dama ga batun ɗa ana yi, an ce ka na da ɗa da a ƙalla ya shekara biyu, yanzu kuma na kama ka da wata, amma kana iƙrarin zan cutar da kai? Da ni da kai waye ya cutar da wani? Wadda ka yi wa ciki ba ta ishe ka ba, ka ɗauki kukunka ka sanya a sashen Sultan ka ke lalata da ita"
"Ban taɓa cutar da ke ba Asal, a shekara goma sha biyu da muka yi da ke, idan zan iya aikata abin da ki ka faɗa kin sani, idan akasin hakan ne ma kin sani. Amma mu je gurin Sultan ɗin ki ji komai daga bakinsa.
Nana kuwa guntun tsaki ta yi bayan fitarsu, ta tashi ta shiga banɗakin ta yi wanka, ta yi alwala. Ta ƙura wa kanta ido a mudubin banɗakin, tana tunanin yadda Asal ta din ga yi mata kallon ƙasƙanci, da bautar da ita ta ƙarfi da yaji, saboda tana da kuɗi da mulki, a matsayinta na kishiyarta, kuma ta daure ta haɗiye. Ta ci gaba da tunanin daga bisani ta fito da niyyar ta canza kaya, amma ta kasa, ta nemi guri ta zauna ta yi shiru.
A zuciyarta take addu'a ta ce "Allah ga Nana, bakwarka ce ni mai raunin gaske, ga ɗan jaririn ɗa na da nake fatan ya samu kyakykywar rayuwa ya tashi a tsakanin uwa da uba. Ubangiji Allah ka na ji ka na gani, ka ga wahalar da na sha a baya, ga shi na zo wani bugire da nake sanya ran samun afuwa, sai dai alamu sun nuna an fi ƙarfina. Allah idan sun fi ƙarfina ba su fi ƙarfinka ba, da ni da su duk bayinka ne. Ubangiji Allah ka sassauta mini ka kawo mini ɗauki. Ubangiji Allah ka yaye mini wannan kishin da nake ji, ka sanya su bar ni na rayu da mijina da ɗa na. Ubangiji Allah ka ba wa mijina ingantacciyar lafiya ka yaye masa abin da yake damunsa, Allah ka ba kare mini ɗana daga dukkanin sharrin da ido ka iya gani, da wanda ma baya gani. Ƙaisar ma bawanka ne, Allah ka ba shi lafiya. Allah ka ga wahalar da na sha a baya, yanzu idan na koma suka raba ni da ɗa na, wata wahalar zan shiga, Allah ka kawo mini agaji" Sai kuma ta yi shiru tana nazari, duk abin da take faɗa ai Allahan yana ji yana gani.
'Idan ba ubangijina ba, wa nake da shi da zan kaiwa kukana kai tsaye ya share mini. Na san ya sani amma ƙara gaya masan, yana sama mini nutsuwa da kwanciyar hankali, ko da ina cikin damuwa. Ta ba wa kanta amsa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.