Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 17 of 99
Nana ta yi wata irin zabura ta nufe shi da gudu ta ɗauke shi, ta ƙanƙame shi a jikinta, tana zubar da hawaye cikin damuwa da kewar tilon ɗan nata. Shi na Muhsin ɗin, ƙanƙameta ya yi ya fashe da kuka.
Jikin Sayyid ya yi sanyi sosai, ya din ga jin abin da ya aikata bai kyauta ba, kamar ya shiga hakkinsu da yawa, amma babu yadda ya iya ne, hakan ne kawai masalaha a garesu baki É—aya.
Sultan ya kalli Abdou matawalle suka haɗa ido, suka mayar kan Nana da ta durƙushe a gurin tana ta uban kuka.
Matawalle ya yi gyaran murya ya ce "Wannan yaron wane ne shi a gurinki?"
"ÆŠa na ne" Ta faÉ—a cikin kuka.
"Shi kuma wannan fa?" Ya nuna mata Hammad.
"Mijina ne" Ta furta cikin sanyin jiki.
"Waye baban yaron naki?" Ya sake tambayarta. Ta kalli Hammad ta ce "Shine"
"Kin tabattar shi ne mahaifin yaron nan, kuma ke ki ka haifi yaron?"
Ta jinjina kai ta ce "Na tabattar"
"Ya aka yi ku ka haÉ—u ku ka yi aure?"
Ta numfasa ta ce "A Nigeria muka haÉ—u, a can muka yi aure"
"Waye shaidarki cewa mijinki ne shi?"
Takaici ya fara kama Nana, wace shaida kuma bayan wannan É—an wata shaida suke nema?.
"Ni ba ni da wata shaida, Allah ne shaidata sai babana da ya É—aura mana aure."
Sardauna ya ce "Yaya aka yi mahaifin naki ya aura miki wanda bai san daga inda yake ba, ko ku ƙasarku ba ka bincike ku ke aure?"
Jiki a sanyaye Nana ta ce "Ana yi, akwai 'yan uwansa da suke gadi tare, sun san aure muka yi, su Habu"
Matawalle ya ce "Ban gane gadi ba, gadi kamar yaya?"
Hammad ya ce "Ina neman alfarma dan Allah a tsagaita yi mata tambayoyin nan haka, duk a rikice take. Ga wannan wayar akwai video da hotuna a ciki, lokacin da muna rayuwa ne da ni da ita a Nigeria"
Sulta ya ce "Hammad, ya zama dole ka yi mana shiru, a kammala binciken da yakamata, domin tabattar da gaskiyar lamarin nan"
Sardauna ya sake kallon Nana ya ce "Ya aka yi ki ka zo gidan nan yin aiki?"
Ta haɗiye yawu ta ce "Mu na Nigeria lokaci ɗaya na nemi 'yan uwansa na rasa, ya haɗu da larurar zuciya, ina tsaka da jinyarsa na neme shi na rasa. Kawai na yanke shawarar na zo Nijar ko zan haɗu da shi" Mamaki ya kama Hammad, yadda kai da fata taƙi bayanin ainihin ciwon da ya din ga yi bayan hawan jini.
Matawalle ya ce "Ya aka yi da ku ka haɗu ba ki sanar da kowa mijinki ne ba? Kuma me yasa wacan karon da ya kira ki a nan, ki ka ce ba ki san shi ba? Anya akwai ƙamshin gaskiya a maganar nan?"
Imam ya ce "Wancan karon laifina ne, kuma gaba É—aya a ruÉ—e take"
"Ba kai ake tambaya ba, ita muke tambaya" Matawalle ya katse Sayyid.
Cikin kuka Nana ta ce "Dan Allah ku yi haƙuri, ni ba na buƙatar na ci gaba da zama da shi, ku bani ɗa na kawai zan tafi na yi muku alƙawarin ba za ku sake ganina a inda yake ba"
Suka yi tsit suna kallon Nana, daga bisani Sardauna ya ce "Haƙiƙa idan ta tabatta kin auri Imam Hammad, to kun tafka babban kuskure mussaman shi da ya san ƙa'ida da dokar masarauta. Sai dai uzuri ɗaya za a yi muku, shi ne shi ya haɗu da larura, ke kuma ba ki san wannan ƙa'idar ba. Babban mai laifi shi ne Mahmoudu kuma sai ya haɗu da tsatsauran hukunci. Babu buƙatar mu ci gaba da bincike da wani bin diddigi.
Daga nan za a ɗauke ki a kai ki gidan baƙi na musamman, ki huta kwana biyu zamu haɗa miki sha tara ta arziki, za kuma mu sanya a mayar da ke har ƙasarku.
Imam Hammad dole zamu san yadda zamu juya wannan lamarin, mu ɓoye gaskiyarsa, idan haryanzu da aurenka a kanta, zaka sauwwaƙe mata zamu karɓi ɗanmu a mayar da ita Nigeria"
Wani irin mugun kallo Hammad ya yi wa Sardauna. Nana kuwa zabura ta yi tana ƙanƙame Muhsin ta ce "A'a Sayyid ne ɗanku, Muhsin kuma ɗa na ne, ba zan baku ɗa na ba, da shi zan tafi Nigeria"
Matawalle ya ce "Ba zai yiwu ba, mu zamu karɓi Muhsin ki yi haƙuri. Abu ne da muka daɗe mu na nema daga Hammad. Ki yi haƙuri dole mu kare kimarsa da mutuncinsa a Agadez"
Hammad ya miƙe a rikice, jin matakin da za a ɗauka, amma Sultan ya kira sunansa cikin ɗaga murya. Da ido aka yi wa hadimar nan magana, ta nufi Nana gadan-gadan za ta ƙwace Muhsin.
Nana ta ƙara ƙanƙame shi tana kuka cikin ɗaga murya ta ce "Ba zan baku ɗa na ba, ku ƙyale mini ɗa na, baku san baƙar azabar da na sha kan na haife shi ba. Zan bar muku naku ɗan har abada nima ku bar mini nawa" Matar ta fi ƙarfin Nana, Muhsin na zunduma ihu, Nana na kuka ta fizge shi.
Nana ta bita da gudu tana janta "Ki bani É—a na, wallahi ba zan bar muku shi ba. Ba za a kassara rayuwarsa kamar yadda aka kassara ta Sayyid ba".
Wasu hadiman ne maza suka shigo, za su tasa Nana a gaba su fita da ita. Amma mugun kallon da Imam ya yi musu ya sanya suka tsaya.
Ya ƙarasa inda Nana ta riƙe hadimar, ya saka hannu ya cire hannun Nana daga jikin hadimar da ta riƙe gam.
"Ka ce su bani É—a na, kuna ina lokacin da nake gantalin nemanka ba ni da ko muhallin zama da tsohon cikinsa? Ka damu da É—an naka, ka tafi baka sake waiwayata ba? Ka bani É—a na na tafi na barku"
Idanunsa fal hawaye ya ce "Na sani, ki yi haƙuri Ma viee, ba a son raina ba komai ya faru ki yi haƙuri ki saurare ni"
Sai dai tamkar yana ƙara ziga ta, ta ci gaba da cewa "Na yi dana sanin saninka a rayuwata, soyayya da tausayi ba su amfana wa rayuwata komai ba. Da na san abin da zan tarar kenan da na zauna inda Allah ya ajiye ni ban fito neman ka ba. A kan Muhsin zan iya karɓar Ƙaisar da abin da yake so na aikata sai dai masarautar taku ta tarwatse" muryarta tuni ta fara dashewa, saboda ɗaga murya da kukan da take yi mai tsuma zuciya.
Matawalle ya ce "Imam wannan wace irin yarinya ce, mara É—a'a da rashin tarbiyya? Kai ku fita da ita"
"Kar wanda ya taɓa mini mata, zan fita da ita da kaina" Ya yi maganar yana ɗaga musu hannu alamar dakatarwa.
Nana kuwa tuni ta silale jikinta ya saki, ya riƙe ta a jikinsa ba ta iya cewa uffan sai sauke numfashi da take yi kawai.
Sultan ya yi shiru, yana ƙara jujjuya lamarin a cikin zuciyarsa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.