Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 78 of 99

"To ki daina takura mini a kan lallai sai na yarda da abin da ki ke kai"

99

1k ne via 0069685771
Aisha Adam stanbic
08081012143

Har Nana za ta sake magana, Nene ta riƙo hannunta, ta ce "Nana mu koma ciki, ai kin ɗan tattaka, kin san baya son a ganki, ko a gane ki a yanzu. Ɗan uwa idan muka kuma haɗuwa zamu tattauna sosai mu gaisa.

Sosai shirye-shirye suka yi nisa, hankalin Sultan gaba ɗaya ya koma kan shirin zuwa Nigeria da bikin da za a gudanar. Sai dai yana ta fuskantar ƙalubalanta a kan hukuncin da ya zartar.
Gimbiya Bilkisu ta rasa inda zata sanya kanta, ta tuntuɓi Tafawa ta sanar masa da matakin da Sultan ya ɗauka a kanta, amma ya ce mata shi ma ta kansa yake yi, hankalinsa a tashe yake.
Duk yadda ta kai ga ƙoƙarin yin dabarun da Sultan zai saurare ta, fafur ya ƙi ko kallo ba ta ishe shi ba.
Ranar ƙarshe ma da ta je ɗakinsa kamar zai dake ta ya ce "Bilkisu bana ƙaunarki bana ƙaunar ganinki, tun da har za ki yinƙurin sabauta mini rayuwar ɗa, idan ki ka sake zuwa inda nake, sai na yi miki abin da baki taɓa tsammani ba, fice ki bar mini ɗaki kafin na yi miki illa" Abin ya ɗaure mata kai, bata taɓa tunanin zai yi irin wannan fushin har haka ba.

Jamila ta koma gata nan gata nan, ita ba mahaukaciya ba, ita ba mai hankali ba, kuma ita ba mara lafiya ba. Shi Baba gaba ɗaya ma yanzu tsoro suke ba shi. Ya riƙe istigfari ba dare babu rana, gaba ɗaya yaransa sun watse babu wani na kamawa.
Gaddafi ya zo gida, ya tarar da gidan nasu duk wani iri. Yayi mamakin ganin yadda Jamila ta wani rakwakwkwaɓe, jiki babu ƙwari, ta yi wata irin muguwar rama ta fita daga hayyacinta kamar ba ita ba.
Sun dawo daga sallar Asuba, tare da Baba, Baba ya numfasa ya ce "Gaddafi ka ga yadda Allah ya yi da gidanmu ko? Gaba É—aya babu wani mai É—an dama-dama"
Gaddafi ya ce "Na gani Baba, ina son na yi magana dai na fasa, na ga Suwaiba ta daina magana gaba É—aya, har da dalalen yawu take yi. Jamila kuma na kasa gane abin da yake damunta"
Baba bai ɓoye masa komai ba, jikin Gaddafi ya din ga tsuma, ya dubi Baba ya ce "Baba, Jamila ta yi ciki, kuma tana maganar ƙungiyar asiri? Innalillahi wa Innalillahi raji'un"

Cikin matsananciyar damuwa Bab ya ce "Babarta ta ce zafin ciwo ne, amma na kasa yarda nima" Ya yi maganar yana zubar da hawaye.
Gaddafi ya ce "Shiyasa Baba na din ga maganar kuɗin da ta din ga ta'amalli da su, amma mahaifiyarta ta nuna ba ta so, ta nuna baƙin ciki nake yi, da ci gaban Jamila ka ga irin abin ko? Shikenan sun lalata mana gida"
Baba ya yi kuka ya ce "Ina kyautata zaton hakkin yaran nan ne, su Nana, dan sai daga bayan nan, nake duba wasu abubuwan da na aikata musu na ga sam babu adalci a cikinsa. Amma wasu mutane sun zo wai daga Agadez sun ce mini tana gurinsu" Nana Baba ya gaya wa Gaddafi abin da su Mahmoudu suka zo masa da shi.
Gaddafi ya rikice ya ce "Baba kuma baka karɓi lambar wayarsu ba ko ka bi su ba?"
Baba ya girgiza kai ya ce  "Ban karɓa ba, ni tsoro ma na ji, ji nake kamar ƙarya suke yi. Na bar wa Allah ikonsa"
"Amma Baba akwai mamaki a cikin abubuwan da suka faɗa, masu sarƙaƙiyar gaske"
Baba ya ce "To ai shiyasa ban ma gazgata ba, sai abin da hali yayi"
Gaddafi ya ce "Ba wani abu, in sha Allah mu tsammaci alkhairi"
Baba ya jinjina kai cike da gamsuwa.

****
Nana ce a tsaye, tana kallon Ƙaisar, yana zuba wa wata tsuntsuwa abinci a cikin keji.
Nana ta kalli tsuntuwar ta ce "Ƙaisar ita kuma wannan fa, a ina ka samo ta?"
Ba tare da ya kalli Nana ba ya ce tsinto ta na yi a daji, za ta mutu, ban zaci ma zata rayu ba, sai kuma na ga ta farfaÉ—o yanzu ta ware ma"
Nana ta ƙarasa gaban kejin ta zauna, sannan ta ce "To kuma tsuntsuwa ce ita, ko kuma aljana ce?"
Ya kalli Nana ya ce "Dama akwai tsuntsu mutum da aljan ne?"
Nana ta É—an yi shiru tana kallon tsuntsuwar.
Ya ce "Mutum jinsinsa daban, aljani daban, haka ma tsuntsu daban. Babu Aljani tsuntsu sai dai Aljani ya shiga jikin tsuntsun, ina fatan kin gane?"
Ta gyaɗa kai, ta ce "Haka ne, wai ni kuwa Ƙaisar ina Haulat? Ka fara son nata?"

"Ban sani ba" Ya yi maganar yana hararta.

Nana ta yi murmushi ta ce "To shikenan kai ba zaka yi aure ba kenan? To sonta ne baka yi ko kuma me ta yi maka?"
Yayi mata shiru, yana rufe kejin tsuntsuwar nan.
Nana ta numfasa ta ce "Ƙaisar ina kewar gida fiye da tunani, zuciyata kuma ta cika da fargabar rashin sanin abin da zan je na tarar. Ina jin kunyarsu ban san da wani idon zan kalle su ba. Duk da Imrana ya haɗa ni da Mama, ta yi mini Addu'a ta ce na kwantar da hankalina, amma kunyarsu nake ji ban kyauta ba abubuwan da na yi"
Ya ce "Za ki tarar da alkhari in sha Allah, da abun da zai yi miki daÉ—i da wanda ba zai yi miki ba. Ni na din ga shagaltar da ke daga tunaninsu, da tunaninsu ya yi tasiri a zuciyarki, da ba ki cimma wannan nasarar ba, da kin rushe komai, dan idan ki ka koma gidan babu abin da zai canza"

Cikin mamaki Nana ta kalle shi ta ce "Ban gane ba, kai ne ka sanya na daina jin damuwar da na din ga ji a baya, da son komawa gida?"

"Sosai, saboda ruhi ne mu, mu na iya shiga ko ina a jikin ku, kuma muna iya hargitsa tunani da sanya muku rashin nutsuwa"

Ta yi shiru tana nazari, ta sake cewa "Ƙaisar ka sanya ni a fargaba, abin da zan tarar a gida da gaske mara daɗi ne? Kodayake ko ka gaya mini ma idan na tashi na san mantawa zan yi sai abin da na je na tarar kawai"

"Kin yi zaton da mugunta kawai nake nuna miki abu na mantar da ke ko?" Nana ta jinjina kai.

"Ba haka ba ne, duk da ta wani fannin haka ɗin ne, muguntar ce da takaicin ƙin yarda da abin da na zo miki da su.
Mafarki ya kasu kashi-kashi, duk da shi ma ina kan bincike a kansa. Akwai mafarkin da yake daga Allah ne, akwai mutanen da akan yi wa ishara a cikin bacci, na kusantowa ko kuma faruwar wani al'amari da bai faru ba kwata-kwata. Wasu kuma a nuna musu makamancin abin, wasu kuma su ga abu a duƙunƙune sai an fassara musu.
Galibi waÉ—anda aljanu ke nuna wa mutum a mafarki, na haÉ—in faÉ—a ne. Abu ne da aka yi shi a bayan idon mutum bai san an yi ba, sai su nuna masa. Kuma ba su fiye nuna abin alkhairi ba sai akasin haka. Wasu idan sun gani su na iya shiru da bakinsu, wasu kuma basa iyawa sai sun faÉ—a. Sai su sanya a din ga yi wa mutanen wani kallo na daban, wasu a dole dalilin hakan kan sanya su fara bayar da magani.
Ke na biyo miki ne ta hanya mai sauƙi, saboda bana son tilasta miki, na fi son ki amince da kanki. Sai na nuna miki abin da ya faru da baki sani ba, ko kuma wanda yake shirin faruwa, ko wanda nake hasashen abu ne mawuyaci bai faru ba. Akwai abin da idan na ƙyale ki, ki ka tashi da shi a ƙwaƙwalwarki, ba za ki iya yin shiru ba, za ki yi yinƙurin ɗaukar mataki, wanda hakan ka iya haifar da fitina, saboda idan ki ka haifar da matsalar ba ki da maganinta, tun da ba ki amince da bayar da magani ba.
Ɗan Adam kuna da nau'in ciwo na gangar jiki, da kuma na ruhi, amma ba kwa damuwa da ciwon da yake damun ruhinku, kun fi damuwa da na gangar jiki. Mutum zai iya kashe maƙudan kuɗaɗe, a kan lafiyar gangar jikinsa, amma sam wani baya yadda ma ruhinsa yana rashin lafiya."
Nana ta ce "Nima ban gane ba"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.