Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 41 of 99

Ayshercool
08081012143

89
LITTAFIN KUÆŠI NE 1K 0069685771
Aisha Adam stanbic
08081012143
A hankali Nana take ƙoƙarin buɗe idanunta, zuciyarta cike da matsanancin tsoron, da rabon da ta ji makamancinsa har ta manta, tare da fatan Allah ya sanya ta farka daga wannan mafarkin mara kan gado. A hankali take jin numfashin sa na sauke a fuskarta. Ta buɗe idonta sosai ta sauke a kan fuskarsa da ya tsare ta da idanunsa, sai dai kan ta yi wani yinƙuri, ƙamshin ɗakin ya mamaye mata hanci, hakan ya sake tabattar mata da ba mafarki ba ne ba zahiri ne. Ta zabura da sauri ta gansu a kan gadon tare ita da shi a cikin ɗakin dai.
A gigice ta fara ƙoƙarin sauka daga kan gadon cikin matsanancin tsoro, tana zazzaro masa ido. Sayyid ya riƙe ta ya ce "Dan Allah ki daina tsorata kanki, ki nutsu mana. Babu wani abin tsoro a gurin nan"
"Ta yaya zan nutsu, kana caza mini ƙwaƙwalwa, na ma rasa me yake faruwa, kuma sannan ka ce babu abin tsoro a gurin"
Ya ce "Zaki fahimci abin da yake faruwar, amma dole ki nutsu, kuma ki saurare ni"  Ya ɗago yatsunsa ya kalli zobunan hannunsa, da space ɗin guda ɗayan sannan ya dubi Nana ya ce "Abubuwan da ki ke gani a tare da ni, su na da alaƙa da wannan zobunan na hannuna. Nana ta kalle shi ta kalli zobunan cikin rashin fahimta.
"Ina Zoben da na baki, mu na Nigeria?" Ba ta ba shi amsa ba, kawai ta hau ƙoƙarin tashi ta bar gurin.
Ya din ga kokowa da Nana, amma idonta ya rufe, hanya kawai take nema ta gudu ta bar gurin. Dan gani take idan ta ci gaba da zama zaucewa za ta yi.
Sai da ƙyar ya  lallaɓa ta ya ce "To shikenan, mu je na mayar da ke mu tafi, tun da ba za ki nutsu ba" Ya riƙo hannunta, sai dai duk a tsorace take, su na fita daga wannan ɗakin ya shiga da ita wani ɗakin.
Gurin duk an yi wearing ɗin fitilu, sai dai da ya kunna fitilun gurin ya yi haske. Ta ƙara razana da ganin gurin. Komai na zamanin da ne sosai da sosai.
Wasu zane-zanen mutane ne a manyan frames a kafe, har zuwa kan wasu hotunan da suke dishi-dishi na Black and white na da, zuwa kan hotunan da ake iya gane mutanen jiki sosai wanda ya nuna na baya-baya ne hotunan sai hoton Sultan da ya fita fes. ÆŠaya bangon Hoton Sultan ne shi ma, da hotunan Imam Imam na Agadez a jere.
Sai dai mutanen na jikin zanen da na hiton duk masu kyau ne, kuma yanayinsu ya nuna daga zuriya É—aya suke.
Sai kuma gefe  wasu ƙananan hotunan a wani ɓangare na ɗakin, da suke nuna yaƙe-yaƙe, da yanayi na zamanin bayi.

Hammad ya ce "Wannan hotunan da ki ke gani, tun daga kan na zanen nan, hotunan wasu daga cikin sarakunan da suka yi gwagwarmaya gurin kafa masarautar Agadez ne.
Waɗannan kuma, wasu daga cikin bayi ne, da suka yi wasu laifuka na rashin kyautawa, wanda tun daga zamanin har kawo yanzu, duk wanda aka haifa a zuriyarsu bawa ne, ciki har da wannan dattijon da yake gadin ƙofar gidan tarihi na Agadez. Idan ya mutu dole zuriyarsu za su bayar da wani wanda zai ci gaba da wannan aikin.

SHEKARUN DA SUKA GABATA.

Kamar yadda Nana ta fara karantawa, a cikin littafin Ƙaisar. An sha gwagwarmaya da yaƙe-yaƙe tsakanin 'yan uwa da suke ciki ɗaya domin samun damar ɗarewa karagar mulki. Kowane Sultan da ya zo karaga, akwai kalar mulkin da yake shimfiɗawa, wani al'ummarsa su samu sassauci, wasu kuma su shiga halin matsi. Sai dai hawa kan karagar ba shi ne aiki ba, ci gaba da ɗorewar mulkin, saboda a kowane lokaci ana iya samun masu kawo maka farmaki, a haɗa kai da na kusa da kai, a yi maka juyin mulki. Sannan tsugunno ba ta ƙarewa duk wanda ya zama Sultan ba, domin bayan kare kansa dole ya kare iyalinsa, idan ba haka ba 'ya'yansa tun da  ƙuruciya za a yi ta kashe su, ana gwara kansu da kwaɗaita musu kwaɗayin mulki, ta yadda idan ba su kashe junansu ba, za su iya kawar da uban dan su hau karagar mulkin.
Ƙasar Agadez Allah ya albarkace ta zinari, wanda tun a wancan lokacin, shi ne babban dalilin da ya sanya kowa ke kwaɗayin ya hau mulki, aka yi ta yaƙe-yaƙe ana zubar da jini, tun da aka fuskanci zinaren abu ne mai matuƙar daraja a lokacin.
Suka ci gaba da gudanar da yaƙe-yaƙe su na mamayar mutane su kafa Daular su. Ana tafe da wannan mulki, wanda mai ƙarfi ya kan kifar da na kan mulkin ya ƙwata, ya kashe na kan karagar, har aka zo kan mulkin Sultan Azhar.
Zuwan Sulta Azhar ya sauya da yawa daga tarihin Agadez, kowane Sultan yana amfani da wani amintaccen boka, da yake yi masa ta'amalli da Aljanu, domin sanin abin da zai faru da ba shi wata kariya ta mussaman.
Sarki Azhar ya gagari duk magautansa, yana da tarin mabiya. Azhar yana cikin manyan kwamandojin yaƙin sarkin wancan lokacin. Kakansa ya taɓa zama Sultan, aka yi masa juyin mulki aka rufe shi a kurkuku. Aka kame 'ya'yansa aka mayar da su fursinoni ciki har da mahaifinsa lokacin shi Azhar yana ƙarami Nono yake sha. Bayan da ya tasa bai fi shekara sha biyu ba, aka kame shi, aka sanya shi cikin sojojin yaƙi. Duk zuriyarsu aka mayar da su bayi, ya tashi da wannan ciwon a ransa, ya zama gawurtaccen Sadauki da ake ji da shi, saboda ƙarfinsa. Ashe yaƙin sunƙuru yake shiryawa Sultan ɗin lokacin ya shammace shi ya kifar da shi, ya ɗare karagar mulkin. Ya kame 'ya'yansa ya kashe su, ya kashe matan Sarkin, har ma da sauran 'yan uwansa da yake tunanin za su iya tasowa su nemi su karɓi sarauta.
Ya din ga yaƙar sauran ƙasashen da ke kusa da Agadez, yana mayar da su ƙarƙashin ikonsa, ya kame baƙaƙen buzaye ya mayar da su bayi. waɗanda suka rage a 'yan uwansa wanda su ma sun tasa, yake ganin za su iya kawo masa tarnaƙi ya sanya aka gina wata irin kurku a ƙarƙashin ƙasa, duk aka zuba su a ciki.
Wannan cikin dutsen da suke ciki, Bayin zamanin Sarki Azhar ne suka rarake shi, suka gina katafariyar fadarsa, kuma a cikinta aka gina kurkun da ya zuba 'yan uwansa.
A cikin kurkukun nan, idan ka mutu a ciki zaka ruɓe ka lalace, a cikin rayayyu za ka gama ruɓewa babu mai fita da gawarka. Babu kalar azabar da ba a ganawa fursinoni a wannan kurkuku. Bayi kuma su na aikin ƙarfi gurin haƙo zinare, da aikinsa a kai wa Sarki Azhar a sarrafa a yi kayan more rayuwa ko a sayar ga maƙwabtan ƙasashen, ko kuma a yi musayarsu da wani abu mai muhimmanci.
Ya kame bokayen ƙasar gaba ɗaya, aka haƙa rami aka cinna musu wuta, a cikin wannan fadar tasa.
Boka É—aya ya bari, wanda shi ne ya tallafa masa ya zama Sultan, wanda shi ma iyayensa na cikin amintattun kakan Azhar da ya yi sarauta, kan a yi juyin mulki a kashe su. Bokan nan ya mallaka wa Azhar gangan manyan Aljanu da suke taimaka masa gurin tafiyar da mulkinsa.
Duk wata kafa da zai iya bari da za a iya amfani da ita gurin kawo ƙarshen mulkinsa ya toshe ta. Sai da ya fara manyanta, sannan ya auri wata kyakykywar matashiyar budurwa. Ta fara haifa masa 'ya'ya maza. Allah ya ɗora masa tsananin ƙaunar yaran nan kamar ransa. Sanin a kowani lokaci, ana iya amfani da wata dama a cutar da su, ya sanya ya killace su. Ya sanya bokansa sadaukar musu da wasu Aljanu da za su din ga yi musu hidima.
Ya sanya doka a kan ko bayan ransa, babu wani wanda zai yi sarauta idan ba a cikin yaran nan ba. Duk dokar da ya kafa, babu mai iya yi masa musu. Babban abin da yake bawa al'ummarsa mamaki bai wuce yadda duk wanda ya fara ƙoƙarin ƙulla wani abu a kan ya kawar da sarkin nan ba, sai dai a wayi gari ya zama gawa.
Sultan Azhar ya shimfiɗa mulki da dokoki yadda yake so, ya tara dukiya da haraji, da kuma arzikin zinarin da Agadez take da shi. Duk da haka ya kamanta kawo ci gaba a lokacin, a wani abin talakawa sun samu sassauci, an samu ci gaba a fannin cinikayya a lokacin, sai dai laifi ƙalilan sai a kai ka kurkukun Sultan Azhar wanda har abada babu wanda zai sake ganinka, idan kuma ya so sai a gadar wa zuriyarku da wata hidima ga fada da kai da iyalinka har abada.
Sultan Azhar bai bar mulki ya mutu ba, sai da ya tsufa sosai da sosai, yaransa sun tasa sun zama matasa. Bayan ya mutu aka naÉ—a babban É—ansa a kan karagar mulki. Shi ma ya É—ora daga inda mahaifinsa ya tsaya, kuma shi bai samu tangarÉ—a da 'yan uwansa ba, saboda ya janyo su cikin harkar mulki.
Sai dai mahaifiyarsu ce ta je ta samu bokan mijinta, ta gaya masa kokenta a kan ba ta son kan yaranta ya rarrabu, a kan mulki, ko wani ya kashe wani.
Ya ba ta tabbacin hakan, ta hanyar yi mata surkulle daban-daban a kan yaran nata.
Kasancewar komai nufin Allah ne, da wanda ya yi addu'a, da wanda ya bi hanyar da ba daidai ba ma, yana iya amsa wa kowa idan ya so, Allah ya taimake ta ba su kashe junansu a kan Mulki ba. Shi ma ya yi tsawon rai a kan karagar mulki, sai dai Aljanun nan sun ci gaba  da bibiyar zuriyar 'ya'yan sarakunan, su na ba su kariya. Bayan mutuwar wannan Sarkin da aka zo naɗa sabon Sarki, a nan aka samu dambarwa, sai da aka yi hatsaniya aka so yin ƙaramin yaƙi daga bisani aka ɗora ɗaya daga jikokin Azhar a kan Mulki wato Sultan Sadam. Har a lokacin matar Azhar tana raye haka Bokansa. Ba ta da wani abokin shawara da ya wuce wannan boka. Ta fuskanci kalubale sosai da sosai, saboda yadda magauta suka sako ta da 'ya'yanta gaba da son tarwatsa mata iyali, dan a banƙara Sarautar ta bar gidansu.
Bayan hawan jikanta karagar mulki, a lokacin Bokan nan ya mutu, ɗansa ya gaje shi. Shi ma ya samu kyakykywan kusanci da Sultan Sadam a lokacin. Bokan ya ba shi shawarar mallakawa 'yan'yansa Aljanu, domin su ƙara samun tsaro daga duk wani farmaki.
Sarki ya yi shawara da bokan, a kan yana son duk yadda za a yi, ya zamana kar sarauta ta bar gidansu, kar wani daga cikin 'yan'yan 'yan uwansa ko 'yan uwansa su yi sarauta.
Sai ya fara da kafa dokar, duk wanda ya haura shekara talatin da biyar, babu shi babu sarauta a Agadez, sai dai ka na kan mulki ka kai wannan shekarun. Kamar yadda ya zo a tarihi da kakansa, da Sultan É—in da ya gabace shi, duk ba su kai shekaru talatin da biyar ba suka hau kan karagar mulki.
Bokan nan ya ƙera masa zobuna da azurfa kowanne yana da mallakin Aljani a jikinsa, da wannan zoben za su iya sarrafa aljanun nan yadda suke so.
Tafi a hankali bayan shuÉ—ewar zamaninsa, abubuwa suka ci gaba da juyawa, kowane Sarkin da zamaninsa da kuma yadda yake nasa mulkin.
Sai dai Mallakar zoben nan ya zama sabon tashin hankali, dan daga bisani sai ya zamana wanda yake da zoben nan, shi ne kaÉ—ai zai iya zama Sarki. Sai faÉ—a ya koma kan kowa na son ya mallaki zobe cikin 'ya'yan Sarakuna. Dan sai Zobunan suka zama gado na kowane gida, daga cikin 'ya'yan Sultan É—in da ya sanya aka ba shi zobe.
A hankali ya zama doka, duk wanda zai zama Sultan, sai ya zamana bai kai shekaru talatin da biyar ba, kuma sai ya zamana ya mallaki wannan zoben.
Duk wanda ya mallaki zoben, yana da damar sarrafa aljanin da aka É—ora wa alhakin É—awainiya da mamallakin wannan zobe, da dole sai ya zamana jinin zuriyar Sultan Azhar sannan zai yi masa hidima."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.