Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 85 of 99

Ƙaton ɗakin taro ne, ta kowane ɓangare mutane ne, daban daban, 'ya'yan sarakuna da manyan mutane gurinsu daban, ɓangaren danginta daban, abin har ya fara bata tsoro ta ji kanta yana juyawa. Ba iya wannan ba, shi kansa Muhsin da kusan kwana biyar rabon ta da shi, an yi masa ado, kayansa iri ɗaya da na mahaifinsa.
Aka buÉ—e taro da addu'a, da karanto jadawalin abin da za a gudanar a gurin.
Aka fara da sake tabattar da rushe majalisar Imam, da zimmar duk wani É—an sarki Imam ne, amma babu majalisarsu, da kuma cewar lallai su za su gaji sarauta.
Aka sanar da sauke wasu daga manyan makusantan Sultan, ba tare da faÉ—ar cikakken dalili ba, sai cewa saboda za a yi gyare-gyare ne a masarautar Agadez.
Aka gabatar da roƙo ga gwamnatin tarayya, a kan ta bayar da tallafi su haɗu da masarautar Agadez, a gyara gidan tarihin nan, a faɗaɗa shi a ƙawata shi, ya zamana gurin buɗe idanu sosai ga baƙi. A kuma gina Hotel a ciki ko wajen gidan, saboda samar da masauki ga baƙin da za su din ga zuwa yawon buɗe ido.
Daga nan aka sake jaddada dokar, halattawa ƙabilar buzaye auren duk matar da suke so, daga kowace ƙasa.
Aka yi ta kaÉ—e-kaÉ—e ana shiga ana fita da abinci kala-kala.
Daga bisani aka yi wa Imam Hammad naÉ—i aka ba shi sarautar Sardaunan Agadez, yayin da Imam Zahradeen aka ba shi sarautar Tafawa.
Sai kuma abin da ba a taɓa tsammani ba, Sultan ya yi wa Mahmoudu Sarautar Tafeedan Agadez, tare da ba shi auren ɗaya daga cikin 'ya'yansa, wanda za a gudanar a nan take. Gigicewa Mahmoudu ya yi, Nana ma ta waro idanu saboda mamaki. Hammad kuwa ya sani, tare da Sultan suka shirya komai. Kuma ya tabattar ƙanwar tasa ta amince da auren Mahmoudu, ita ma tata mahaifiyar rasuwa ta yi, ita ce 'yar autarsu. Dama ba shi da matsala da Mahmoudu, kuma ya fuskanci su na shiri sosai, shiyasa ya nemi alfarmar Sultan ya yi wannan haɗin.
Aka fito da Muhsin, aka gabatar da shi, a matsayin ɗan Hammad, da Duniya ba ta san da shi ba, kuma a ka yi masa naɗin Imam kuma Yariman Agadez mafi ƙarancin shekaru a tarihin Agadez, haka zalika kuma Imam da mahaifiyarsa ta sauya tarihin Agadez baki ɗaya. Nan manyan mutane suka din ga bajinta, da gwangwaje Muhsin da tsadaddun kyaututtuka na ban mamaki. Har sai da Nana ta kalli abin a matsayin Almubazzaranci.
Daga bisani aka din ga koÉ—a Nana ana yi mata kirari, ita ma aka gabatar da ita, a matsayin matar sabon Sardaunan Agadez, kuma mahaifiyar Yarima.
Nana gaba É—aya sai ta rikice, kawai ta fashe da kuka.
Aka bata mic a kan ta yi magana, amma ta kasa ƙarshe kawai ta yi sujudu shukur a gurin, jikinta na tsuma tana wani irin kuka. Hammad ne ya din ga rarrashin ta, yana ankarar da ita ranar farin ciki ce a gare su. Ba a bar uwar Yarima haka ba, sai da ta samu sarautar Garkuwar matan ƙasar Agadez.
Haka matan manyan mutanen nan, suka din ga guÉ—a, suna yi mata kyaututtuka.
Hammad ya yi godiya ga tarin al'ummar da suka halarci taron, tare da fatan É—orewar Canjin da aka samu, na halatta auratayya da kuma tabattar da 'yancin kowane kalar fata.
Ya yi godiya ga dangin Nana, tare da jinjina mata, da kamba mata a gaban tarin jama'ar nan. Duk bai fito ya bayyana wa mutanen abin da Nanan ta yi yake ta wasa ta ba, amma ya nuna wa Duniya yana ƙaunar Nana, kuma komai zai yi ba zai taɓa biyanta soyayyar da sadaukarwar da ta yi masa ba.
"Haƙiƙa yau rana ce mai girima, da ɗumbin tarihi a gare ni, da ma al'ummar ƙasar nan, duk da akwai ranar da ta fi ta da ba zan manta da ita ba, ranar da na mallaki Gimbiya Asma'u a matsayin matata. Ba ni da kalaman da zan yi amfani gurin yi mata godiya, da nuna muku girma da matsayinta a rayuwata ba. Ni dai na san halitta ce mai girma, da ta cancanci na wasa ta, na yabe ta, na so ta na kambama ta ko a ina ne. Asma'u ke rayuwata ce" Ya ƙarasa maganar a raunane.
"Allah ya yi miki mafificin tukuici. Haka zalika ba zan manta da ɗan uwana ba, ba sabon Tafawan Agadez ba, dama wannan yayana ne. Ina nufin Tafeedan Agadez. Ba ni da abin da zan iya faɗa, sai dai za ku dauwwama a cikin zuciyata da kuma addu'ata. Sai mai gayya mai aiki uba na gari mai girma Sultan uban ƙasa uban kowa da kowa. Mu na godiya da tarin karamci da dattakunka a gare mu.
Iyayena na Nigeria, kafataninku muna ƙara sake miƙa godiya a gare ku"
Nana kam kasa jurewa ta yi, ta rasa ma kukan me take yi, na murna ne ko kuma na damuwa.
Ba Nana ba hatta iyayenta, sai da suka yi kukan murna, Baba bai taɓa tsammanin a zuriyarsa za a samu irin wannan tagomashin ba. Sai dai shi Allah, mai aikata abin da ya so ne a lokacin da ya so, ya kan ɗaga abu a lokacin da ya ga dama, zuwa ƙololuwar matsayin da zato bai taɓa zata ba.
Taro ya watse lafiya, aka tashi cikin farin ciki, duk da zukatan maƙiya ba haka suka so ba.
Ai kamar yadda Hammad ya ce, a ranar za ta tare, babu wani abu da ya yi saura da ake jira.
Batun sabbin naɗe-naɗen da aka yi, ya sake cika gari, wasu suna ganin Sultan ya nuna son kai, gurin cire manyan mutane masu muƙamai, ya bawa 'ya'yansa.
Nana ta so ta huta kafin ta tare, amma Maijidda ta ce a'a, tun da haka mijinta ya ce yana so.
Baba duk abin sa, sai ga shi ga babar su Nana, a gurin bikin Nana. Abin mamaki Imrana ne ya sanya su a gaba ya din ga yi musu nasiha, da nuna musu illar gabar da suka din ga ya haifar musu.
Nene ta riƙe hannun Nana ta ce "Gimbiyarmu, dan Allah a yi mana godiya, tabbas Hammad ya cika jagora, na ji daɗin abin da ya yi wa Mahmoudu, Ubangiji Allah ya saka da mafificin alkhairi"
Gaba É—aya Nana ta so ta sake sosai a cikin 'yan uwanta.
Hammad yana ta shiri a ɗakinsa, Mahmoudu ya shigo, dan bai samu sukunin haɗuwa da Hammad ba, saboda karɓar baƙi.
Hammad ya kalle shi ya ce "Ango ka sha ƙamshi"
Ya buɗe baki zai yi magana, Hammd ya girgiza masa kai ya ce "Ɗan uwa kai ka ke bi na bashi, dan haka babu buƙatar wani dogon jawabi ko godiya a tsakaninmu, mai girma Tafeeda Allah ya taya riƙo" Ya yi maganar yana fesa masa turaren hannunsa.
"Sardaunanmu, godiya ta zama dole a tsakaninmu ai, godiya dole na...
Hammad ya tsuke fuska ya ce "To jeka waje ka yi godiyar"
Mahmoudu ya yi murmushi ya ce "Wallahi jin abin nake kamar a mafarki, bawa ya zama saraki ikon Allah, amma kana ganin Hanin ta amince da auren nan, tsakaninmu ba soyayya raha ce dai da girmama junanmu"
Hammad ya ce "Ka na tsoro ne? Hanin na sonka, da amincewarta aka yi komai".
"To kuma tana son baƙar fata"
Hammad ya yi tsaki ya ce "Ka na da abin haushi wallahi. Kaf ƙabilar buzaye, ban taɓa ganin baƙi mai kyanka ba, har fararen ma, idan kuma duk baƙar fata gaba ɗaya matata ta fi kowane baƙar fata kyau" A tare suka yi dariya. Hammad ya ce "Kai mutumin kirki ne, mai nagarta na san na yi wa ƙanwata kyakykywan zaɓi ne, dan haka ba ni da fargaba" Suka ci gaba da tattaunawa cikin raha.
Nana tamkar wadda za ta yi sabon aure, haka aka zaunar da ita aka din ga yi mata nasiha, Mai jidda ta nanata mata batun riƙe addu'a a duk inda take.
Sai da aka kai ta har gurin Sultan nan ma ya yi musu nasiha sosai ita da Hammad.
Daga bisani, Hammad ya É—auke ta daga can gurin Sultan suka tafi, ya ce akwai walimar cin abincin dare tare da ita da danginta kaÉ—ai, washegari kafin su wuce Nigeria.
Asal kamar za ta mutu, haka take wani irin kuka tana rirriƙe Hasna.
Tafawa ne yake ta bala'i ya ce "Wallahi ko za ki mutu sai ya sake ki, ban ga amfanin ki ci gaba da zama da mutane marasa mutunci ba, babu kunya babu tsoron Allah Jalaludeen ya sauke ni daga kujera ta, ya bawa 'ya'yansa, zai ga matakin da zan É—auka a kansu."
Asal ta girgiza kai ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, amma zan koma gidan Hammad, iya rufin asirin da ya yi mini ya isa, na yi maka biyayya iya yi na, amma ƙarshe na faɗa halaka, kuma buƙatar taka bata biya ba"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.