Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 79 of 99

Yayi murmushi ya gyara zamansa ya ce "Ruhi shi ne asalin rayuwa, da gangar jiki ta dogara a kai, wanda ba a iya ganinsa, ko taɓa shi, amma wanzuwarsa ce take sanya gangar jiki motsawa. Ruhi yana da alaƙa da hankali domin shi ne, ku 'yan Adam ku ke amfani da shi, gurin sarrafa duniyarku da gangar jiki. Lafiyayyen ruhi da tunani suke samar da nutsatsiyar gangar jiki mai cike da karsashi. Rashin lafiyar ruhi, ta fi ta gangar jiki hatsari. Idan ruhi yana rashin lafiya, yana kashe gangar jiki baki ɗaya.
Sannan warkar da gangar jiki ya fi sauƙi a kan warkewar ruhi. Na san bayan nan nawa sun ɗan yi miki tsauri, amma bari na ɗan sauƙaƙa miki bayanan.
Kamar yadda na ce miki ruhinku yana rashin lafiya, tabbas yana yi ciwukan da ido baya iya gani, sai dai ciwon na sanya hankalinku ya ƙwace, ku aikata abin da ba shi kenan ba. Misali Alhaji Zailani ruhinsa na fama da ciwon Hassada, amma bai taɓa tsayawa ya fahimta ba, saboda hankalinsa ya ƙwace har ya din ga aikata miyagun ayyuka. Wasu lokutan ku kan ji duniya ta yi muku zafi, kun tsani komai babu laifin tsaye babu na zaune, yana daga cikin alamomi na ruhinku na buƙatar kulawa ba shi da lafiya. Dan wasu lokutan shi ne yake taɓuwa sai hankali ya taɓu, nan da nan sai a ce ƙwaƙwalwa babu lafiya, idan ciwon ba shi da alaƙa da irin matsalolin da muke haddasa muku a ruhi. Hassada, ƙyashi, yawan ƙarya baƙin ciki babu dalili, burin gushewar ni'ima ga wani, yawan raya faruwar munan abubuwa. Yanke tsammani daga samun rahama, ko wani abu na alkhairi a rayuwa. da wasu cututtukan ma da ku kan danganta su damu, alamomi ne na rashin lafiyar ruhi, duk da mafi yawa wasu lokutan mu ne muke haddasa rashin lafiya a ruhinku.
Idan ku ka ji alamu na ƙyashi ko hassada, ba ku fiye sakankankancewa ku roƙi Allah ya yaye muku ba, ko ku miƙe ku nemi maraba da hakan ba, ba ku fiye ɗaukarsa komai ba. Sai dai a hankali idan ya tsananta sai hankalinku ya gushe gangar jikinku ta aikata ɓarna. Kamar dai abubuwan da suka faru a masarautar su mijinki. Da abubuwan da aka yi masa. Ƙyashi, baƙin ciki hassada, son kai, da makamantansu duk larurar ruhi ce da ke kashe gangar jiki.
Sai dai a zamana da ke na ƙara fahimtar wani abu, babu abin da ya kai addu'a kusanta mutum da Ubangiji, kuma duk ruhin da yake da kusanci da Allah zaka same shi cikin nutsuwa. Babu wanda ya san inda ruhin ɗan Adam yake sai Allah, amma galibi cututtukan da suke alaƙa da ƙwaƙwalwa da abubuwan da zuciya ka iya rayawa su na da alaƙa da ruhi.
Lokuta da dama sai bawa ya yi ta addu'a, ya ga kamar bata karɓuwa, amma tasirin Addu'a da kusanci da Allah na sanya mutum a cikin nutsuwa, ta yadda zai ga wani da irin kaddararaa koma wadda ba ta kai tasa ba, amma ba shi da nutsuwa da kwanciyar hankali.
Yanzu mu tsaya a nan, ma ci gaba wani lokacin, zan je É—ebo wani magani ne"
Nana ba ta yi magana ba ta ji Muhsin yana kiran sunanta, yana kiran ruwa.
Ba ta motsa ba, ta ji Nene ta tashi ta nemo ruwan ta ba shi.
Abubuwan da suka tattauna da Ƙaisar kaf suka dawo kanta. Ya gaya mata wasu abubuwa da hannalinta bai taɓa kai wa kai ba. Tabbas ɗabi'ar zuciya ce jin ƙyashi ko hassada ko son kai wasu lokutan, hakan na nufin ruhin mutum babu lafiya kenan yana buƙatar attention?.

*****
Babu kowa a gidan, Mama ta ritsa Jamila, cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali take tambayarta "Jamila ki gaya mini gaskiya, da gaske ne abubuwan da ki ke faɗa cewar kin shiga ƙungiyar asiri, ko kema aljanun ne suka taɓa ki ki ke wannan soki burutsun?"
Jamila ta sunkuyar da kai. Ta taƙarƙare ta dunƙule hannu ta ɗirka wa Jamila dundu ta ce "Za ki gaya mini ko sai na danne ki da fulo na kashe ki?"

"Ki daina duka na, ba soki burutsu nake yi ba, da gaske nake Hajiya Sa'a ta saka ni a ƙungiyar asiri ba tare da sanina ba. Ta ƙulla alaƙa da ni ne, saboda na kawo mata jinin Nana ta ba wa ƙungiyarsu ta yi arziki, da ban kawo jinin Nana ba ta saka ni a ƙungiya. A can aka fara lalata mini rayuwa, sannan tsautsayi ya sake shiga tsakanina da ɗanta Abba, cikin jikina da ya fita nasa ne. Shi ya sadaukar da kansa saboda kar da na bayar da kowa a ƙungiya, amma haryanzu aljanun ƙungiyar bibiyata suke yi, suna nema su kashe ni nima, wannan ce gaskiyar da ki ke son ji Mama, wannan ce bayan ita babu wata kuma"
Kafin Mama ta yi magana suka ji muryar Baba yana kuka ya ce "Jamila kin cuci kanki, ba ki kyautawa kanki ba, Jamila ƙungiyar asiri, kuma aka nemi jinin Nana"
"Wallahi Baba ban bayar da jinin kowa ba, ba dan son raina na shiga ba, ban san ya aka yi na shiga ba."
"Rufe mini baki, ni ta wani fannin na gode Allah da na yi wa Nanan aure ma, ta bar muku gidan. Kuma ki tattara yaranki ku bar mini gida Rabi, ko ƙaunar ganinki bana son yi. Ku je ku da Allah" Yayi maganar yana kuka. Mama ta rasa bakin magana, tabbas ita da din ga ƙara tunkuɗa Jamila jikin Hajiya Sa'a, ba tare da tunanin abin da ka iya faruwa ba.
Daga cikin ɗaki Jamila na kuka take faɗin "Dan Allah Baba kar ka yi mini baki, ka yi haƙuri ka yafe mini dan Allah, ko iya haka na sha wahala, ina kan sha ma na san ba tsawon rai zan yi ba, ba za su bar ni haka ba nima kashe ni za su yi"
"Gara su kashe ki, sai ya fi mini kwanciyar hankali" Ya goge hawayensa ya fice.
Yana fita ya ci karo da Ummi, ta kalle shi ta ce "Baba fita zaka yi, ina ta sauri saboda na cim maka, ina ta kiran wayarka amma ba ta shiga"
Ya ce "Eh, fita zan yi Allah ya sa dai lafiya?"
"Lafiya ƙalau, mu shiga daga ciki"
Ya girgiza kai ya ce "Ba na son sake shiga cikin gidan nan"
Ummi ta ce "Amma Baba meyasa, magana ce mai muhimmanci"

Ya ce "Ki yi ta a nan kawai"

Jiki a sanyaye ta ce "Ranar da 'yan uwan mijin Nana suka zo gurinka sun je gidana" Sai Baba ya gyara tsayuwarsa, ya ce "Yaya aka yi suka san gidanki?"

Ta ce "Nima ban sani ba, amma har magana na yi da mijin Nana, ka san lokacin da suka samu matsalar nan, da ba shi da lafiya sun zauna a unguwarmu"

"Haka ne, amma nifa ban yarda da abin da suka gaya mini ba"

Baba ya nuna wa Ummi guri suka zauna, ya ce "Ummi da gaske ke kin yadda?"

Ummi ta ce "Baba ga zahiri nan kana gani, tun daga Nijar suka taho fa. Sun gaya mini ma an so gyara maka gidan nan ka ce ba ka so"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.