Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 73 of 99

Nana ta risuna ta ce "Na gode sosai da sosai Abie, Ubangiji Allah ya ƙara girma da sutura, ya kare ku daga dukkanin abin ƙi. Amma ni hukuncin da ka yanke mini bisa adalci da tausayi, da bani damar na rayu da Muhsin da mahaifinsa ya fi komai yi mini daɗi, ina ga ba sai an yi bikin nan ba, har dukiyar auren ma na yafe"

Sultan ya yi murmushi ya ce "Ba biyanki abin da ki ka yi mana zamu yi ba, kyautatawa ce daga gare mu, dan ƙara nuna martaba da daraja da duk wani ɗan Adam yake da shi, fari ko baƙi koma wani kalar launin fata ne. Ina ƙara amfani da wannan damar, gurin ƙara nuna ɗimbin godiyata a gare ki. Kin sadaukar kin jajirce, mun san bamu da abin biyan ki, amma ina kyautata miki zato da yi miki fatan alkhairi"
Nana ta sunkuyar tana murmushi ta kasa magana ma.
"Na ɗauki darussa daban-daban, a kan abubuwan da suka faru, komai sila ne, kuma wasu lokutan bawa baya samun ɗaukaka ko cimma nasara, sai an jarraba shi, wasu lokutan mai sauƙi, wasu lokutan kuma mai tsanani. Allah dai ya baku zaman lafiya na har abada. Shi kuma mai magani Sarkin baka ko? Ya ce yana nan tare da shi za a je Nigeria. Ɗan uwanki ma an ce mini yana Agadez yanzu haka, da Zahradeen ya kai shi karatu, zan saka a kawo mini shi nan, shi ma na yi masa godiya na ba shi haƙuri shi ma"
Nana ta ce "Dan Allah Abie, ka duba girman abin da Imam Zahradeen ya yi, fiye da laifinsa ka yafe masa. "

Yayi murmushi kawai ya ce "Za a duba"

Hammad ma ya ci gaba da yi wa Sultan godiya, dan bai taɓa tsammanin zai yanke wannan hukuncin ba. Sultan ya ce Nana zata iya tafiya, bayan tafiyarta Hammad ya sake yi wa Sultan godiya sannan ya ce "Amma Abie hukuncin nan da ka yanke, ba zai janyo surutu da 'yan majalisar ka ba?"

Sultan ya ce "Hammad, zan yi duk abin da nake ganin shi ne dai-dai, har abada na daina jiran wani ya sarrafa ni, duk abin da nake ganin shi ne daidai zan zartar da shi."

Hammad ya jinjina kai yana sake gode wa Allah. Ya sake cewa "Amma Sultan meyasa ka ce na saki Asal?"

"Me za ka yi da ita? Ko ba ka ji abin da É—an uwanka ya faÉ—a sun haÉ—a kai da ubanta da Bilki suna neman ganin bayanka ba?"

Hammad ya jinjina kai ya ce "Haka ne"

"Amma idan kana son matarka, shikenan ba zan yi maka dole ba"

Hammad ya ce "Ba na son aikata abin da za kalle ni a matsayin mara adalci, amma kamar ku ne ɓoye mini wani abu da kai da Maman Muhsin"

Sultan ya sake yin murmushi ya ce "To idan ma mun ɓoye maka ai ba laifi muka yi ba, tashi ka yi tafiyarka"

*****

Alhaji Fatuhu yaje dubiyar Doctor Sharif tare da Fadila da Suwaiba, sai dai ya tsorata da yanayin da ya gan shi a ciki, tun da ya ga Alhaji Fatuhu yake kuka, amma ya kasa magana, sai da kyar kamar an fizgo maganar ya ce "Ka yi hankali da Alhaji Zailani, kuma ka yafe mini dan Allah" Hakan ma ba komai ake ganewa ba, sai dai maganar ma bata fita da kyau, da kyar suka gane me yake cewa.
Daga bisani suka tafi gidan Hajiya Sa'a, tana kwace a cikin najasa, Alhaji Fatuhu ya din ga yi wa masu aikinta faɗa, yana iƙirarin tun da komai ya fara daidaita, gidansa zai mayar da ita. Sai dai haka kurum ƙasan zuciyarsa ya din ga mamakin wani irin nau'in ciwo ne ake ta fama da shi haka.

Maganar da Muhsin ya yi, yana ƙoƙarin karɓar wayar mamansa, ya sanya Hajiya Sa'a waiwayo wa da sauri ta kalli yaron.

Ayshercool
08081012143

98
1K NE VIA 0069685771
AISHA ADAM STANBIC BANK
08081012143

Cikin mamaki Alhaji Fatuhu yake kallon Hajiya Sa'a, saboda yadda ta ƙure Muhsin da ido.

Ya ce "Yaya Sa'a, kin gane ni? Ko Muhsin ki ka gane?"

"Ba dole na gane wannan tsinannen yaron da Allah ya tsine wa albarka ba? In sha Allah sai ya mutu kuma kun rasa. Da shi ne ya mutu da Abbana bai mutu ba, É—an nawa guda É—aya na rasa shi, ku ga naku nan yana rayuwa "
Cikin rashin fahimta Alhaji Fatuhu ya ce "Yaya Sa'a kin san kuwa me ki ke cewa?"
Cikin tsawa ta ce "Na sani mana, na sani, ina sane. Yanzu ga Abba ya mutu a banza, ni kuma dodon ƙungiya ya shanye mini wasu sassan jikina."
Gaba ɗaya ya yi iya ƙoƙarinsa gurin ganin maganganun da take yi, ba su yi tasiri a zuciyarsa ba. Ya dubi Fadila da ta takure a gefe, tana zare ido ya ce "Fadila, kar fa ku damu ko ku ɗaga hankalinku, kun san ba a hayyacinta take ba, tana fama da matsalar taɓin hankali."
Hajiya Suwaiba ta ce "Duk da haka amma mutum ko ba shi da hankali, yana faÉ—ar abin da yake aikatawa ne, amma babu rami mai ya kawo rami?"
"Ƙaryata ni za ki yi kenan Suwaiba? Meye haɗin Yaya Sa'a da wani shan jini, kawai raɗaɗin mutuwar ɗanta ne yake damunta"
Fafur ya hana su magana, tare da kare Sa'a, duk da ƙasan zuciyarsa maganar Hajiya Suwaiba ta kama zuciyarsa, da ta ce babu yadda za a yi Hajiya Sa'a ta yi wannan maganganu idan bata da alaƙa da su.

*****

Imam Zahradeen ne zaune a gaban mahaifiyarsa Hajiya Bilkisu, cikin kuka take yi masa bala'i "Yanzu Zahradeen har zaka iya fifita bare a kaina mahaifiyarka, ka zaɓi ka tona mini asiri? Yanzu amfanin me hakan ya yi maka daga kai har ni. Duk fafutukar da na yi domin ka ne, amma a ƙarshe ka watsa mini ƙasa a idona. Ka lalata komai abin da nake harin ba zaka samu ba, saboda kai ne gwanin na iya da son burgewa, ka tona mana asiri ga shi kaima baka tsira ba"

"Ban yi duk abin da na yi, domin tozarta ki ba Ammi, duk abin da na yi, na aikata ne domin kaucewa faɗa wa fushin Ubangiji. Bawa bai taɓa isa ya yi wa bawa abin da Allah bai yi masa ba. Duk ƙoƙarin ku Ammi idan Allah bai ƙaddara mu hau karagar nan ba ba zamu hau ba. A yanzu hakan ku nawa ne ku ke fafutuka, ko da an kawar da Hammad, kuma ba zaku samu zaman lafiya da fahimtar juna ba, kowa na sa yake son ya hau. Ammi Hammad fa shikaɗai ne ɗan uwana namiji...
"Tashi ka bani guri, kafin baƙin ciki ya sanya na tsine maka, ka fita ka bani guri" Zuciyarsa cike da ƙuna ya tashi ya bar sashen ta.

Murmushin fuskar Nana ya kasa ɓoyuwa, Ƙaisar shi ma murmushin ya yi, kamar koyaushe gyaran litattafansa yake yi. Ya ce "A karo na babu adadi, ina sake taya ki murna ma a wannan karon, tabbas ko a iya haka kin yi nasara. Kuma aya ce ke mai zaman kanta ga mutanen Agadez ba Agadez ba kawai ga duk wani mai hankali ma. Jaruma ce ke ta gaske uwar gijiyata"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.