Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 52 of 99
Hammad ya ce "Waye kai?"
"Arun, bawan aljani ga Sultan Azhar, wannan tagullar mallakinsa ce, kuma ni mai hidima ne ga ma mallakin tagullar"
Hammad ya zuba ido sosai, ya ga ɗan abin tsoho ne tukuf sosai da sosai. Domin kuwa gemunsa ƙasa yake ja.
Ya ce "Amma da idan na murza zoben ba kai nake gani ba"
Arun ya ce "Ai ba ni ka ke kira, hadiman wancan zoben daban, nima kuma daban"
"To ina zoben nawa yake?"
"Ka yi kyautarsa ga wanda ka ke matuƙar ƙauna a matsayin tukuicin soyayya"
Hammad ya ce "Soyayya kuma? Ni É—in?
"Ƙwarai ya shugabana"
"To wa na bawa, kuma yaushe na yi soyayyar, kuma mace ce ko namiji?"
Arun ya sake cewa "Ba na son shiga hurumin da ba nawa ba, ina gudun sake rura wutar fitinar da ke tsakanin gangar jiki buyi, ruhika huɗu, alaƙa huɗu. Gangar jiki ta mutum biyu, ruhi huɗu, na mutum biyu da na aljan biyu, sai kuma alaƙar mata da miji da kuma uba da ɗa, sannu a hankali duk za ka fahimci abubuwan da nake nufi" Daga nan ya ɓace Hammad ya yi shiru yana juya maganganun da suka fi yi masa kama da shirme.
Ya tashi ya fita falo, ya san lokacin kawo masa shayin dare ya yi, sai dai tun kafin ya ƙaraso cikin falon yake jiyo sautin muryarta tana waƙa. Daga nesa kaɗan ya tsaya yana kallonta, yana jin yadda zuciyarsa take bugawa da sauri.
*_ina zana ganka_*
*_saƙo zana baka*_
*Hotona da naka*_
*_Ko ina zana bika*_
*_Kowa tsane ka, ni na tsane shi sanya a ranka*_
*_Zuciyata na baka duk masu ƙin ka su daina shakka*_
*_Rayuwata na baka_*
*_Ni ta ya zan guje ka*_
*_Ka dawo gare ni dan zuciya ta bar kewa*_
Gaba ɗaya sai ya daskare a gurin, gumi ya din ga tsatstsafo masa, ƙwaƙwalwarsa ta shiga Kai komo, kansa kamar zai yi tsawa ya fashe. "Tabbas akwai wani abu, ya san wani abu mai kama da haka, amma yaushe? Kuma a ina?"
Ya daɗe a tsaye a gurin, kafin ya saita nutsuwarsa ya shiga falon. Murmushi ta yi ta daina waƙar da ta ga ya fito ta risuna ta ce "Barka da dare"
Ya jinjina mata kai.
"Sayyid ga shayinka nan, ina fatan na kammala komai, zan iya tafiya?" Ya yi shiru yana jujjuya Sayyid da take kiransa da shi.
Washegari da sassafe ya kira Mahmoudu a waya, ya sanar masa da yana son ganinsa za su yi magana.
Amma Mahmoudu ya ce masa yana hanyar MaraÉ—i, zai kai wa Nene ziyara ne.
Hammad ya yi ta mitar me yasa bai gaya masa su tafi tare, su je su gaishe ta, ya ba shi haƙuri.
Sai dai tun da Mahmoudu ya je ya ga Muhsin ya rikice, ya din ga yi wa Nene tambayoyi a kan Muhsin, amma ta ƙi gaya masa haƙiƙanin gaskiyar waye Muhsin.
Sai dai yanayin yadda ta ga Mahmoud ya rikice, ya sanya ta tabattar da ya ga abinda take tunani ita ma.
Kwanansa É—aya ya shirya ya nufo Agdez bayan ya faki idon Nene ya É—auki hotunan Muhsin. Ya nufi Agadez da nufin komai zai faru sai dai ya faru.
Hammad kuwa ya lallaɓa Asal ya yi mata wayo ya sanya ta dawo da Nana sashen su, ba tare da ta kawo komai a ranta ba. Amma shi a jikinsa yana jin baƙin abubuwa game da 'yar Nigeria da jikinsa bai ba shi cutar da shi za ta yi ba, amma kasancewarta daf da inda yake yana samun nutsuwa da nishaɗin kallonta.
Tun da Mahmoudu ya dawo, Hammad ya lura bakinsa akwai magana, amma ya ƙi ce masa komai.
"Mahmoudu na lura bakinka akwai magana, amma ka ƙi gaya mini, duk da ba ma 'yar haka da ni da kai, amma bari ni na gaya maka tawa damuwar".
Mahmoud ya ce "Ni babu wani abu da zan gaya maka, amma gaya mini mene ne yake damunka?"
"Ina kukun da nake gaya maka Asal ta samo 'yar Nigeria?" Gaban Mahmoud ya faÉ—i amma ya dake ya ce "Eh meyafaru?"
"Wasu abubuwa nake ji game da ita, da tun da nake ban taɓa ji game da wani mutum ba"
Mahmoudu ya yi murmushi ya ce "Ko santa ka ke yi ne?"
"Anya kuwa, ban dai sani ba, amma ba normal mutum ba ce"
"Ka na da mata fa a Nigeriar nan"
Hammad ya kalle shi yana jiran ƙarin bayani. Mahmoudu ya ce "Da wasa nake yi, na dai ce zan aura maka 'yar maka 'yar Nigeria idan ka na so. Amma ina da wani abin al'ajabi da nake son nuna maka, amma tashi mu je ka shirya, ka ce mini za ku yi hawan raƙuma kar a yi ta jiran ka" Babu musu ya tashi suka fita. Kowanne a cikin su yana ta saƙe-saƙe a cikin zuciyarsa.
Sai dai bayan an yi hawan raƙuman, da Hammad ya faɗo tare da Mahmoudu aka dawo da Hammad gida. Sai dai ya yi mutuwar tsaye, da hango ta tana leƙen mutanen da suke kaiwa da komowa a falon fuskarta ɗauke da damuwa.
A jere zuciyar Mahmoudu ta buga, addu'a ya fara yi, a kan Allah ya sanya ba mafarki yake yi ba, ko kuma tsabar saka abin a ransa ne ya sanya ta fara yi masa gizo ba.
Ayshercool
08081012143
93
93
LITTAFIN KUÆŠI NE, KI BIYA KUÆŠIN KARATU KAFIN KI KARANTA.
08081012143
Cikin hanzari Habu ya ja rawaninsa ya nufi barin falon, yana daf da fita Nana ta waiwaya ta ga wucewarsa, sosai ta tsaya tana kallon bayansa har ya fice tana yi masa kallon sani.
Washegari da safe Bayan Tafawa ya zo duba shi, ya tafi zuciyarsa a cunkushe babu daÉ—i, saboda kausasan kalaman da Tafawa ya yi amfani da su, har da ce masa ko shaye-shaye yake yi, shi ya sanya ya faÉ—o daga kan Taguwa.
Wajen ƙarfe sha ɗaya, da ya ji sauƙi, ya lallaɓa ya fito, yana mamakin dalilin da ya sanya Nana hana shi hawa kan Taguwa, da ya hau kuma ya faɗo. Yana fitowa ya tarar da ita da Asal su na mujadala. Sai dai hangota kawai da ya yi, sai ya ji wani sanyi a ransa.
Nana ce take kallon Asal cikin takaici, bayan da Asal ta ce mata ta din ga sanya da hadiman gidan suke sakawa.
Nana ta rasa dalilin da ya sanya Asal ke son ƙasƙantar da ita ko ta halin ƙaƙa.
Nana ta dube ta ta ce "A gaskiya ba zan iya sanya kayan da hadimai suke sanyawa ba, ko ki haƙura ki kalle ni da kayan jikina, ko kuma ki sallame ni. Tun da ni ba baiwarki ba ce ba, aiki kawai ki ka ɗaukko ni na yi miki"
"Idan na so mayar da ke baiwar tawa ina da halin yin hakan, ke kin san ina da abin da ko nawa za a yi miki kuÉ—i zan iya bayarwa na saye ki"
"Ko da Goma ta lalace a gaban biyar take har gaban Abada Gimbiya Asal. Kuma wani garin ya fi gaban kunu. Ba ki da arzikin da za ki Asma'u a matsayin baiwarki" Nana ta ƙarasa maganar a zafafe. Hammad ya yi gyaran murya, suka tsaya Asal ta haɗiye maganganun da ta yi niyyar caɓawa Nana.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.