Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 3 of 99

Ganin gurin zai sake yamutsewa, ya sanya Imam Hammad yin gyaran murya. Cikin girmamawa ya ce "Ina godiya matuƙa da wannan dama da aka so ba ni, amma zaman lafiya da kwanciyar hankalin Agadez shi ne a gaba da komai. Ina roƙon a yi mini alfarmar yi mini afuwa, ba zan samu damar yin tafiya wakilcin nan ba, sakamakon hali na rashin lafiya da nake fama, ciwo zai iya kama ni a ko ina, dan haka Tafawa ya yi gaskiya, ina buƙatar hutu"

Cikin tsawa Sardauna ya ce "Ba kai ka ke da wannan hurumin ba."

"Mai girma Sardauna, gaskiya Tafawa ya faÉ—a, ban cancanci duk wannan abubuwan ba, shugabancin Imam ma zan sauka na nemi lafiyata"

"Mun san ba ka da lafiya, amma ka ka na kan magani, dan haka larura ba za ta hana ka aiki ba"

"Larurar ƙwaƙwalwa, mahaukaci ba zai wakilci masu hankali ba, ina neman afuwarku"

Daga wannan maganar ya yi waje, saboda yadda idanunsa suka yi jawur, jikinsa ya fara tsuma.

Tsit gurin ya yi aka hau kallon-kallo.

Sardauna ya ce "Ka ga abin da ka janyo ko?"

"Ai ba ƙarya na yi ba, shi ya faɗi cewa ƙarya nake yi ɗan sa ba mahaukaci ba ne?" Ya yi maganar yana kallon Sultan.

AREWABOOKS

Har wani duhu yake gani a idanunsa, saboda matsanancin ɓacin rai da tashin hankali. Mutumin da yake uba a gare shi, shi ne ya yi masa wannan kausasan laffuzan a gaban jama'a.
Ya daɗe yana nuna masa ƙiyayya, amma lamarin bai fito ƙarara ba sai bayan da ya zama Imam.  Mussaman wannan dswowar da ya yi, dan ya matsa a kan lallai sai ya ji wani ciwon ne ya zaunar da shi a ƙasar waje har shekara biyu, kuma aka hana kowa zuwa duba shi?
Ya kawo kai cikin falo, Nana tana ta aikace-aikacenta. Ɗan turus ta yi bayan da ta tuna Asal ta ce mata ba yanzu zai dawo ba. Fuuu ta ga ya nufi uwar ɗakinsa. Ta ɗan taɓe baki ta ci gaba da aikin gabanta. Sai dai zuciyarta na kan abin da ya sanya shi cikin fushi da tashin hankali haka.
Duk da ba ta da wani kusanci da shi a wannan Duniyar tasa, amma mutum ne mara magana, amma yana da yawan fara'a.

Asal ta fito daga wanka ta gan shi kwance a kan gado. Ta kalle shi ta ce "Amour ya na ga ka dawo kuma? Lafiya kuwa?" Muryar Asal kawai ta fusata shi, saboda abin da mahaifinta ya yi masa a fitarsa. Dan haka ya yi mata banza.
Ta nufi gaban mudubi ta amsa wayar da take ta ringing, ta ajiye ta dawo ta dube shi ta ce "Sultan yana neman ka a sashen sa yanzun nan"
Ya yi mata shiru, bai yi magana ba, ta nufe shi ta zauna a kusa da shi, ta É—ora hannunta a kan kafaÉ—arsa. Ya tashi zaune a fusace ya ture hannun Asal, ya tashi ya fita.
Sororo ta tsaya tana mamakin me yake damunsa haka?
Gaba É—aya ya fita ya bar sashen.

****
Cikin matsananciyar damuwa Mama take kallon Jamila da ta yi wata irin rama mara fasali, duk ta bushe ta yi haske sai uban kai É—auke da gashi.

"Jamila ni fa na rasa gane kan ki gaba ɗaya, kalli yadda ki ka koma, dole ki shirya mu je gurin masu magani ko mayu ne suka kama ki, ki ke ta wannan wahalar duk kin ƙi lafiya"

"Ni babu wasu mayu da suka kama ni"

"To idan ba mayu ba wannan ciwon na mene ne haka? Fitar nan ma da ki ke yi gurin kasuwancin naku kin daina gaba É—aya"

"Ki ƙyale ni zan warke ne" Ta yi maganar cikin ƙosawa da maganganun Mama.

Su na haka Yaya Atine ta yi sallama, Mama ta amsa tana yi mata maraba.

Mama ta ce "Ke ki ke tafe a yammacin nan?"

Ta ce "Wallahi kuwa, na ga kwana biyu ban leƙo ba, na ce bari na shigo, Isan ba ya nan ne?"

"Eh ya fita baya nan"

"Ita kuma wannan fa?"

Cikin damuwa Mama ta ce "Ba ta da lafiya ne, nayi-nayi da ita, mu je gurin mai magani ta ƙi yarda, ga na Asibitin an yi ya ƙi jiki kullum ƙara rikicewa yake yi"
"To me yake damunta ne har haka?"
Mama ta ce "To gata nan dai, kullum zazzaɓi ba ta kuma son cin abinci ko fita ba ta yi, na Asibitin ya ƙi yi mata, mu koma na gargajiya ta ƙi"

Yaya Atine ta É—an zura wa Jamila ido, har sai da haushi ya kama Jamila, ta tashi ta bar gurin. Yaya Atine ta ce "Mhmm" Ta É—aukko wata hirar daban.

Ba ta wani jima ba ta yi wa Mama sallama ta tafi, sai dai cikin sa'a ta haɗu da Baba a ƙarshen layin, dan haka ta zauna suka dasa hira a hanya.
Ta ce "Ashe Jamila babu lafiya?"
"Eh wallahi ana ta fama, an kasa gane abin da yake damun ta"

"Lallai, to gaskiya yakamata ku zurfafa bincike dan kuwa É—an yau ka haife shi ne, amma ba ka haifi halinsa ba"
Cikin rashin fahimta ya ce "Me ki ke nufi?"

"Ni babu abin da nake nufi, balle a ce na ce, ni dai kawai na ce a zurfafa bincike ka ga tafiyata" Ya yi shiru yana nazarin maganganun 'yar uwattasa.

****

Cikin fushi Sultan yake kallon Imam Hammad, ji yake yi tamkar ya kwaÉ—a masa mari ko ya huce.
"Sai yanzu ka ga damar amsa kiran nawa?"

Ya girgiza kai ya ce "A yi mini afuwa, jikina ne ya so motsa mini shi ya sanya ban samu fitowa ba"

Sai kuma ya sassauta murya ya ce "Wani abin ne ya faru da kai bayan tafiyar taka?" Ya girgiza wa Sultan kai.

Cikin rarrashi ya ce "Hammad, ba a cin nasara da karaya da kuma miƙa wuya farat ɗaya. Kuma Tafawa Maleeka bai yi ƙarya ba, ina son ka gaje kujerar Sultan ba dan komai ba sai domin ina buri da fatan ka gyara kura-kuran da na aikata a baya. Ni ba ina burin ka zama Sultan domin son zuciya ko wani abu ba, ko iya haka Allah ya yi maka mai kyau a duniya, ina yi maka fatan mai kyau a Lahira. Ka ma da ilimi, ka na da dukiya, ka na da mulki iko ka ke buƙata gurin aiwatar da wasu abubuwan.
Kai kaɗai ne kujerata ba ta gabanka, kuma ka fi ni jajircewa da tsayawa a kan ra'ayinka da aƙidarka, burikanka a kan Agadez da ƙudure-ƙudirenka abubuwa ne da za su sauya rayuwar mutane da dama, saɓanin sauran da hawan kujerar ne kawai a gaban su, ba ƙalubale da abubuwan da suka kamata ba. Dan Allah ka yi haƙuri ka jure kar ka watsa mini ƙasa a ido. Wannan nagartar taka ya sanya manyan nan na majalissata suka ƙara tsanarka ba wani abu ba"

Imam Hammad ya numfasa ya ce "Abie na ji duk bayananka. Amma ka yi haƙuri na riga na karaya, kalaman da ake jifa na da su sun yi tsauri da muni, su na taɓa zuciyata da yawa"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.