Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 94 of 99

"Mmm" ya amsa da kyar.

"Mene ne, me ya yi maka?"

Ya girgiza kai ba tare da ya buÉ—e idanunsa ba.
Da su Sultan suka dawo, suka tarar da ita hankali a tashe.
Matawalle ya ce "Ki kwantar da hankalinki, zai wartsake a hankali in sha Allah. Ya ce sai dai mu kwana a nan, mu ga yanayin jikin nasa tukuna, sannan kema ya duba ki"
Kasancewar mutumin babban malamin ruƙiyya ne, da magungunan musulunci yana da gurin saukar baƙi, saboda yadda ake zuwa daga garuruwa gurinsa.
Sannu a hankali Hammad ya dawo hayyacinsa, har ya yi salla ya ci abinci, amma kana kallonsa zaka gane ba ya jin daÉ—i. Nana dai ba ta iya tambayarsa komai ba.
Sultan ya tambaye ta, za ta iya kwana da shi, ko a bata wani É—akin, ta ce zata iya zama tare da shi.
Ba da wani shiri suka taho ba, kasancewar ba su san za su kwana a gidan ba. Gidan Sarkin baka ne ya faÉ—o mata, da irin gane-ganen da ta yi a gidan.
Ta nemi guri ta kwanta a kusa da Hammad, ta ji ya matso da ita jikinsa, ya ƙanƙame ta.
Kamar wadda ta farka daga bacci, haka ta ganta a Libraryn Ƙaisar.
Sai dai gurin ya ɗan yi duhu, sheshsheƙa ta din ga jiyowa daga wani guri, ta tafi a hankali tana sanɗa. Tana buɗe ƙofar da take jiyo sautin ta ga wani irin ƙaton guri, Ƙaisar na durƙushe a kan gwiwoyinsa, ya saka wani abu dogo da ba ta san ko menene ba a gabansa, yana wani irin kuka. Da sauri ta ƙarasa gabansa, ta gefen mayafin take hango wani abu baƙi ƙirin kamar an ƙona itace.
Sandar Giyaz ta gani kwance a gefen abin da yake gaban Ƙaisar ɗin, a razane Nana ta ce "Giyaz ne ya mutu?"

Kawai Ƙaisar ya sake fashewa da kuka, yana yaye mayafin da ya rufe Giyaz. Ya yi wani irin baƙi kamar dutse yayi gobara. Ga wani irin tsawo mara misali da yayi, sai gemunsa da ya ƙara wani irin tsawo. Nana ta ja da baya a razane. Ƙaisar ya kifa a kansa yana wani irin kuka.
Ji ta yi an girgiza ta, ta buɗe idonta, ta ga Hammad ya tsare ta da ido ya ce "Lafiya kuwa? Meyafaru?" Kasa magana ta yi, sai ajiyar zuciya da take yi kamar za ta shiɗe. Duk da jikinsa babu ƙwari haka ya din ga rarrashinta, yana tambayarta mene ne, amma taƙi magana. Da kyar ta tashi ta yi sallar asuba. Aka kawo musu abin karyawa, amma ta ƙi ko kallon abincin. Da ta tuno yadda Ƙaisar ya rungume Giyaz yana kuka, sai ta hawaye yana zubo mata.
Hammad ya fita daga ɗakin, bayan mintuna kaɗan, ya dawo ya ce ta taso. Jikinta gaba ɗaya babu ƙwari, ta tashi ta bi bayansa.
Ko su Sultan kasa gaisar da su ta yi, tana ganin Hammad ya nufi hanyar da aka bi da shi jiya, ta ja ta tsaya.
Ya ce "Meya faru ne? Mu ƙarasa mana" Ta girgiza kai ta ce "Kai dai ka je, ni ba zani ba"

"Saboda me?" Ta yi shiru ba ta ce komai ba.

"Ma viee, ki yi haƙuri babu abin da zai faru in sha Allah, magani za a yi mana mu rabu da wannan larurar, mu samu kwanciyar hankali mu zauna lafiya mu rayu kamar sauran mutane"

Ta ce "Ni ba na so" Ta yi maganar tana kuka.
Sultan ya ƙaraso ya ce "Meyafaru ne?"

"Ni ba zan je ba, a ƙyale ni ba na so"

Da gaske Nana ta kafe, ta ce ba za ta shiga ba, Matawalle ya shiga ya yi wa mutumin magana. Mutumin na fitowa ta juya zata arta da gudu. Hammad ya riƙo ta, ya ce "Amsy me yake damunki ne?"

"Wallahi ba za a kashe Ƙaisar kamar yadda aka kashe Giyaz ba. Wallahi ba zan je ba. Da ya kashe shi gara ni ya kashe ni"

"Asma'u, kin zaɓi aljani a kaina da rayuwar aurenmu kenan? Ki nutsu mana"

Hammad ya yi mata magana cikin tsawa.

Tana kuka ta ce "Wallahi ba zan tsaya ba, shi ma mai rai ne, kuma yana son rayuwarsa, ba zan tsaya a kashe ƙaisar ina gani ba"

Mutumin ya tambayi Hammad, me take faÉ—a ne.

Hammad ya yi masa bayani, cikin harshen turanci, yake gaya wa Nana, ba shi ya kashe Giyaz ba, taurin kai Giyaz yayi shi ya kashe kansa da kansa, amma ba shi ya kashe shi ba"

"Ni dai ku ƙyale ni, zamu rabu a hankali, idan na bari aka kashe shi a dalilina ban yi masa adalci ba, ko ya cutar da ni ta wani bangaren bai cutar da ni ba. Ni dai kar a kashe shi dan Allah."

Sultan ya sassauta murya ya ce "Kina ji, ba kashe shi za a yi ba, za yi miki tsakani da shi ne ya rabu da ke, amma ba kashe shi za a yi ba. Wancan ɗin ma ba shi ya kashe shi ba, shi ne ya kashe kansa dan kawai an nemi ya musulunta ko a ƙona shi"

Nana ta girgiza kai ta ce "Ƙaisar kuka yake yi, an kashe babansa, ni ku bari zan yi magana da shi, yana cikin jimami dan Allah kar ku kashe shi" Ta ƙarasa maganar har da haɗa hannayenta biyu alamar magiya.
Hammad ya rungume ta, ganin yadda take neman ta fita daga hayyacinta, ga shi yana kyautata zaton tana É—auke da juna biyu.
Nana tana da matuƙar raunin zuciya, da tausayi banda haka ya za a yi abin da ya wahalar da ita, ta din ga wannan kukan ta ce ba za a raba ta da shi ba.
104

Sosai Nana ta rikice musu, take ta uban kuka, babu irin ban haƙuri da rarrashin da Hammad bai yi mata ba, amma ta ƙi saurararsa tana cewa ita ba za a kashe Ƙaisar ba.
Malamin ya ce su rabu da ita, su koma masaukinsu su kwana biyu ta samu nutsuwa, sai su dawo da ita.
Har suka koma masauki, Hammad bai kula Nana ba, gani yake yi kawai kamar ta fifita zama da Aljani a kansa, ban da haka ita da kullum cikin taka tsantsan take da imaninta da rayuwarta, me za ta yi da zama da aljani, aljanin da babu abin da ya yi face wahalarwa da muma azabtar da rayuwarta.
Ita ma ba ta kula shin ba, ba ta bi ta kansa ba, Sultan ya ja masa kunne sosai a kan kar ya yi mata faÉ—a, ko kuma ya ce zai takura ta.
Kamar wasa Nana abu har da rashin lafiya, zazzaɓi sosai da sosai, ta ƙi cin abinci. Da ta tuna yadda ta ga Ƙaisar yana kuka, sai jikinta ya yi sanyi, shi ma halittar Allah ne, cutar da shi ba zai kawo masalaha ba, wataƙila sai ma ta'azzara wasu abubuwan.
Tun bayan tariyarsu, ba su taɓa yin faɗa ba sai a wannan lokacin.
Da daddare ma a ƙasa ya kwanta, ba ta ko saurare shi ba, ta haye gado duk da rashin cin abinci da ta yi, ya tsaye masa amma ya dake ya ƙi kula ta.
Gefe guda ta hango Ƙaisar, yana zaune ya saka wata hanya a gaba ya takure yana kallon hanyar.
Jiki a sanyaye Nana ta ƙarasa gefensa ta zauna ta ce "Ƙaisar" Ya waiwayo a hankali ya kalli Nana ya ce "Na'am"
Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ina matuƙar jin nauyinka, da kuma kunyarka, ban ma san me zan ce ba, ina mai baka haƙurin rashin mahaifinka da ka yi".
Ya ɗan jinjina kai ya ce "Haƙiƙa mahaifina ya so ni, so mai tsanani, duk mai sonsa to ya so ni. Sai dai bayan mun raba gari babu yadda ban yi ba ya gane gaskiya, amma abu ya gagara. Ban ji baƙin cikin mutuwar mahaifina kamar mutuwar da ya yi a matsayin kafiri babu ta inda zan yi masa addu'a na roƙa masa Allah gafara. Tabbas Giyaz shi ya kashe kansa bayan malamin nan ya takura masa a kan ya musulunta ko ya ƙona kansa." Ya yi maganar cikin matsananciyar damuwa.
Nana ta rasa abin yi, a hankali ta ce "Ka yi haƙuri, babu wanda ya isa ya shirya wani, idan ba Allah ba, wannan ita ce taka ƙaddarar"
Ya jinjina mata kai, sannan ya ce "Me yasa ba kya son a kashe ni? Ko a raba mu?"
Nana ta ja numfashi sannan ta ce "A tarayyata da kai, duk da akwai ƙalubale mai tarin gaske, amma na koyi darrussa daban-daban, kuma na fahimci abubuwa da dama. Tabbas yadda muke da mutanen kirki da kuma ɓata gari, kuma ku na da na kirki da ɓata gari a cikin ku. Kamar yadda nake yawan faɗa, idan ka na son ka zama mafi alkhairin mutane, ka rinjayar da alkhairi a kan sharri. Kuma bayin Allah ne, ku na taku da rayuwar Allah ya sanya mu rayu da mu da ku a Duniya ɗaya, duk da mu na da banbancin halitta, bai kamata ɗayanmu ya zamana yana cutar da ɗaya ba, ko amfani da ɗaya gurin fin ƙarfi da mugunta ba. Ni dai a yanzu zan iya bugun ƙirji na ce a cikin halittar aljanu akwai bayin Allah, sai dai su ma ajizai ne su na aikata laifuka kamar yadda ɗan Adam yake yi"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.