Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 90 of 99
"Ba ka tuna Alhaji Zailani ba?" Ya yi shiru ya tafi tunanin, kamar ya san sunan, can kuma ya ce "Na tuna, mutumin da muka fara gadi a gidansa da su Mahmoudu. To Allah ya kyauta ke mene ne naki na shiga tashin hankali haka?"
"Dan Allah Sayyid ina son zuwa Nigeria" Ta yi maganar cikin tsoro da tashin hankali.
"Sati uku da gama hidimar nan ki ce za ki Nigeria, a ƙalla nan da wata biyu nake son mu je tare"
Sai ta rikice masa gaba ɗaya a kan ita fa dole Nigeria take son zuwa. Abu kamar wasa ya ɗauka da wasa take yi, sai da ya ga ta yanke jiki ta faɗi, jikinta ya yi sanyi ƙalau. A hankali ya ɗaga kai ya kalli tsuntsun da yake shawagi a saman ɗakin, da hakan ya tabattar masa da Ƙaisar ne ya zo mata.
A ransa ya ƙudurce lallai a shirya tafiya Egypt ɗin nan, kafin su zo su ci gaba da samun matsala, su sake hana su zaman aure cikin kwanciyar hankali.
Sai dai idan ya ce a yi mata passport a Niger, zai ɗan ɗauki lokaci, dan haka ya yanke shawarar za su je Nigeria a yi mata, sai su tafi. Har wajen ƙarfe goma na dare yana tare da Nana, sai dai ba ta dawo hayyacinta ba. Ya kira Asal ya gaya mata Nana babu lafiya, dan haka ta yi haƙuri ba zai samu damar dawowa a ranar ba.
Asal kamar ta haÉ—iyi zuciya ta mutu, gani take kawai faÉ—a yayi, dan ya zauna ya kwana a gurin Nana, amma babu yadda ta iya. Shi kansa sai da ya raya za ta yi tunanin hakan, amma babu yadda za a yi ya tafi ya bar Nana a wannan yanayin.
Duk yadda su Sagir suke yi wa Shukura ɓoye-ɓoye, sai da ta san Allah ya yi wa mahaifinta rasuwa.
Hajiya Suwaiba ce ta fara ganin Videon nan, sai ba ta yi wa Alhaji Fatuhu magana ba, ta je gurin Fadila. Fadila ta É—an yi mamakin ganin Hajiya Suwaiba a falon ta.
Bayan sun gaisa ta ce "Fadila, ko Daddy ya gaya miki abin da yake damun sa?"
Fadila ta ce "Wallahi bai gaya mini ba, na yi na yi ya ƙi ya gaya mini"
"Kin ga wani video"
Fadila ta karɓi videon tana kallo, jikinta ne ya hau karkarwa ta ce "Wannan ai Alhaji Zailani ne? Wai yana nufin Alhajinmu ya yi wa abin da yake faɗar nan?"
"Nima abin da ya É—aure mini kai kenan"
Alhaji Fatuhu ne ya yi sallama, ya ga duk sun zubo masa ido, kamar marasa gaskiya.
"Lafiya kuwa?"
Hajiya Suwaiba ce ta yi kokarin cewa "Daddy wani abu muka gani, shi ne dama abin da ka ke ɓoye mana?"
"Me na ɓoye mukun?"
Ta miƙa masa wayarta, yana kalla ya ajiya, ya zauna cikin damuwa, ya ce "Koma mene ne ya faru, ya riga ya faru, dan Allah a bar maganar nan ta wuce"
Hajiya Suwaiba ta ce "Amma ya batun maganganun da ya din ga faÉ—a, yana cewa shi ya yi maka sihiri?"
"Suwaiba a bar maganar nan dan Allah"
"Amma ya zaka ce a bar ta, mutumin da ya tsugunar da mu, ya saka mu a wahala, to wallahi ni dai ban yafe ba."
Fadila ta sha mamakin abubuwan da ta ji a videon nan, kuma ta tsorata imani ya ƙara shigarta, sai dai tun da ta ji Alhaji Fatuhu bai musa ba, to tabbas an yi hakan.
*****
Nana Bakinta ya ƙi rufuwa, wani irin farinciki take ci, ganin sun kama hanyar Nigeria.
Ta din ga tuna lokacin da ta yi balaguro, daga Nigeria zuwa Niger tsawon shekaru, ta tafi zuciya a cunkushe cike da rashin sanin makoma, sai dai kyakykywan yaƙini da dogaro ga Allah. Sai ga shi a wannan karon ta nufi zuwa gidan, cike da farinciki da kwanciyar hankali. Ta so tahowa da Muhsin, amma Hammad fafur ya hana, wai sai zo ɗaukarta zai taho da shi.
Sai da suka samu saɓani kafin ta taho, dan cewa ta yi muddin Asal zai kai wa ɗanta gara ta haƙura da tafiyar. Ƙarshe sai da suka kai shi gidan Zahradeen, sannan ta hakura ta taho.
A garin Bauchi ta fara yada zango, duk da nan ma abin da ya faru ba zai taɓa gogewa daga cikin ƙwaƙwalwarta ba. Mama tana ta kiranta a waya ta ji ko ta kusa ƙarasowa.
Ko da Nana suka isa, Iliyasu ta fara gani a ƙofar gida, ya tsaya yana washe baki, ganin Nana ta fito daga danƙareriyar mota da aka kawo ta a ciki.
"Maraba, sannunku da zuwa, sannu da zuwa"
Ita Nana ma abun da yake yi matan, kunya ya din ga bata. Ta tarar da su Adda Maryam da Fati da wasu daga dangin Umman, duk sun cika gidan. Sun yi murna sosai da sosai da ganin Nana. Suka din ga yi mata barka da zuwa.
Nana ta sha karramawa, mijin umman sai nan nan yake yi da ita, yana washe mata baki har da yi mata raha.
Baba ya din ga kiran Nana yana tambayarta sai yaushe zata ƙaraso. Ta ce masa ai ta sauka a Bauchi, sai ta kwana biyu za ta zo. Gaba ɗaya bai ji daɗin hakan ba, saboda yadda yake Alla-Alla ta zo ya sake ganinta.
Sai da Nana ta kwana uku a Bauchi, Mama tana a kaita tasha a saka ta a mota, ta ce ai direbanta yana nan a Bauchin bai tafi ba.
Suka sake É—aukar hanyar Kano, jalla babbar Hausa yaro ko da me ka zo an fika. Nana ta yi kewar garinta na haihuwa ba kaÉ—an ba.
Da sallama Nana ta shiga gidansu, Iya suturar jikinta, da yadda ta yi kyau mai É—aukar ido ya sanya Mama yin saroro da kasa amsa mata sallamar. Nasiru ne ya fito da gudu yana faÉ—in Oyoyo ga masarautar Agadez da kanta. Masu arzikin zinare, masu kyauta da dama hagu ma ba ta san ana yi ba. Barka da zuwa Garkuwar matan Agadez ke ta Afrika ma gaba É—aya." Kawai Nana ta tsaya tana murmushi, Jamila ta fito daga É—akin, ta zo ta rungume Nana, sai Nana ta manta da batun wata Mama, ta hau murnar ganin 'yan uwanta. Nasiru ya je ya É—aukko mata Akwatinta a mota.
Nana ta dake ta ce "Mama ina wuni?"
A dole bisa yaƙe Maman ta ce "Lafiya ƙalau Nana, ai kasa gane ki na yi, irin wannan gwala-gwalai haka. Ai na zata ba zaki sake saka su ba, dan kar ki yi almubazzaranci tun da da muka je fama aka yi ta yi da ke, ki ka ce ba kya so"
Nana ta yi murmushi, tana tuna karatun da Ƙaisar ya yi mata, amma ta ce "To Mama yana iya, masu abu da abinsu, an ce mini haka suke adonsu, idan ka je gari ka ga 'yan gari da jela, aka ce kai ma ka nema ka maƙala. Gaba ɗaya Mama ba ta san baƙin cikinta ya fito muraran ba.
Baba ma da ya dawo ya ga Nana, bakin nan a buɗe ya din ga murna yana yi mata maraba. Babu laifi sun yi nata karɓa mai kyau. Ta yi musu tsaraba mai yawa sosai kamar yadda ta yi wa mutanen Bauchi.
Da daddare suna ɗaki suna ta hir da Jamila, take gaya wa Jamila abun da ta gani a waya, Jamila ta ƙara bata cikakken labarin abin da ya faru, da yadda Hajiya Sa'a take bayar da 'ya'yan Alhaji Fatuhu har ma da rashin lafiyar da Alhaji Fatuhun ya yi sai da ta bata labari. Jikin Nana ya din ga tsuma ta shiga tashin hankali, ta ƙudurce a ranta lallai a washegari za ta je gidan Alhaji Fatuhu, za ta je.
Suwaiba ma ta dage ta din ga yi wa Nana hira, duk da galibin hirar tata shirme ce, tayi baƙi ƙirin duk ta bushe kamar wadda aka tsotse wa sinadaran jikinta.
Gaddafi ma sun sha hira sosai da sosai da Nana. Da Safe da ta ce zata fita sai da Baba ya yi ta mitar daga zuwanta za ta fara yawo.
Amma Nana ta nuna masa fitar ta dole ce, gidan Ummi za ta je. Tare da Jamila suka tafi gidan Alhaji Fatuhu.
Sashen Fadila suka je, sai dai har suka gaisa ba ta gane su ba, har gara Jamila tana ta ƙoƙarin tuna ta.
Yaronta Muhsin ne ya fito ya taso daga bacci, kamarsa É—aya sak da wancan Muhsin É—in.
Nana na ganinsa ta miƙe tana faɗin "La haula wala ƙuwwata illa billah. Banda na zo gaisuwar Muhsin, da cewa zan yi Muhsin ɗina ne nan". Ta yi maganar tana ɗaukar Muhsin tana shafa kansa.
Fadila ta ce "Ya salam, Anty ai sai yanzu na gane ki, malamar Muhsin ko? Ai kin canza kamanni ne gaba É—aya. Tun da ki ka yi aure bamu sake ganinki ba"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.