Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 37 of 99

Sarkin Baka ya ce "Nima Sarki ne, dan haka a bari ni na gudanar da aikina. Kai ka manta Garba ga Baka ga Aska da ku ka kai mini wannan É—an uwan naku can Nigeria" Mahmoudu ya yi sak ya ce "To ai na ga kamaninka sun canza?"

"Eh, ba kamannina ne suka canza ba, dan baka ganni cikin kayan aikina ba ne ba."

Sultan ya ce "Asal tashi ki je, duk abin da  aka tattauna za a gaya miki"

Asal ta ce "Allah ya baka nasara, dan Allah ina roƙon alfarma, a yi komai a gabana, ina son sanin halin da yake ciki nima".
Sardauna ya ce "Ke Asal! Ki nutsu ki saurara tukuna, ki tsaya mu ji kan rashin lafiyar tasa, sannan a yi miki bayani daga baya"

Asal ta tashi jiki a sanyaye, tana kallon inda Nana take da kuma Hammad ta fice.

Sarkin baka ya kalli Nana ya ce "Nana Asma'u, mene ne labari? Meyafaru bayan tafiyarki ne? Kuma yaya aka yi na ganki a birnin Agadez?"

Nana ta yi murmushi ta ce "Komai ma ya faru Sarki, amma dogon labari ne, mai tsayin gaske"

Ya murmusa, ya ƙare wa mutanen gurin kallo, sannan ya sake kallon Nana ya ce "Uwar ɗakina, me ya kawo ki Agadez ne?"

Nana ta nuna masa Sayyid. Mahmoudu ya yi murmushi ganin abin da Nana ta yi.
Ya ce "Uwar gijiyata, kina nan me yasa aka neme ni, kin karɓi aikin gurin uban duƙusa ne?".

Nana ta girgiza kai. Ya ce "To bani labari meyafaru?"

Sultan ya ce "Bawan Allah, ban fahimta ba me yake faruwa ne?"

"Allah ya baka yawan rai, duk cikin aikina ne. Idan babu damuwa ina son na san matsayin kowa a nan"

Mahmoudu ya ce "Ga Sultan kana gabansa, shi ne mahaifin Imam Hammad, sarkin Agadez, ga Matawalle da Sardauna, su ma iyaye ne a gare shi, kuma manya ne a Agadez. Sai Gimbiya Asal matarsa da ta fita. Sai kuma" Sai ya yi shiru yana bin su da kallo yana tsoron ya faÉ—i matsayin Nana ya yi laifi.

Sarkin baka ya ce "Ba ka gaya mini matsayin uwar gijiyata ba"

Sayyid ya ce "Matata ce"

Sarkin baka ya sake yin murmushi ya ce "Na san a rina, an saci zanin mahaukaciya jikina ya bani tun a lokacin da na ganku. Allah ya baka yawan rai, in dai yana tare da Nana Asma'u zai samu sassaucin matsalarsa. Tana ɗaya daga cikin dalilan da ya sanya yake zaune lafiya a Agadez, bai sake ɓallewa ya bar ƙasar nan ba"

Sarkin baka ya sake maimaita musu, Nana tana da alaƙa da maganin Hammad.

Matawalle ya ce "Me ka ke nufi? Ko dai wani haÉ—in bakin ne, ku ke son ku yi mana" Sardauna ya yi maganar yana kallon Sarkin baka.

Sarkin baka ya ce "ÆŠan tsahirta mini tukuna, a kan aikina nake"

Ya sake kallon Mahmoudu, ya ce "ÆŠan uwana ko za ka iya tuna abin da na gaya muku, lokacin da ku ka je gurina?"

Mahmoudu ya jinjina kai ya ce "Ka ce mana asiri aka yi masa, da baƙin aljani, ya manta duk abin da ya shafe shi, ya bar garinsu ba zai iya zama a garinsu ba. Kai kuma ba zaka iya ba shi magani ba, saboda ba aljani ne da za a iya sasantawa da shi ba, sai dai a je a karya asirin da aka yi masa. Na tambaye ka ko zaka iya karya asirin? Ka ce a'a shiga al'amuran aljanin nan akwai matsala, mu koma ƙasarmu a bincika inda aka yi masa sihiri a warware shi a can"

Ya ce "Madalla"

"Uwar gijiyata, ranar da aka kawo ki gidana neman magani, Meyafaru?"

Nana ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Ka ce a je a kira buzayen da suka tafi. Aka ce maka sun tafi. Ka ce da an same su, wataƙila ga maganin nasa ciwon ko nawa"

Sarkin baka ya ce "To Alhamdillah, an zo gaɓar da nake so a zo"

"Allah ya baka nasara. Wannan ita ce rabin maganin abin da yake damunsa"

Matawalle ya ce "Kai kalle mu da kyau, kar ka kuskura ka zo nan ku na gaya mana maganar banza. Idan ma haÉ—a kai ku ka yi, ku ka haÉ—a baki domin ku raina mana hankali, wallahi muka kama ka da rashin gaskiya, sai mun yi maka mummunan hukunci"
Sarkin baka ya ce "Na san dai duk azabar da zaka yi mini ba zaka saka ni a jahannama ba ko? To bayan wuta da Ubangiji zai saka ni a ciki, azaba in dai ta Duniya ce babu wadda ban sha ba, duk wadda za ta biyo baya ɗazu ce. Ban sanku ba ban taɓa ganinku ba, dan me zan yi muku ƙarya? Wani abu ne ya faru da tun a baya, na yi hasashen faruwarsa. Zan yi wani bayani amma a gaban mara lafiya da shaƙiƙansa da ya yarda da su. Idan na faɗa ban ce lallai sai kun yadda ba, amma iya gaskiyata zan gaya muku. Wannan baiwar Allah da na nuna na santa, tabbas na santa amma ni babu wanda na haɗa kai da shi domin na zo nan gurin na yi cuta ba. Saboda duk wani abun duniya da nake fatan samu, Allah ya riga ya bani shi. Ranka ya daɗe zaɓi mutum biyu zamu yi magana.

Duk suka yi zuru da ido, suna kallon Imam Hammad.

Hammad ya kalli Sultan, Sarkin baka ya yi caraf ya ce "Ɗayar, na zaɓi uwar gijiyata mutum biyu kenan. Allah ya baka yawan rai, idan babu damuwa ina so mu keɓe tare da ku"

Sultan ya ce "Babu laifi, Matawalle ko za ku bamu guri?"

Sardauna ya ce "Mai girma Sultan, ka yi a hankali kar ka bari su yi maka wasa da hankali, su faÉ—a maka abin da ba shikenan ba"

Sultan ya ce "Babu wani abu in sha Allah"

Bayan fitarsu gaba ɗaya, Sarkin baka ya ce "Allah ya baka yawan rai, ba dan ina tsoron hadisin da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya ce Allah yana fushi da ɗan kasuwa mai rantsuwa a kan kasuwancinsa ba, da na yi maka rantsuwa domin nima bayar da magani kasuwancina ne, amma ina baka tabbacin duk abin da zai fito daga bakina gaskiya zan gaya maka. Na san duk alkhairin da zaka yi mini ba zaka yanke mini talauci ba, sai Allah ya yanke mini. Kuma ba zaka talauta ni ba sai Allah ya talauta ni. Babu ƙarya ko haɗin baki ko yaudara a cikin abubuwan da zan yi maka. Wannan bayin Allah biyu babu wanda ba a kawo mini shi gurina neman magani ba. Asma'u ko ba ta bayar da magani ba, tsantsar tauhidinta da yarda da Allah da ta yi, zai iya sanyawa yadda yake tare da ita ya samu lafiya ko dan albarkacin addu'a. Ai Allah shi ya ce a roƙe shi zai amsa. Kafin na ce maka komai, bari na yi maka wasu tambayi m ya ka ji lokacin da ka neme shi ka rasa a ƙasar nan?"

Sultan ya ce "Na shiga tashin hankali, ba na iya cin abinci da cikakken bacci saboda rashin sanin inda yake."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.