Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 97 of 99
Asal duk sai ta tsargu, ta kalli fuskarsa ta ga hirarsa kawai yake yi, hankali kwance, ba domin da alamar wata manufa a fuskarsa ba.
10YRS LATER
Muhsin na da shekaru goma sha huÉ—u a Duniya, Nana ta kammala karatunta, na ilimin magungunan addinin musulunci. Hammad ya taimaka mata, ta gina katafariyar cibiyar koyar da addinin musulunci, wata a Agadez wata a Nigeria.
A lokacin Nana yaranta huÉ—u duk maza, tana sanye da glass a fuskarta tana rubuce-rubuce, Hammad ya kira ta ya ce mata Asal ce ta kira shi ba ta da lafiya, ko za ta tura mata ko Yarima ne, idan da wani magani da za a bata kuma a bata.
Nana ta ce "Ahh me Yarima zai iya yi, bari na je da kaina".
Ko da ta je gidan kuwa, tuni Muhsin yana can, Nana ta ce "Amma maimakon ku kira ni ku gaya mini, me Muhsin zai iya yi miki?"
Asal dai ta yi shiru, Muhsin yana kusa da ita ya ce "Kawai zuwa na yi nima, na tarar da ita bata da lafiya"
Nana ta ce "Ina ganin kawai mu tafi Asibiti" Nana ta taimaka mata ta canza kaya, suka tafi Asibiti.
Likitoci suka ce tiyata za a yi mata a cire abin da yake cikinta. Nana ta kira Hammad ta ce masa lallai ya dawo, tiyata za a yi wa Asal ana buƙatar a saka hannu.
Ya ce "Ki saka, ba zan iya dawowa a yau ba, sai zuwa gobe in Allah ya kaimu"
Nana ta ce "To ai ba zai yiwu ni na saka ba, ko a kira mahaifinta a waya?"
Da sauri ya ce "A'a bari na kira Sultan, kuma ki tsaya ki bayar da order, kar wani ya zo a ba shi É—ana, idan ba ke ko Sultan ba, babu yadda zan yi na dawo ne"
Haka aka yi, Sultan ya je Asibiti da kansa ba wakilici ba, ya sanya hannu aka ciro wa Asal jaririyarta. Nana aka fara ba wa yarinyar, ta yi wata irin ajiyar zuciya tare da gode wa Allah, sannan ta kai wa Sultan ita.
Ya rungume yarinyar yana kallonta cike da ƙauna, ya ce "Kin ga ikon Allah, bayan shekaru kusan ashirin da aure, sai yanzu Allah ya yi ikonsa"
Nana ta ce "Tabbas Allah abin godiya, Abin da na yi ta gaya wa Sayyid kenan, ba a cire rai da rahamar Allah.
Asal na kwance a post up room, ta buÉ—e idanunta a hankali, ta kalli Nana da take ta shafa kan jaririyar. Tsawon wannan shekarun, babu wata jituwar arziki a tsakaninsu, sai dai tun kiran da Sultan ya yi musu, ya yi musu nasiha Nana ta daina hana yaranta zuwa inda Asal take.
Aka sanar da haihuwar Asal, amma aka hana kowa zuwa Asibitin da take.
'ya'yan Nana haka suka kewaye Asal da jaririyar nan, wannan ya É—auka wannan ya É—auka.
Da kyar suka tafi gida, saboda makaranta. Ƙarfe sha biyu da rabi Hammad ya iso Asibitin. Ya tarar da Nana tana shirya jaririyar a cikin kaya.
Bakinsa ya kasa rufuwa, ya miƙa mata hannu ta bashi, Nana ta ce "Ba tukuici babu komai"
"Zan baki idan muka haɗu" Tana murmushi ta miƙa masa jaririyar, ta tashi ta basu guri. Ya ƙarasa kusa da Asal yana murmushi ys rungumota ya sumbaci goshinta. Ya ce "Kin ga ikon Allah ko Cherié?"
Ta yi murmushi ta ce "Na gani, kalli kamar ta É—aya da Yarima, duk kamar ka suke yi"
Ya yi dariya ya ce "Ba dole su yi kama da ni ba, ni É—in na wasa ne. Alhamdillah bayan samari da Allah ya bamu ga 'yar budurwa."
Asal ta ce "A saka mata Asma'u" da sauri ya waiwayo ya kalle ta, ya ce "Ba na son wasa"
"Da gaske nake, na ga kana sonta da yawa, ko ita ma za ta ci albarkacin son da ka ke yi wa rayuwarta, ka so ta sosai"
Hammad ya ce "Kin ga ni ba na son rigima daga haihuwar ki, ke cewa na yi ba na sonki ne?"
Ta girgiza kai ta ce "Ai ba ƙarya na yi ba, da na ce ka na sonta sosai, kuma ta cancanci ka so ta, na gane hakan bayan da na saurari yadda aka yi ka aure ta, da irin rayuwar da ku ka yi da kunnen basira. Duk a ajiye wannan a gefe, tsawon wannan lokacin na rayu da ci gaba da sanya ran samun haihuwa da kalamanta da suka bani ƙwarin gwiwa. Lokacin da na dawo gidanka, babu daɗewa, cikin dare na tashi fitsari saƙo ya shigo wayarka ƙarfe uku na dare. Na ɗau wayar na duba sai na ga saƙonta ne, ta ce ; Albishirinka yanzu na tashi daga barci, na yi mafarkin Asal ta haihu, ana ta shagali har na tashi ina jin abin a jikina da zuciyata, ko a kusa ko a nesa mafarkin nan zai zama gaske in sha Allah, ka samu maƙubaci ka bayar da nannauyar sadaka, Allah ya tabattar mana. Kuma idan mace ce sunana za ka saka"
Duk da a lokacin da naga saƙon nan, na cire rai da samun haihuwa, amma a duk lokacin da na tuna saƙon nan, sai na ji ina ƙara sanya rai. Tsawon shekara goman nan, wannan saƙon nata yana cikin kaina, ina jin sa ina fatan Allah ya tabattar da shi. Babu wanda na taɓa gayawa sai yanzu da nake gaya maka. Bayan haka sanin sirrina, da abubuwan da na aikata bai taɓa sanyawa ko sau ɗaya ta kalle ni ta yi mini gori, da abubuwan da na aikata ba, banda barazanar da ta yi mini, lokacin da na gano matarka ce ita. Kuma bata taɓa yi mini wani abu, na gadara ko makamancin haka ba, saboda ta haihu da kai ni ban haihu ba. Ko na yi yunkurin sanya wa zuciyata irin wannan tunanin Hasna da Fadila su na ankarar da ni, mussaman da Fadila ta gaya mini Nana tana addu'ar ka da Allah ya sanya mata jin wani abu a ranta, dan ta haihu ni ban haihu ba, balle ta yi wani abu da zai sosa mini rai.
A ƙarshe, na san maganin da ka kawo mini, ita ta sarrafa shi a kaina ta yi gwajin maganin haihuwa, kuma Allah ya amsa.
Babu riba yin adawa da mutane irinta, rayuwarta take yi kai tsaye, ba tare da ƙyashi ko baƙin ciki ba. Kuma kasancewata tare da su Hasna, suna ƙara saita ni, saɓanin da da nake tare da miyagun ƙawaye.
Na san ba zan taɓa kai wa ko rabinta a zuciyarka ba, kuma ba zan yi maka dole ba, iya wannan jihadin na zama da ni ka yi, ya isa a kira ka gwarzo, kuma hakan ne hukuncin da ya dace da ni, kana iya ƙoƙarinka a kaina, amma ni dai ka saka mini sunanta, ba kuma na yi hakan dan na burge ku ba ne, ko a ce tsirfa ba ce, a'a na yi hakan ne saboda jin wani sashin na damuwata da ta yi kamar tata."
Gaba É—aya jikin Hammad ya yi sanyi sosai da sosai.
Ya rungumo Asal a jiknsa, yana sumbatar goshinta ya ce "Abubuwan da suka faru sun riga sun wuce, ki daina dawo da su. Kuma tun farko abubuwan ku ne na kishi da yake damunku, amma tabbas Nana tana da halaye da É—abi'u na kirki, ina fatan Ubangiji Allah ya haÉ—a mini kanku gaba É—aya ya shirya mini yarana".
Nana ta ƙwanƙwasa ƙofar ta yi sallama, suka amsa, ta shigo da kwanukan Abinci.
Hammad ya ce "Wai gida ki ka je?"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.