Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 65 of 99

Imrana ya ce "Za ki gane ne"

"Imrana ina Baba da su Jamila, na san ba zuwa gurin su Mama ka ke yi ba, da gurin su Ummi, ban san da wani idon zan tunkari gida ba, na tafka babban kuskure da bana tunanin za su iya yafe mini"

"To kar Allah ya sa su yafe É—in mana, ke dai ba kin riga kin yi gaba ba, su zauna da rashin yafiyar"

Nana ta buÉ—e baki ta ce "Lallai hali zanen dutse, Imrana kar Allah ya sa su yafe, su Baban?"

"Eh ɗin, ai ke yakamata a ce ma sun nemi yafiyarki, idan sun yafe shikenan, idan ma ba su yafe ba za ki ci gaba da rayuwa wataƙila ma babu wanda ya neme ki a cikin su"

Hammad ya dubi Imam Zahradeen bakinsa fal tarin tambayoyi, amma yanayin fuskar Zahradeen É—in babu alamar zai amsa masa tambayoyin nasa"

Imam Zahradeen ya ce "Ya na ga ka ƙure ni da ido ne?"

Hammad ya ce "Abubuwan da na gani suka É—aure mini kai nake son ka yi mini bayani"

Ya numfasa ya ce "Bayani ya zama dole Hammad, amma ina fatan zaka yi mini afuwa da duk abin da za ka ji a bayanin nawa"
Imam Hammad ya ce "In sha Allah"
Kamar yadda suka taru a falo É—azu, haka suka sake taruwa bayan sallar la'asar.
Imam Zahradeen ya ce "Ina yi wa kowa barka da zuwa wannan gida nawa. Wasu sun san da zuwan wasu, wasu ba su zan da zuwan wasu ba. Cikinmu akwai yan gidanmu na sarauta, akwai wanda ba su da alaƙa da gidan namu, amma a yanzu tilas mun zama abu guda, kuma zan warware wani abu da na san wasu za su gan shi wani iri, amma yi haƙuri da yadda komai zai zo, duk wanda yake gurin nan abin ya shafe shi ne.
Imam Hammad, wannan bawan Allah da ku ke gani Sulei yarona ne, zamanku a tare da shi, da duk wani abu da ku ke ciki, wani abu ne na shiri da na yi shi" Gaba ɗaya suka ɗaga kai suna kallon Sule tare da Imam Zahradeen. Bai damu da kallon da suke yi masa ba, ya ci gaba da cewa; wannan matashin saurayin da yake ɗan uwa ga matarka Hammad wato Imran, bayan da ya je ya same ku, ya yi yinƙurin tafiya da ƙanwarsa, hankalinka ya tashi sosai, ka kira Mahmoudu ka gaya masa, shi kuma sun yi maganar da Sulei, shi kuma Sulei ya gaya mini. Gudun kar ya kawo tangarɗa a rayuwar aurenku, ya sanya na saka aka bi diddigi aka nemo shi.
Aka kawo mini shi har Agadez, na yi masa bayanin komai, da ko kai waye, da alfarmar da nake nema ya yi mini na yin shiru da bakinsa ya yi haƙuri ya bari ku rayu da ƙanwarsa, kai mutum ne mai asali da daraja, ƙaddara ce ta faɗa maka.
Sai dai ya fututtuke yana ganin kamar rainin hankali ne kawai, idan kana da asali da daraja dan me zan barka a wulaƙance kana gadi. Da kyar ya fahimci abin da nake son ya fahimta, sai dai duk da haka gudun ya ƙara burkicewa saboda na ga rigimamme ne, na aika shi waje karatu. Sunansa yana cikin jerin waɗanda ka ke bawa tallafin karatu a Agadez, a cikinsu na saka shi aka kuma fitar da kuɗin dan kai ka biya masa ba ni ba.
Fuskar Hammad ta yi wani irin ja, cikin kakkausar murya ya ce "Zahradeen"

"Hammad" Ya miƙe tsaye ya ce "Labarin nan bai cika ba me ka ke ɓoyewa?"

Imam Zahradeen ya yi murmushi ya ce "Wannan rigimar cikin gida ce, ka bar maganar a haka"

"Ba zan bari ba, sai ka yi mini cikakken bayani"

Mahmoudu shi kansa É—aurewa ya yi, kenan duk wannan abin Sulei, kallon biri yake yi masa yake yi musu na ayaba, ya san komai, ya san waye Imam Hammad, amma ya zauna da su har da yi masa masifar kullum yana É—awainiya da mutumin da bai san asalinsa ba?"
Gaba É—aya jikin Hammad ya hau tsuma, yana neman ya fita hayyacinsa.
Hammad ya riƙe rigar Imam Zahradeen yana tsare shi da idanu cikin tuhuma.
Zahradeen ya yi murmushi ya kalli Mahmoudu ya ce "Ni ne nake tura maka saƙon cewar kar ka dawo da Hammad Agadez, lallai ka tafi Nigeria. Kuma ni na shirya yadda aka haɗa ku da Sule har ku ka yi aikin gadi tare. Sule ni yake yi wa aiki, duk wani abu da yake faruwa, da motsinku Sule yana sanar da ni. Kuma nine nake tura maka kuɗaɗe domin kula da Hammad da iyalin da ya aura, kuma aka sanar da ni kwanciyar hankalin da yake ciki.
Sai dai bayan kame ku gaba ɗaya na kasa sanin halin da yake ciki, na tura Nigeria a bincika mini, aka tabattar mini da kama ku. Na ci gaba da bibiyar inda Nana take, amma binciken nawa bai cim mata ba, tayi ɓatan dabo, ga kuma alƙawarin da na yi wa ɗan uwanta, na zan tabattar da tana cikin ƙoshin lafiya. Sai dai da Allah ya dubi zuciyata sannu a hankali, komai ya din ga warwarewa, tun kafin ka gane ta, ni na gane ta saboda har hotonta ina da shi. Kuma aka yi sara a kan gaɓa ka zo ka same ni, da maganar cewa ka yi aure a Nigeria.
Sai na bika muka tafi a haka, ban nuna maka komai ba, zuwa lokacin da nake ganin ya dace ka san komai!.
96
1k ne via 0069685771
Aisha Adam stanbic
08081012143

Hammad bai iya cewa uffan ba, kawai ya tashi ya nufi hanyar fita. Imam Zahradeen kuma bai motsa daga inda yake ba, ya zuba masa ido. Nana ta tashi a rikice ta ce "Sayyid ina zaka je ne? Kar ka yi fushi, ka tsaya ka saurare shi, kar ka yi wa al'amarin wata mummunar fassara.
Bai tsaya ba kawai ya yi gaba, Mahmoudu ma tashi ya yi ya bi bayansa da sauri.
Wannan shi ake kira da ga ƙoshi ga kuma kwanan yunwa.
Ga farincikin ganin Imrana, amma alamu sun nuna Hammad ya É—auki zafi da abin da Yayansa ya aikata, duk da ta wani fannin taimakonsa ya yi, amma ta wani fannin abin a saka masa ayar tambaya ne.

*****
Sagir kuwa kamar zai haukace, saboda tashin hankali bai fita daga tashin hankalin ɓatan Shukura ba, ga Yusra ma ya neme ta ya rasa, tun safe ana maganar sha biyu saura na dare.
Ga shi layin wayarsa yana cikin wayar Yusra, haka a dole yaje police station ya kai rahoton ɓacewar Yusra. Ya fara tunanin kar a fara zarginsa da ko shi ne yake aikata wani abu, matan nasa suke ɓacewa.
Ƙarfe shida na safiya, suka ji ana bugun gate, bugu na tashin hankali kamar za a ɓall gate ɗin. Afujajan mai gadi ya buɗe gate ɗin, babu tsammani yaga Yusra a tsaye kamar korarriya. Ya zaro ido yana kallon ta cikin matsanancin mamaki. Gaba ɗaya gari ma bai gama waye ba, ya kalli hannunta ya ga jariri, bai yi magana ba ta banke shi ta wuce cikin gidan.
A falo ta tarar da Antynta tare da mai gidanta, saboda bugun ƙofar da suka ji ana yi.
Cikin mamaki Antyn ta ce "Yusra lafiya ki ka zo gidan nan da sassafen nan haka? Daga Kanon ki ka taho Abuja" Yusra ta yi shiru ba ta yi magana ba, kallon falon Yusra ta hau yi, tana tunanin yaya aka yi ma ta zo nan. Ita dai ta san ta ɗaukko jaririn ta fito titi, tama tafiya a hankali tana waige-waige, daga nan bata sake sanin abin da ya faru ba, ta ganta a ƙofar gidan Antynta da ta koma hannunta a Abuja.
Mai gidan ya ƙarasa gaban Yusra, ya karɓi jaririn da ya fara kuka a hannunta. Yusra ta nemi guri ta zauna tana mayar da numfashi.
"Yusra dan waye wannan, a ina ki ka samo shi?"
Mai gidanta ya ce "Rabu da ita ta huta, wannan yaron a samo madara a bashi, sannan a kira mijinta mu ji ko da saninsa ta taho, kuma me yake faruwa"
Antyn ta jinjina kai cikin damuwa, da fargabar a ina Yusra ta samo É—a.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.