Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 77 of 99
Baba ya ce "Jamila, ki gaya mini, me ki ka aikata?"
"Ƙungiyar asiri, Baba ƙungiyar asiri aka shigar da ni, saboda na kai jinin Nana"
Kamar ta watsa wa Baba wuta, haka ya fizge hannunsa ya ja da baya, yana kallon Jamila da take ta uban kuka.
Mama ta ce "A'a baban su Jamila, dan Allah kar ka yarda da abin da ta faɗa, ka san ba ta da cikakkiyar lafiya, wataƙila zafin ciwo ne, amma wace irin magana ce wannan, a ina Jamila za ta ga wata kungiyar asiri ta shiga"
Alhaji Zailani ne a durƙushe a gaban gawar ɗansa Yusuf, bayan an dawo da shi daga makaranta, dama babu rai aka dawo da shi. Ba shi ne abin da ya ɗaga masa hankali ba, sama da ganin busashshen jini a baki da kuma hancin Yusuf. Ba dan ya yi iya ƙoƙarinsa ba, da tuni ya aikata abin da zai fallasa kansa. Wani irin raɗaɗi da zafi ya din ga ji a zuciyarsa ya kasa magana, ya kasa ko ƙwaƙwƙwaran motsi.
Ba a jima ba, gidansa ya cika da jama'a, Hajiya Amina sai kuka take, ga Shukura ta ɓata, ga kuma mutuwar Yusuf.
Ya hau neman lambobin yaransa, da ya sanya su kashe Shukura, a kan kar su kuskura su kashe ta, amma ya kasa samun su. Duk da daÉ—ewar da yayi yana aikata zalunci kala-kala, mutuwar Yusuf ta dake shi, ta tsaya masa. Ya din ga jin tamkar ya yi ta kururuwa yana burgima, ko zai ji daÉ—i.
Ko da aka yi jana'izar Yusuf, Alhaji Zailani tafiya ya yi ya kulle kansa a ɗaki. Kaf yaransa babu kowa sai Shukura yanzu, Shukuran ma ba a san inda take ba. Kuma ita ma baya tsammanin za ga tsallake sharrin dodon ƙungiya, tun da ya gaza bashi jinin shekara.
Sosai ake ta shirye-shiryen gudanar da bikin auren Imam Hammad, da matarsa 'yar Nigeria. Ita Nana abin har mamaki yake bata.
Tun da Sultan ya amince da auren Nana da Sultan, Nene take sintiri kawo wa Nana kayan gyaran jiki. Ban da matar da ake ware mussaman Nene take zuwa da ita, take yi wa Nana wani irin gyaran jiki na mussaman.
Nana ta ce "Nene duk wannan abin fa ihu ne bayan hari"
Nene ta ce "Ke, gyaran ne ba kya so?"
"To Nene ya riga ya sanni a yadda nake, me kuma zan gyara?"
Nene ta ce "To kar ki gyara, komai yana buƙatar gyara ai"
Aka ajiye wa Nana kayan sakawa, da na ado irin na Buzaye. Nana ta ƙudurce a ranta, bayan ta tare, kayanta na 'yan Nigeria za ta saka Hammad ya ajiye mata, saboda ita ma tana son tata al'adar.
Shi kansa Hammad ya so a ƙyale masa ita a haka, dan shi komai nata ya yi masa. Sai dai gyaran jikin da ake yi matan ba ƙaramin kyau take yi ba.
Ga shi tare da Muhsin suke kwana da Nene, hakan ya ƙara sanya ta farin ciki.
Hammad ya ce ta fita ta É—an zagaya, amma ta sanya takunkumi ta rufe fuskarta.
Har mamaki Nana take yi, yadda idan Muhsin ya ga raƙuma ko shayi, kamar zai tashi sama saboda murna. Sarkin baka ta hango, suka nufe inda yake.
Cikin jinjina ya ce "Barka da tattaki uwar gijiyata" Nana ta yi dariya ta ce "Dan Allah ka daina kunya ka ke bani"
Shi ma yana murmushin ya É—ago ya kalli Nene, ya ce "Ni kuwa dama ina ta son na yi miki magana, Allah bai yi ba"
Nene ta ce "Ni É—in ko? Ka sanni ne?"
Ya ce "Eh, ai duk inda muka ga juna, muna gane kanmu"
Ta yi dariya ta ce "Na ji, ai ban yi zaton haryanzu akawai abin da tattare da ni ba"
Sarkin baka ya ce "Ni na ji na gane ai. Kuma ni É—alibin marigayi Sa'adu Aska ne"
Nene ta waro ido ta ce "Kana nufin Babana?"
Sarkin baka ya ce "Ƙwarai da gaske, ya sanar da ni magunguna, sai muka kwana casa'in tare da shi, a mabanbantan dazuzzuka, daga bisani muka rabu, ban sake ganinsa ba. Mahaifinki mutumin kirki ne, ba zan manta da shi ba har abada"
Nene ta ce "Ikon Allah"
Nana ta ce "Sarki kai komai ma ka sani ne? Kuma kowa ya sa ka"
Yayi murmushi ya ce "Na san dai abin da Allah ya sanar da ni, kowa ya sanni kuma na sha yawon duniya ne" Yayi maganar yana É—aukar Muhsin.
Nana ta ce "Sarki ka ga Nene ta daina harkar bayar da magani, kaima ina fatan zaka daina?"
Ya ce "Meyasa zan daina? Ba a daɗe ba ni ba, ke kanki ki ka bayar da magani zan ce, ko ba ke ki ka tono inda aka yi wa mijinki asiri, meyasa Allah ya zaɓe ki ya nuna miki, duk yawan jama'ar da ke ƙasar nan. Abin da ki ke ta gudun sai da ya faru"
Jiki a sanyaye Nana ta ce "Ba ina nufin ka daina bayar da magani ba, ka daina aiki da aljanu, shi ne ɓarnar. Sannan ka yi ilimi na zamani, cikakke domin ka inganta harkar maganin naka. Ya zamana maganunnanka da awo kar ka bayar da abin da zai cutar maimakon a samu lafiya"
Yayi dariya, Nene ma ta yi, Ya ce "Yaro yaro ne. Nana a dalilinki wallahi na daina surkullen haɗa ayoyin Alkur'ani da wasu abubuwan na yi sihiri. Saboda uban gidana ma, Allah ya ja zamaninsa uban duƙusa ko in ce Ƙaisar, shi ma ya ce na daina wannan, na kuma daina. Na daina surkulle da sihiri na tuba, amma ba zan iya daina aiki da aljanu ba"
Nana ta ce "Amma saboda me?"
"Saboda É—ebo mini magani, wasu ayyukan kuma dole su ne nake aikawa su yi wani aikin."
"Sarki, ta'amalli da aljanu da ka ke yi ba shi da wani alkhairi shirka ne, dan Allah ka daina. Kana cikin mutanen da nake son mu tsira Duniya da lahira."
"Ni ba ni na nemi aljanu na fara aiki da su ba, aljanu su suka takura ni, kamar dai ke da kuma wannan baiwar Allah.
Bana ta'amalli da aljanu, na bayar da kuÉ—i, ko na yi wa wasu sihiri, ko wani abu makamancin haka, ai kin je gurin maganin nawa kin gani"
Nana ta ce "Sarki, kar mu shiga wani bugire da bai kamata mu shiga ba, mu kalli gaskiya kai tsaye kar mu yi mata wata kwaskwarima saboda son zuciyarmu"
"Asma'u babu kwaskwarima domin ba wa ƙarya kariya a maganganuna. Su turawan da ku ke taƙama da su, su na amfani da ku, da daƙile magungunnku ne, saboda gina nasu kasuwancin. Kuma Nana magunguna na da awo nake bahar da su. Ban ƙi ba akwai masu bayar da magani, saboda neman abinci. Amma wanda ya sani ya sani, wanda bai sani ba, bai sani ba kawai. Kuma banda abin ki tun a zamanin baya magungunan 8su na da awo, wani a ce ka auna da ɓawon gyaɗa,ko farce, wani a ce ka sha safe da yamma, duk sharri ne wasu abubuwan da ake faɗa, da ƙoƙarin kashe mana magungunanmu. Sai a ce ku daina shan magungunan gargajiya saboda ɗaci, hanta ba ta son ɗaci, amma Allah ya halicci maɗaciya a tsakiyar hanta. Idan hanta ba ta son ɗaci, Allah ba zai sanya matsarmama a cikin hanta ba. Kuma su magungunan baturen, ba ɗaci ne a cikin su ba. Ba zan kushe wa kowa ba, amma kar a kuskura a kushe mini nawa. Yakamata mu daina wannan musun haka,kowa ya riƙe abin da yake ganin shi ne dai-dai "
Nana ta ɗan yi jimm tana tunani, daga bisani ta ce "Wasu maganganun naka na kan dai-dai, amma kowa ya riƙe abin da yake ganin shi ne dai-dai!"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.