Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 35 of 99
Asal ce a gaban Sultan, tana ta uban kuka, fuskar nan ta yi jawurr, idanunta sun kumbura sosai da sosai.
Sultan ya yi shiru, saboda yadda abubuwan shi kansa suka kulle masa kai. Gaba É—aya bai yi tunanin abubuwan za su damalmale har haka ba, ya ma rasa ta ina zai fara.
Ya ce "Ki na ji na Asal. Wannan maganar abu ne mai faɗin gaske, da ko ba ki gano ba, dole za a yi miki bayani. Amma wannan bayanin ba ke kaɗai yakamata mu yi wa ba, a gaban mahafinki yakamata mu yi shi. Tabbas da gaske Imam Hammad ba shi da lafiya, kuma ke ma shaida ce, saboda kin zo kin gan shi a halin da yake ciki. Sai dai ita wannan yarinyar tana da alaƙa da samun sauƙinsa. Yanzu bayanin da zan yi miki ba za ki gane ba, ina son sai mun zauna gaba ɗaya za mu yi miki bayani. Amma ki samu nutsuwa ki kwantar da hankalinki.
Gaba ɗaya Asal ba ta fahimci abin da Sultan yake gaya mata ba, gani take kawai yana ƙoƙarin goyon bayan ɗansa ne.
Muryarsa ta sake tsinkayowa yana faÉ—in "Kar ki bari kowa ya ji maganar nan, sai mun zauna an yi miki bayani tukuna dan Allah." Ya dubi Imam Hammad ya ce masa ya kai Asal gida, ya rarrashe ta, ta samu nutsuwa kafin a yi mata bayanin komai.
Nana kuwa kajin gurin Nene ta samu ta ci, saboda taga alamun idan ta biye ta kishin nan, yunwa ce za ta kar ta a banza, duk da yanzu naman duk ya ishe ta, abinci take so ta ci sosai. Ga shi ta yi zaton ko zai dawo mata da Muhsin, amma bai dawo mata da shi ba.
Ba ta sake ganin Hammad ba, sai bayan sha É—aya na dare. Idanunsa jawur da alama yana cikin damuwa kuma ko abinci ba ta tunanin ya ci. Sau É—aya ta kalle shi ta basar, ba ta ko kula shi ba.
Gani ta yi ya cire rigar jiknsa ya yar a ƙasa, ya hau kan gadon ya kwanta, ba ta motsa ba ta ci gaba da zamanta, dan haushinsa ne ma ya kama ta. Jin ya fara numfarfashi ya sanya ta tashi tsaye. Ta kalle shi ta ga ya fara komawa ja. Sai kuma jikinta ya yi sanyi, abin da ta lura da shi kamar ciwon ya fi tsananta masa a Niger.
Ta fara ƙoƙarin ninke masa rigar, kawai wannan takardar ta faɗo daga aljihun rigar. Ta ɗauki takardar ta yi shiru tana kallon takardar.
Ta hau kan gadon ta juya shi da kyar, taga yana ta taune leɓensa yana jujjuya kansa.
"Ki yi mini addu'a, zan mutu" ya furta da kyar kamar numfasihinsa zai É—auke. Suratul Fatiha ta din ga karantawa da Bismillah tana tofa masa. Fizge-fizge ya fara yana girgiza kai ya ce "Tashi mu tafi"
Cikin rashin fahimta ta ce "mu je Ina?"
"Ki tashi nu tafi, kafin na rasa raina" Ya ƙarasa maganar yana dafe kansa da yake jin kamar zai yi bindiga. Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin aka yi. Amma ba damar Nana ta tashi, saboda yadda ya rirriƙeta. Ga shi ta san ko ta ce a shigo babu lallai a jiyota daga waje.
Mai bugun ne ya gaji da bugawa, ya turo ƙofar, Sultan ne tare da wata babbar mace fara solnda ita. Sai kuma Mahmoudu.
A rikice suka ƙarasa gaban gadon, cikin tashin hankali Sultan ya ce "Jikin ne?"
"Ki tashi mu tafi, zan rasa raina, ƙwaƙwalwata za ta tarwatse. Ki yi mini addu'a"
Tuni Nana ta fara kuka, ta ce "Ina yi maka, kai ma ka din ga yi ko a zuciyarka ne. In sha Allah babu abin da zai same ka"
Matar ta ce "Wannan ce matar tasa?"
Sultan ya jinjina kai ya ce "Ita ce"
Ta ce "Ikon Allah, lallai Allah gwani ne"
Mahmoud kuwa jiki a sanyaye ya ce "Sannu Imam"
"Hamud, dan Allah ka É—auke ni ka sake tafiya da ni, ba na son zaman garin nan, ba ku san me nake ji ba."
Mahmoudu ya kalli Sultan ya ce "Ranka ya daÉ—e, a irin wannan yanayin fiye ma da wannan, na bar Niger da shi a wancan lokacin. To kuma na ga alamar jikin na neman sake dawowa.
A hankali ya fara fita hayyacinsa, ya fara lanƙwasa Nana, ta rintse idanunta Sultan ya ƙarasa da sauri yana faɗin "Kai kar ka yi wa 'yar mutane illa, Hammad" Mahmoudu rasa abin yi ya yi, dan ya san ganganci mafi girma da zai aikata shi ne ya taɓa jikin Nana garin ƙoƙarin ɓanɓare shi daga jikinta.
Sai kuma Sultan ya ja ya tsaya shi ma ya rasa abin yi.
"Ke kin san me nake ji ai" ya sake futawa cikin ƙarfin hali.
"Na sani, shi ya sanya nake yi maka addu'a"
Sultan ya ce "Hammad, kar ka ji mata ciwo fa"
A hankali Nana ta ce "Ba zai ji mini ba in sha Allah"
Addu'a ta ci gaba da yi masa, tana tofa masa. Sultan kam kasa jurewa ya yi, saboda ba ƙaramin tashin hankali yake shiga ba, idan ya ga ɗan nasa a cikin wannan yanayin.
Sai kusan ƙarfe biyu na dare sannan ya dawo hayyacinsa gaba ɗaya. Ya yinƙura ya tashi zaune yana kallon Nana.
Ta ce "Sannu. Ka daina jin abin da ka ke ji É—in?"
Ba ta yi zaton zai iya magana ba ta ji ya yi, ya ce "Ina ji amma ya lafa mini"
Ta ce "To Allah ya baka lafiya ingantacciya. Amm ka yi haƙuri kana cikin yanayin larura zan tambaye ka abu" ya yi shiru yana kallon ta.
Ta É—ago masa wannan takardar ta ce "A cikin rigarka na ganta, waye ya saka maka ita?" Ya girgiza kai ya ce "Nima ban sani ba"
Ta sake cewa "Shekaranjiya wani abu mai kama da mafarki ya faru, har muka fita ta wata ƙofa, gaske ne ko kuma mafarki nake yi?"
"Gaske ne" Ya bata amsa kai tsaye.
"Ina buƙatar fahimtar wasu abubuwan, dan ka na yin abubuwan da ba kowane ɗan Adam ne zai iya ba. Tun mu na Nigeria ka ke yin wasu abubuwan. Kuma ina buƙatar na ji abubuwan da suka faru wanda ban sani ba" Ya numfasa ya ce "Zo ki raka ni shan iska tukuna" Suka sauka daga kan gadon. Ya zira rigarsa ya buɗe ƙofar nan, suka ƙara ratsa duhu suka fita wannan corridor.
Yau ma saharar ta gani, gurin ya É—auki sanyi sosai da sosai. Ta kalli Wannan tsaunin dake gefen saharar ta ce.
"Wai mene ne a cikin dutsen can, shi nake son sani"
Ya kalli gurin ya ce "Nan ne ainihin inda kakanninmu suka fara mulki, dan haka duk wani kayan tarihi, a ciki a ke adana su"
Nana ta ce "To ka gaya mini abin da na tambaye ka, kuma ina son ka kai ni na ga abubuwan tarihin garin naku"
"Zan kai ki, kuma zan yi miki bayanin amma yanzu ba na jin daÉ—i"
Ta É—an shafa bayansa ta ce "Sannu" ya jinjina mata kai. Ya matsa kusa da ita, ya rungume ta, sanyin gurin ya din ga ratsa su a tare.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.