Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 81 of 99

Mama ta ce "Ban fa gane ba, yaushe aka ganta"

Uwani ta ce "Ke Ummi, ba ku gaya mata ba ne?"

Ummi ta ce "Ina ga Baba bai gaya mata ba, Nana tana Agadez can hannun dangin mijinta, gobe in Allah ya kaimu za su zo kawo kayan aurenta"

"Shi ne kuma dan munafunci ba a gaya mini ba? Kuma wane irin kayan aure kuma bayan wanda aka yi"
Ummi ta ce "Wallahi nima ban sani ba, sai dai sun zo za mu ji"
Mamaki ya cika Mama, domin babu wanda ya tsaya ya yi mata cikakken bayani, kamar ma ba a son ta ji abin da yake faruwa.
Washegari tun ƙarfe sha ɗaya na safe, gidan abincin da aka sai Abinci a hannunsu, suka kawo abinci mai rai da lafiya cikin kuloli na alfarma. Baba ya din ga shiga yana fita, shi fatansa kawai ya ga Nana ba wai abin da za a kawo na auren ba.
Da azahar motoci biyu suka iso, É—aya guda É—aya ta alfarma É—aya kuma ta matafiya.
Ƙaton carfet dama aka shimfiɗa a tsakar gidan, aka shirya wannan uban kayan Abincin.
Manyan mutane ne, farare sol Turaki da Matawallen Agadez, sai kum Tafida, sai kuma Imam Zahradeen, Mahmoudu Sulei, sai kuma Imrana.
Kai tsaye Imarana ya nufi Baba, aikuwa Baban ya rungume shi yana fashewa da kuka. Yadda ya ga Imarana a nutse cikin kamala kawai ya sanya shi mantawa da tarin baƙin cikin da yake ciki, kuma sai a lokacin ya gazgata mutanen nan da gaske suke.
Imrana ya ce "Baba kar ka yi magana, ka ga mu na tare da baƙi" Baba dai kai kawai ya iya jinjinawa yana sake riƙe shi, kamar zai sake guduwa.
Ta taga Mama take ɗan leƙowa, ta saki baki tana kallon ikon Allah, suturar jikin buzayen kawai ya fallasa cewar a cikin rufin asiri suke, ba ƙananan mutane ba ne.
Bayan Baba ya ɗan nutsu, duk sun nemi guri sun zauna, suka gaggaisa. Imam Zahradeen ya ce "To Baba mun sake dawowa, mun zo mu cika alƙawari da muka ɗauka, waɗanan 'yan uwan mahaifinmu ne, ga shi muka zo tare da su"

Suka sake gaisawa Matawalle ya ce "Ɗan uwa, Sultan ne ya aiko mu wakilci mussaman, mu zo mu yi godiya, mu jinjina wa namijin ƙoƙarin da ka yi, na aura wa ɗanmu 'yarka ba tare da sanin waye shi ba. Haƙiƙa mu yarinyarka alkhairi ga ahalinmu da ƙasar Agadez baki ɗaya ma. A madadin Sultan Jalaludeen ya ce "Mu ce maka mun gode, mun sake gode wa. Mu na tafe da dukiyar aurenta, kamar yadda ake yi wa kowace 'ya da ake yi wa kabilar buzaye. Sannan ya ce ita wannan 'ya yanzu ta zama tasa, yana kuma gayyatarka da duk wani wanda yake sha'awar zuwa, gagarumin shagalin bikin yaran nasa. Hammad da kuma Gimbiya Asma'u."
Baba ya numfasa yana ganin abin kamar a mafarki, ya ce "To ai tun da dai da aure a tsakaninsu, a ganina da an haƙura da bikin shagalin nan"

Turaki ya ce "To ai ɗan gidan mulki ne, abu ne aka yi shi da babu wanda ya sani, kuma ya saɓa wa al'adarmu, wands a dalilinta an soke al'adar ma gaba ɗaya, dan haka dole a yi shagalin bikin domin nuna wa Duniya ita. Saboda gudun abin da ka iya biyo baya, saboda mutum ne mai mulki mai faɗa a ji a garin Agadez. Dan haka nan da mako guda za a yi bikin, duk adadin waɗanda za su je, za a ɗauki nauyinsu tun daga ƙasa Nigeria har can, domin yin wannan shagali" Daga cikin ɗakin Uwani ta rafsa wata irin guɗa mai ɗan karen sauti tana faɗin "Alhamdillah" har sai da hankalinsu ya koma kan inda sautin guɗar ya fito. Gaddafi dai daga baya ya shigo, suka yi ido huɗu da Imrana. Imarana ya tashi ya nufe shi, rungume juna suka yi. Gaddafi ya ce "Imrana, wannan karon nisan kiwon naka har ya kai tsawon wannan lokacin?"
Imrana ya ce "Wani nisan kiwo, kame ni a kayi, a ka kai ni makarantar dole, abubuwa ne da yawa suka faru" Ai tuni suka manta da wani batun ba sa jituwa, saboda girman alaƙar jini, suka din ga murnar ganin junansu.
Daga nan aka shiga shigo da kayan auren Nana, sai da Baba ya saki baki, a ransa ya fara tunanin anya mutanen nan su na da hankali kuwa. Saboda shi yanzu al'amuran abin duniya tsoro suke ba shi.
Domin karrama abin da su Baba suke da shi, su Turaki suka ci abincin da aka kawo musu.
Aka gabatar musu da 'yan uwan Nana, Yaya Atine sai rawar kai take, tana nanata musu ita yayar Baban Nana ce uwa É—aya uba É—aya, ita ta saki Nono ya kama.
Haushi sai da ya kama Imran, Gaddafi ma ya tsuke fuska ya ce "Matar nan duk abin da aka haÉ—a da ita sai ta yi hauka"
Imrana ya ce "Har da wani ita ta saki nono ya kama, kamar nonon akuya, ko kunya ba ta ji ba, kamar ba da ita aka dinga muzguna wa Nana ba"
Ta din ga rawar ƙafa tana jan su da hira, sai da ta ba wa kowa haushi.
Da suka tashi tafiya kuwa, Haka Ummi ta shiga maƙwabta ta karɓo kayan da aka shirya, na tukuci da za su tafi da shi, dan kar ma wani ya sanya zalama. Kaji, da kayan snacks masu yawan gaske, da dabino kusan kwano biyar da tasoshin turare.
Turaki ya ce karramawar da aka yi musu ta isa, ba za su karɓi komai ba, ai Nana 'yar Sultan ce.
Gaddafi ya ce idan ba su karɓa ba, ba za su ji daɗi ba.
Baba ya ga za su tafi ya yi musu godiya sannan ya ce "To ba za a kawo mini Nanan ba, ita yaushe zan ganta?"
Imam Zahradeen ya ce "Zaka ganta Baba, sai kun zo Agadez biki, za ku ganta in sha Allah, ga Imrana mun kawo maka har gida ai"
Jiki a sanyaye ya ce "Nanan dai nake son gani, amma shikenan mun gode sosai da sosai"
Imrana ya ce "Tun da ni baya son ganina, bari na biku mu koma"
Cikin sauri Baba ya ce "A'a Imrana, kai ma na yi murna da ganinka"
Suka yi murmushi baki É—aya, su Mahmoudu ya ce "Duk wanda za su je, a kira a gaya mana adadin mutane, za a É—auki nauyin zuwansu da dawowar su, sannan kuma idan an gama ganin kayan da su za a tafi. Daga nan suka hau mota suka tafi.
Da suka koma gida, aka fara sauke kaya ana bubbuÉ—ewa, Baba komawa ya yi gefe ya fashe da kuka, domin hatta shi akwati guda aka yi masa.
Uwani ta ce "Isa meye haka kuma, ai abin farinciki ne, ka daina kukan nan dan Allah"
Maƙwabta ma ba a bar su a baya ba, suka din ga shigowa, sun ɗauka ko kayan auren Jamila aka kawo ko na Suwaiba. Mama baƙin ciki ya cika mata ciki, ganin yadda nata 'ya'yan duk suka zama abin da suka zama, babu wani na kirki, ta din ga cizon yatsan ina ma nata 'ya'yan ta saka aka aura wa buzun ba Nana ba.
Uwani ta ce "Allah ba azzalumin sarki ba ne, Nana ta sha wahala a rayuwa, ta yi ɗawainiya da yaron nan, da jikinta da ƙarfinta. Allah ya yi tana da rabon jin daɗi tun a Duniya"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.