Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 87 of 99
*****
Duk yadda Alhaji Zailani ya so kawar da komai a ransa a kasawa yayi. Ya din ga zagaya gidan yana kallon hanyar ɗakin Shukura, da har a yanzu idan ta zo gidan, a nan take kwana. Ya kalli inda Yusuf yake zama mussaman idan zai kalli ball. Suna kallon ƙwallo tare dukkanin su akwai team ɗin da suke supporting. Ya tuna kai komon Hajiya Amina a tsakaninsu, da ƙoƙarinta na ganin kowa ya samu abin da yake buƙata. Amma yanzu babu Yusuf babu Amina, Shukura kuma babu wani abu da ta tsana a yanzu sama da shi. Gidan ya yi masa wani irin zafi Duniya ta din ga juya masa. Dama salla ba wani damuwa ya yi da ita, domin rashin kiyaye ta na daga cikin dalilan da yake kawo musu rashin jituwa tsakaninsa da Amina.
Ya din da ga jin sa tamkar a cikin wata Duniya yake, aka bar shi shikaÉ—ai.
Bugun ƙofar da ya yi yawa ne ya tashi ya je ya buɗe ƙofar main falon, ya tarar da mai delivery ya kawo masa abinci, kamar yadda Alhaji Sabo ya yi masa order, ya yi shiru yana tunanin ina mai gadi, da har mai delivery ya shigo haka. Ga harabar gidan babu kowa yan gaisuwa ma duk sun watse ya karɓa ya koma ya ajiye ya nemi guri ya kwanta.
Rufe idanunsa ke da wuya, ya ga duhu ya yi, alhalin yamma ce da sauran haske. Ya buɗe idanunsa ya yinƙura zai tashi, amma ya ji tamkar an saka igiyoyi an ɗaɗɗaure shi, ya kasa motsa ko da yatsansa. Yana jin yadda zuciyarsa take bugawa ya sare cewa kan shi ma ya mutu ne, ya din ga rarraba idanu ya ga ta ina zai fara ganin mala'iku sun bayyana. Ya hango cewar shi ma yanzu likkafani za a saka masa a je a binne shi a rami a tafi a bar shi. Ya yi wani yinƙuri domin ya tashi amma abu ya gagara. Wata irin dariya ya ji ana yi mara daɗin ji, cikin sauti mai ƙarfi.
"Abin da ka ke gudun sai ya faru, ba za ka tsere wa mutuwa ba, dole ka biya wa dodo buƙatar sa, ko kuma ya yi ajalinka. Ɗif ya daina jin muryar, sai kuma fuskar matarsa ta farko da ɗanta na fari, suka fara fitowa a ɗakin. Ya sake rikicewa sai dai bai iya kowane yinƙuri ba, Shukura ta bayyana jikinta duk jini, kamar ba ta daɗe da haihuwa ba, ta tunkaro shi gadan-gadan da wuƙa ta fara ƙoƙarin caka masa. Kamar wanda aka tasa daga bacci ya gan shi a tsakiyar titi, ƙafafuwansa ko takalmi ko babu. Ya kalli jikinsa babu suturar kirki, gari shiru ko ina duhu alamar dare ya tsala. Sai da ya yi da gaske sannna ya gano cam gaban unguarsu ya tafi. Rashin gurin zuwa ya sanya tilas ya sake koma wa gidan nasa, ya ci uwar tafiya da ƙafa ya koma.
Sai dai ƙofar gidan a buɗe, babu masu gadi, abin da bai sani ba tuni zancen ya fara zagayawa, a kan abin da ake zarginsa da shi, kasancewar mai aikin gidan na laɓe ta ji maganganun da aka yi. Suna watsewa da aka tafi da Hajiya Amina Asibiti, aka tafi da Alhaji Zailani ta tattara kayanta ta gaya wa mai gadin abin da yake faruwa ta gudu.
Alhaji Fatuhu ya ƙi sanar wa Iyalinsa abin da ya faru, sai dai gaba ɗaya ba shi da nutsuwa, ga kayansa ana ta saya babu ƙaƙƙautawa amma ba ya iya taɓuka komai, sai dai ya ɓuya ya yi kuka.
Babu tsammani Fadila ta ritsa shi yana kuka, ya kasa cin abinci.
Cikin damuwa ta ce "Daddy, ina gama ka da zatin Allah ka gaya mini abin da yake damunka, da ba haka ka ke yi ba fa. Gaba kamar ma a tsorace ka ke Duniyar, kuka fa ka ke yi dan Allah ka faÉ—a mini mene ne?"
"Wallahi Fadila a tsorace nake da Duniyar, komai tsoro yake bani, ni dama rashin lafiyar da na yi na mutu, ban tashi ba da ban ji wannan abubuwan da damuwa da baƙin cikinsu zai halakka ni ba, bayan warkewr da na yi daga jinya ba"
Ba ta san lokacin da ta fara kuka ba ta ce "Dan Allah Daddy mene ne?"
"Fadila ba zan iya gaya miki ba, ku yi haƙuri kawai, Allah ya sanya mu dace" Haka ta gaji da rarrashin ta ƙyale shi.
Shukura kuwa Sagir da Yusra ba abin da suke yi sai aikin rarrashinta, da bata haƙuri, Yusra ce take kula da Haidar da jaririn da ta haifa aka saka masa Ahmad Annur.
Sai dai ta kasa yin lafiya, kusan kullum tana kwance, Alhaji Fatuhu duk kwana biyu sai yaje gidan ya rarrashe ta, ya bata haƙuri tare da kwantar mata da hankali.
****
Da sassafe Asal ta nemi Hammad ta rasa, ta tashi ta fita falo, ta hango shi a kwnace a kan kujera yana video call da Nana.
Ta tarar da shi yana cewa "Ba fa na ganin komai ma vie, dan Allah ki cire bargon nan"
"A'a nifa bacci zan yi ka ke takura mini"
"Zan rama ne Asmy, me za ki dafa zan shigo anjima in ganki in sha Allah"
"Ba zan dafa komai ba, ai yau kana gurin matarka ta dafa ta baka"
Ya marairaice ya ce "Ni ko? Shikenan tun da kin daina so na. Ɗan yi kissing goshina" Yayi maganar yana kara screen ɗin a fuskar sa. Da sauri Asal ta koma ɗaki, wani irin abu yana taso mata kamar za ta fita hayyacinta. Ji ta yi tana neman yin danasanin biyo shi ta dawo gidansa, amma ta tuna damarmakin da ya bata bayan da ya aure ta. Amma ta din ga muzguna masa, saboda hure mata kunne da Imam Omar ya din ga yi. Bai san daɗin aure ba sai da ta fara hankali ta fuskanci ba ya tanka duk rashin mutuncin da za ta yi masa. Idan zai yi magana a dankwafe shi. Sai a gaɓar da ta dawo hayyacinta ta gane shayi ruwa ne, take sonsa a lokacin ta fara karɓar sakamakon abin da ta aikata. Yanzu ba ta da wani abin cewa sai abin da ta gani kawai. Ta sha kukanta ta gode wa Allah.
Nana an kai mata hadimai, duk da ba komai ta sakar musu ba. Har gida aka kawo mata dalleliyar motar da aka bata a gurin bikinsu, wanda Imam Zahradeen sabon Tafawan Agadez ne ya ba ta. Banda uban gwala-gwalai da ta samu. Ta fuskanci gold ne kyauta mafi tsada da muhimmanci da suke ba wa mutum mai muhimmanci mussaman ma mace.
Lefenta kuwa, sai da ta din ga addu'a, saboda yadda mutane suka camfa duk auren da aka yi ɓarna a gurin yin sa ba ya ƙarko. Sai dai Hammad ya ce mata ai abin da aka yi mata kyautatawa ce, ba wai dukiyar aure ba. Kuma Allah ne ya tsamo ta ya bata rabonta ne. Ya kuma tuna mata a yadda aka yi auren su.
Nana abin har kunya yake bata, yadda manyan mata wasu ma sun haife ta suke zuwa gidan, wai sun zo su gaishe ta, kuma in dai za su zo sai sun riƙo abin bata.
Ta fara yi wa Nene ƙorafin ita wannan abin da ake yi mata ta gaji. Nene ta ce "Waye ya gaya miki ana shiga dawa dan ƙarya? Ai girma ne ya hau kanki, dan haka dole ki yi haƙuri. Ba kuma a yi wa masu mulki kyauta su mayar su ce a'a, dole ka karɓa. Kuma dole kema ki zama mai yawan kyauta. Sannan ki ƙirƙiro wani abu da zai amfani mata a ƙasar nan, saboda tabattar da za ki iya riƙe muƙamin da aka baki"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.