Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 16 of 99

Wata irin mummunar faɗuwar gaba ta ziyarci Mama, ta ja da baya ta dafe ƙirjinta, tana wani irin haki, tare da kallon Jamila cike da tsoro.

"Jaa..jam..jamilahh me ki ka ce? Ciki fa a ina? Kuma garin yaya?" Jamila ta ci gaba da sheshsheƙar kuka ba ta yi magana ba.

Mama ta shaƙe Jamila ta ce "Ki gaya mini uban waye ya yi miki ciki kafin na take ki na kashe, da ki janyo mini abin kunya"

"Ke Rabi, kina ina ne? Waye yake yi mini kuka, kuma maganar me na ji ana yi?" Muryar Baba ta katse ta. Da hanzari ta saki wuyan Jamila, ta ja da baya tana hararta cikin ƙunar rai. Ta yi ƙwafa ta fito daga ɗakin su Jamila.

"Me yake faruwa ne?"

"Babu komai, jikinta na shiga na duba"

Baba ya ce "Kuma shi ne take ta kuka haka? Ni na gaji da larurar nan ta Jamila, wannan banke-banken hayaƙin da ki ke yi mata duk ba ne ba"

Ta ce "To in sha Allah za mu je. Ka san mun je, mun kuma zuwa amma abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, amma za mu koma"

*****
Nana ta tsaya tsuru da rigar nan a jikinta, ita kanta ta san ba dan albarkacin kaza ƙandagare kan sha ruwan kasko ba, ta san ba ta kai ta saka wannan rigar ba.
Ta jikin mudubi ta hango shigowarsa, kayansa royal blue, kalar rigar jikinta.

Ya ƙaraso gabanta, ya fesa mata turare, ya zura hannu a aljihunsa, ya ciro zobuna da abin hannu ya saka mata. Ta yi ƙuri da ido tana kallon hannun nata, rabon da ta sanya wani abu na ado, har ta manta.
A tsorace ta ce "Ni dai zan cire wannan abin tsoro nake ji"
Banza ya yi mata ya gyara zaman mayafin rigar a kanta. Ya din ga ƙare mata kallo yana mamakin yadda Asal take aibata Nana da muni, dan kawai baƙar fata ce.
Idanunta manya sexy eyes, farare ƙal da su, gwanin ban sha'awa, ga shi rigar tamkar dan jikinta aka yi ta.

Ya numfasa ya ce "Ina ƙara tuna miki, duk wani abu da za a tambaye ki, kar wanda ya baki tsoro, kar kuma ki rufa komai, muddin ki na son Muhsin ya dawo hannunki"

"Meyasa kai ba za ka yi musu bayani ba kawai?"

"Da bayanina ya wadatar, ba zan bari a zo wannan gaɓar ba". Ya ciro niƙab ya saka mata.
Sannan ya saka hannunsa ya ciro wayarta daga aljihun rigarsa.

Nana ta waro ido ta ce "Wayata, ya aka yi ta zo hannunka? Dama kai ka É—auka?"

"Eh ni na ɗauka, kin ƙi saurarata, balle na yi miki bayanin komai, mu je" Ya yi maganar yana nuna mata hanya.
Bakinta fal magana, amma ya yi mursisi, ya yi mata shiru. Ta tarar da takalma a falon gidan. Nana ta din ga ganin abin tamkar a mafarki.

Su na zaune a baya ita da shi, ana jan su a motar. Ta yi shiru tana zabga addu'a Ubangiji Allah ya bata nasarar karɓar ɗanta, dan ko kaɗan ba ta sha'awar gidan nan, ɗan zamanta a gidan kawai ta fuskanci akwai kitimurmura a gidan.

Tun da aka doshi gidan gaban Nana yake tsananta faɗuwa, haka kurum take jin ba ta ƙaunar gidan. Gefe guda kuma Nana tana ta tunanin halin da Ƙaisar yake ciki.

Tun da aka yi parking suka fito, hadimai suke gaida Imam Hammad yana ɗaga musu hannu. Ya riƙe hannun Nana yana ratsa cikin gidan da ita. Gaba ɗaya aka zubo musu ido, ana son sanin wacece wannan ya riƙo hannunta, saboda kowa ya san ba Asal ba ce, saboda ba ta kai Asal tsawo ba, kuma Asal ba ma'abociyar niƙab ba ce, ko kanta ma ba ta damu da rufewa ba.

Jikin Nana ya hau rawa, bayan da suka shiga É—akin zama na musamman na cikin fadar Sultan.
A can suka tarar da Sultan É—in, ga Matawalle ga Sardauna, su na jiran isowarsu.
Nana ta ja ta tsaya jikinta yana wata irin rawa, har ƙafafuwanta, gabanta ya din ga faɗuwa. Duk ta kowacwa kusurwar ɗakin, akaai na'urar sanyaya ɗaki, amma Nana ta kasa gane wane irin yanayi ma take ji.

Ya kalli Nana ya ce "Ki nutsu mana, kar ki ji tsoro, dan Allah kar ki yi wani abu da zai rusa mana rayuwa, kar haushina da ki ke ji, ya sanya ki makance, ki yanke mana hukuncin da zai cutar da rayuwarmu" Nana dai ta gaza ko ƙwaƙƙwaran motsi.

Ya ja hannun Nana, suka ƙarasa tsakiyar ɗakin suka zauna. Duk suka zubo musu ido.

Sardauna ya yi wa Nana alama da ta cire niƙabinta. Ta saka hannu ta cire tana sunkuyar da kai.

Abdou matawalle ya ce "Wannan kamar na taɓa ganinki ko?" Nana ta sunkuyar da kai.

Sardauna ya dube ta ya ce "Ya sunanki?"

"Nana Asma'u" Ta yi maganar kanta a sunkuye.

"Daga ina ki ke?"

Ta ce "Nigeria"

"Kin san wannan?" Ya yi maganar yana nuna mata Imam,Nana ta É—aga kai ta kalli Imam, ta kalli Sardauna, ta sunkuyar da kai.

Matawalle ya ce "Ki yi magana mana, kin san shi?"

AREWABOOKS

Nana ta kalle shi, ya kalle ta, ya tsare ta da idanunsa, yana jiran ya ji me za ta ce.

Abdou matawalle ya ce "Mu za ki kalla ki yi wa bayani. Ke ba ke muka gani cikin waÉ—anda suka kawo abinci ranar da aka yi taro ba?"
Ta jinjina kai alamar eh.

"To kin san shi ne dama?" Ya sake jefo mata tambayar.

Ta jinjina kai. Sardauna ya ce "Ki buÉ—e baki ki yi magana mana, ki daina amsa mana da kai".

"Eh na san shi"

"Waye shi a gurinki?"

Ta yi shiru tana nazarin amsar da za ta bayar, kar ta zama ta kwafsa su hana ta É—an ta. Cike da karaya ya sake kallon Nana ya ce "Ma viee, talk ki yi magana mana"

"Ni sai na ga Muhsin zan yi magana, dan Allah ka fara nuna mini É—a na"

Ya ce "To shikenan"

Ya ce "Ina neman alfarma, zan saka a kawo mata Muhsin, za ta yi magana"

Matawalle ya ce "Wane irin abu ne wannan? Ta san a gaban su wa take kuwa?"

Sardaunan Agadez ya ce "Bari Matawalle, a saka a kawo shi, mu ji me za ta ce"

Sardauna ya ciro wayarsa yana ɗan taɓawa, yana satar kallon Nana.

Sultan kuwa rasa abin yi ya yi, ya tuna fuskarta a gurin taron cin abinci da aka yi, ya so ya bibiyi me ya kawo baƙuwa wannan gurin, amma abubuwa suka sha kansa.
Wani irin gumi ne yake tsatstsafo masa bayan tuna irin taɓargazar da Hammad ya aikata, ka iya janyowa. Babban abin da ya ƙara sanya masa fargaba, shi ne abin da yake iya gani daga idanun Hammad a kan yarinyar. Ko a yanzu ya tattara hankalinsa a kanta, ta sunkuyar da kai sai zubar da hawaye take, da alama ma tamkar ya manta da zamansu a gurin.

Wata hadima ce ta shigo, hannunta ɗauke da Muhsin. Yana ganin Nana, ya yi wani irin zillo daga jikin hadimar, yana wata irin ƙara yana cewa "Naaa" kamar yadda yake kiranta, Nene  kuma ya ce mata umma"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.