Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 64 of 99
Ya miƙe tsaye ya ce "Murnar komai ma, alamu sun nuna Ubangiji yana sonki, tsananin da ki ka din ga shiga, ya zame wa wasu silar alkhairi, kuma sannu a hankali Allah yana warware miki komai"
Ta É—an yi shiru ta ce "Ban fahimci me ka ke nufi ba"
Ƙaisar ya ce "Ba sai kin fahimta ba. Ina taya ki murnar ganin ɗan uwanki, sai dai haryanzu da ɗan sauran rina a kaba. Shi wannan mijin naki, zuciyarsa da karsashinsa a kanki kawai yake. Amma bai damu da tsayuwa tsayin daka a kan abubuwa ba, ya kan karɓi abu duk yadda ya zo masa, ya tafi a haka komai zafi da raɗaɗin cutarwar da abin yake yi masa.
Kar ki kuskura Sarkin baka ya tafi, baku bankaɗo abin da yake faruwa da shi ba, sannan Giyaz haryanzu yana tare da shi, sai dai a galabaice yake yana jinya. Kin san bamu fiye saɓa alƙawari ba, dan haka abu ne mawuyaci ya rabu da mijinki ta daɗin rai, saboda yarjejeniyar da suka yi da bokan nan.
Kamar yadda na sanki, ki ci gaba da addu'a, zan iya cewa kusan komai ya zo ƙarshe, sai dai ban san abin da ka iya faruwa a gaba ba."
"Ma vie" Ya yi maganar yana shafa fuskarta, a hankali ta buÉ—e ido ta kalli Sayyid, ta sake É—aga kanta, ta ganta a jikin Imran. Kuka take sosai da sosai, da ita kanta ta kasa tantance ko na mene ne.
Imrana da yake share hawayen ya ce "Ki yi haƙuri ki daina kukan nan haka"
"Kukan ne yake zuwa" Ta yi maganar wasu hawayen na ci gaba da zubowa.
Ya kalli Muhsin da yake ta guje-guje a É—akin, ya kalli Imam Zahradeen ya ce "Wannan ne É—an nata?"
Ya yi murmushi ya jinjina masa kai.
Nana ta sake cewa "Imrana ya aka yi ka san ina nan?"
Ya yi murmushi ya ce "Bacci na kwanta, kawai na farka na ganni a nan"
Kukan da take yi bai hana ta yin murmushi ba. Ta ce "Nene kin ga yayana, duk duniya shi ne kaÉ—ai wanda muke ciki É—aya da shi"
Nene ta ce "Allah sarki, ga kammanni nan ku na yi da shi"
Imam Zahradeen ya ce "Yakamata a fara ba wa baƙi"
Nana ta ja jikinta ta zauna, ta ƙure Imrana da ido, gaba ɗaya ya nutsu, babu wannan hauma-haumar tasa.
Shi kansa Imam Hammad kallon Imam Zahradeen yake cike da mamaki yana jiran jin bayani daga bakinsa.
*****
Jamila ce a durƙushe tana wani irin kakari, ji take yi tamkar barin duniyar za ta yi saboda matsananciyar azabar da take ji. Ta ɗaga kai da kyar ta kalli Mama, a galabaice ta ce "Mama, me ki ka bani a cikin kukun nan na sha, Mama zan mutu zan rasa raina"
Mama ya ce "Ai gara ki mutun na huta Jamila, gara ki tafi asirina ya rufu da wannan masifar da ki ka ɗaukko mini. Ba dai ke taurin kan tsiya ba, ai na san yadda zan yi da ke nima. Ƙwayar zubar da ciki na je na sayo a gurin Mariya Likita na zuba miki, dan ba za ki haife mini shege a gida ba".
Jamila ta girgiza kai cikin matsananciyar azaba ta ce "Mama ba ki kyauta mini ba, zan iya rasa rayuwata Mama, kin san azabar da nake ji kuwa?"
"Tun da ki ka iya jure miƙawa maza jikinki, dole ki jure azabar fitar cikin"
"Wayyo Allahna" Ta faɗa a marairaice tana sake durƙushewa cikin azababben ciwo.
*****
Fadila ce ta fito daga banɗain da ta shafe a ƙalla awa ɗaya da rabi a ciki, tana tufaka da warwara, sosai an matsa musu a kan su tashi su bar gidan. Har ta gaji da zuwan da wanda ya sai gidan yake yi yana ɗaga musu hankali kamar ba abokinsa ne ba. Ga shi haryanzu bai gama samun cikakkiyar lafiya ba, lallaɓawa kawai yake yi, shi kansa ya rasa inda zai sanya kansa saboda damuwa, ƙarfin hali kawai yake yi.
Tana fitowa ta tarar da shi a tsaye da waya a hannunsa. Cikin damuwa ta ce "Lafiya kuwa?"
A sanyaye ya ce "Coustom ne suke nema na a Lagos"
Ta É—an yi saroro ta ce "Suke neman ka kuma, lafiya dai?"
Alhaji Fatuhu ya ce "Wallahi ban san mene ne ba, ga shi ko kuÉ—in motar tafiya ba ni da su. Allah ya sa ba wani abin ne mara daÉ—i ya sake tasowa ba"
Fadila ta ce "Jikina ba ya bani wani mugun abin ne, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi ne ya sanya suke neman ka. Bari na kira Umma idan da kuÉ—i a hannunta ta ara mini"
Ya ce "A'a, kin san ba shi ne da ita ba, ba dan halin da Alhaji Zailani yake ciki na ɓatan 'yarsa ba, ai da shi zan cewa ya biya mana, ya raka ni muje mu ji ko mene ne"
Ta ɗan tsuke fuska ta ce "Dan Allah Daddy ka daina gayyato mutanen nan haka, mu din ga shiru tukuna idan alkhairi ne idan Allah ya tabattar sai kowa ma ya ji. Da za a samu kuɗin sai Umman su Raudha ta raka ka. Amma hakan nan za ka yi haƙuri mu nemo kuɗi ko ta mota ne ku tafi tare. Ya hayyu ya ƙayyum Ubangiji Allah ka sanya alkhairi ne.
Ya amsa da "Amin."
****
Gaba ɗaya Shukura ta yi saranda da da ba zata tsira ba, daga ita har jaririnta, Yusra ta ce mata duk za ta yi ta nemi guri ta ɓuya, ba za ta iya fitar da ita da jaririn lokaci ɗaya ba, ta fuskanci mutanen nan, su na harabar inda Asibitin yake.
Shukura na kuka ta ce "Yanzu tafiya za ki yi ki bar ni?"
Yusra ta ce "To yaya za mu yi, idan ba haka ba daga ke har jaririn za ku iya rasa ranku, ki bari na fita da jaririn, ki san duk yadda za ki yi ki ɓuya ko ki gudu. Amma Shukura suwaye wannan suke binki haka? Kuma me ki ka yi musu?"
Shukura na kuka ta ce "Dogon zance ne, ke dai tafi da shi, idan ban rayu ba ma dan Allah ki kula mini da shi"
Yausra ta bata mukullin motar da ta zo da ita ta ce "Idan kin samu dama, ki gudu ni zan san yadda zan yi" ta goya jaririn Shukura na kuka, Yusra ta fice daga É—akin.
****
Imran ya ci gaba da kallon Nana cikin zallar farin ciki da shauƙi, tare da kallon Muhsin dukkaninsu cikin shiga ta alfarma da kamala.
Ya ce "Nana, ashe zan gan ki cikin farin ciki da kwanciyar hankali haka a rayuwata? Allah na gode maka da ban tursasa ki na kashe miki aure ba, ashe alkhairinki yana tattare da auren.
Kasancewar daga Nana sai shi a ɗakin, ta ɗan jinjina kai ta ce "Amma an sha gwagwarmaya Imrana, duk da na gode wa Allah da ka bayyana yanzu, ka zo a gaɓar da na fi tsananin buƙatar ka, amma meyasa ka yi fushi da ni baka sake dawowa ba, dama akwai abin da zan yi maka ka yi irin wannan fushin da ni?"
Ya girgiza kai ya ce "Babu shi, abin da za ki yi mini da zai sanya na guje ki. Amma ki yi haƙuri kaɗan za ki ji abin da ya faru. Na yi burin na samu wadata ki huta na gatanta ki Nana, amma Allah ya ƙaddara ke ce zan huta a dalilinki."
"Ban gane ba, me ka ke nufi?"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.