Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 13 of 99

Abin ya É—aurewa Sardauna kai, gaba É—aya bai san lamarin nan ba sai a yanzu, jin abin yake tamkar almara.

Mahmoudu ya ce "Bayan na tafi da Shugabana Imam Hammad Nigeria, nema masa magani, bayan da na fuskanci ya manta duk wani abu da ya shafe shi. A can muka haɗu da yarinyar a gidan da muka zauna, mahaifinta ya ba shi aurenta. Shi da kansa ya ce a biya sadakin aurensa da ita. Tun da shugabana ne ba ni da 'yancin yi masa musu. Na yi ƙoƙarin tunatar da shi, amma ko na tuna masa, ba zai iya tuna komai da ya shafe shi ba"

Matawalle ya ce "Wai wannan wace irin shiririta ce ku ke karanta mana? Wane irin abu ne haka? Ta yaya mutumin da ya manta komai ya san ya ce a biya masa sadaki ya yi aure?"

Mahmoudu ya ce "Imam waye shi, da duk abin da ya shafi Agadez ya manta, amma duk wani abu na rayuwa na yau da kullum ya sani. Kuma ga shi a tambaye shi, tun da yanzu yana iya tuna abubuwan da suka faru a Nigeria"

Sardauna ya ce "Shi tunanin nasa network ne kenan, ko zamani da idan wannan ya zo wannan zai wuce?"

Kafin Mahmoudu ya bayar da amsa, Matawalle ya ce "Wato Mahmoudu ba ka ji kashedin da na yi maka ba a kan sanar da shi wani abu ba"

Mahmoudu ya ce "Ba laifina ba ne ranka ya daɗe, shugabana ne duk abin da ya umarce ni, dole na yi ba ni da zaɓi"

Hammad ya miƙe ya ce "Ina zuwa"
Ko da Hammad ya fita, Mahmoudu suka ci gaba da yi wa tambayoyi, yana ta ƙoƙarin basu amsa da rufa wasu abubuwan.

Tsit suka yi da suka ga Hammad ya dawo, Nene na bin sa a baya da É—a a hannunta.

Matawalle ya ce "Imam me ya kawo wannan matar gidan nan kuma?" Nene ta yi turus tana haÉ—e rai ta sunkuyar da kai.
Kafin su ƙara magana, Muhsin ya jefo mayafin kansa ƙasa, tare da waiwayowa yana kallon mutanen gurin.
A sukwane Sultan ya miƙe tsaye. Imam Hammad ya karɓi Muhsin daga hannun Nene, ya nufo Sultan da shi. Jikin Sultan ya hau tsuma, yana kallon yaron da ya jiye tamkar Hammad ɗin sa yana ƙarami.
Shi kuwa Muhsin kallon babansa ya din ga yi yana kallon Sultan, ganinsu iri ɗaya. Ya miƙa hannu ya ɗauki Muhsin yana faɗin "La haula wala ƙuwwata illa billah"

Su kan su Sardauna da Matawalle, ƙura wa yaron ido suka yi, duk sharrin mai sharri ƙarya ne ya ce wannan ɗan ba na Hammad ba ne ba.

Matawalle ya ce "Ikon Allah, da gaske dai Hammad yana da É—a"

Sultan ji yake yi tamkar ya haɗiye Muhsin, da a yake son ya sauke shi ya koma gurin Nene. Ya juya yana miƙawa Hammad hannu ya ɗauke shi.

Sardauna ya miƙe ya ce "Yanzu ina uwar yaron take"
"Tana nan" Imam ya faɗa yana sunkuyar da kansa ƙasa.

Sardauna ya ce "Akwai rikita-rikita a lamarin nan. Dole a san yadda za a yi. Mu na buƙatar ka zo mana da uwar yaron nan, gobe in Allah ya kaimu.
Ku kuma zamu tsare ku har sai komai ya daidaita mun gano komai."

Nene ta ce "Ranka ya daɗe me zai sanya a tsare ni? Mahmoudu ne naku dama, ku ci gaba da tsare shi da duk abin da za ku yi masa, amma ni ina roƙon alfarma a ƙyale ni na tafi"

Matawalle ya ce "Jayayya za ki yi da abin da muka ce kenan?"

Nene ta sunkuyar da kai ta yi shiru. Hammad ya ce "Zan cika miki alƙawarin da na ɗauka, babu abin da zai faru in sha Allah, ki yi haƙuri gobe in Allah ya kaimu zan zo da ita" Nene ta yi shiru cikin sanyin jiki.

Duk yadda Sultan ya so ƙanƙame Muhsin ya ƙi yadda, ya zamo ya sauka daga jikinsa, ya koma jikin Nene ya kwanta, ya saka hannunsa a baki.
Gaba É—aya Sultan ya kasa zaune ya kasa tsaye, saboda ganin Muhsin, bayan shafe lokaci yana fatan É—an nasa ya samu haihuwa.

Sardauna ya ce "To ita matar Mamman me ya kawo ta cikin wannan lamarin ne? Na ga kamar yaron ma ya santa?x

Hammad ya ce "Eh, a gurinta yake ne" Haka aka killace Nene da Mahmoudu, aka hana su zuwa ko ina.

*****

Ko da ya shiga sashensa babu kowa, Asal ba ta nan, ya yi mamakin inda ta tafi. Ya tafi kitchen ɗin da Nana take girki, ya shiga ya buɗe fridge ya samu sassanyar madarar raƙuma, ya tsiyaya ya fita.
A ƙalla ya kai awanni biyu a zaune, sai ga Asal ta dawo, babu tsammani ta gan shi a falo a zaune.
Ɗan turus ta yi tana kallon sa. Ya ce "Ƙaraso mana" Jiki a sanyaye ta ƙarasa ta zauna a kusa da shi.

"Ina ki ka je haka?"

"Nemanka na je yi" ta furta jiki babu ƙwari.

"To zan gudu ne? Ai gani na dawo"

"Wancan karon ma ai ka tafi ka bar ni"

Ya yi murmushi ya ce "Wannan na larura ne ai Cherié" Ya yi maganar yana miƙewa, har ya nufi bedroom ta ce "Hammad" tsayawa ya yi cak, jin ta kira shi da gundarin sunansa na yanka.
"Da gaske ka haihu da wata a waje ban sani ba?"

"Waye ya gaya miki?"

Asal ta kalle shi ta ce "Kar ka amsa tambayata da tambaya, ka bani amsa ko na samu nutsuwar zuciya, babu abin da yake yi mini daÉ—i. An ce ka kira ni da juya, kuma ka ce ka na da É—a, da gaske haka ne?" Ta yi maganar hawaye na cika mata ido.

Sai ya fasa shiga ɗakin, ya nufi inda take zaune, ya tsura mata ido sannan ya ce "Ni da ke na taɓa gaya miki haka? Ta girgiza kai jiki a sanyaye.

"Wanda ya gaya miki ya so cin mutuncinki ne, amma da bakina na taɓa faɗa?" Ta girgiza kai jikinta a sanyaye.

"To ki toshe kunneki daga jin abin da za a zo a gaya miki wai wai, ki jira abin da zai fito daga bakina zuwa kunnuwanki"

Ta yi ajiyar zuciya ta ce "To, amma ba ka gaya mini inda ka je ba"

"Wani aiki nake yi wa Sultan, ki kwantar da hankalinki" Ya miƙe ya tafi ya bar ta a gurin.
Da magariba ta ga yana ta shiri, ta ce "Amour ina zaka je ne?"
Ya ce "Eh yanzu zan yi miki bayani, zan je wani aiki da Sultan da ya saka ni ne, sai gobe in Allah ya kaimu zan dawo"

"Aiki kuma sai da daddare?"

Ya kalle ta ya ce "Asal, wai ki na zargina ne, yau na fara fita yin aiki da daddare, me yasa za ki tsare ni da tambayoyi kamar ba ki yarda da ni ba, shirya mu tafi tare" Yayi maganar yana haÉ—e rai.
Ta risunar da kai cikin girmamawa ta ce "Tuba nake yi, zuciyata ce ta cika fargaba, amma ka yi haƙuri"
Ya miƙe ya nufi hanyar fita, haka nan zuciyarta ta tsananta bugawa.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.