Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 9 of 99
*****
Asal ce take ta shiga tana fita cikin takaici, bayan jin Nana shiru ba ta kawo Abincin safe ba, ga babu alamar na rana, kuma ba ta gyara sashen ba. Ita a tunaninta tuni ta dawo daga kiran da aka yi mata a can gidan Sultan.
Takaici ya ishe ta, dan ta tsani zuwa ɗakin da Nana take a ganinta ƙasƙanci ne, amma jin shirun ya yi yawa, ta fara duba kitchen ba ta nan, ta wuce ɗakin Nana, saboda ya ci a ce ta dawo, duk da ba ta san kiran me Imam ya yi wa Nana ba.
Sai dai tana zuwa ta ga wayam, hatta kayan Nana babu sai katifarta.
Cikin tashin hankali ta fito ta tara su Balaraba da sauran ma'aikatan cikin gidan.
Duk su ka taru "Wai gidan uban wa yarinyar nan, mai yi wa Imam girki ta tafi? Tun jiya ba ta gidan nan, hatta kayanta ta tattara ta tafi ta bar gidan nan."
Cikin girmamawa Balaraba ta ce "Wallahi ranki ya daÉ—e, bamu ganta ba, kin san ta koma cikin sashenku, ba ganinta ma muke yi ba"
"A ce kaf cikinku babu wanda ya ga fitarta?" Suka yi shiru, su na sauraren jarabar Asal.
Ta ƙare musu rashin mutunci, ta sallame su.
Kai komo ta din ga yi tana tunanin ina Nana ta tattara kayanta ta gudu? Haka kurum ta din ga jin kamar akwai abin da Nana take ƙullawa ta bar gidan.
Tana komawa sashenta, ta tarar da tarin missed calls É—in Tafawa.
Cikin rawar jiki ta bi kiran wayar, aikuwa ya É—aga hasale.
"Wace irin wawuya ce ke, ina ta kiran wayarki amma kina can kina shashashanci ba ki É—aga ba?"
"Dan Allah ka yi haƙuri, ina can wani uzuri ne"
"Uzurin banza uzurin wofi? Asal kin san me yake faruwa? Yau ni mijinki ya kalla ya ce mini na bincike ki, ke ce juya shi ba juya ba ne ya na da É—a"
Wani irin dumm maganar baban nata ta daki zuciyarta, ta ji wani banbarakwai, banda ba abokin wasanta ba ne, da ta ce ƙarya ya sharara mata, kuma da sai ta hukunta shi a kan hakan"
"Na ji kin yi shiru?"
"To ai na kasa ganewa ne, wai wane Imam É—in ne yake da É—an?"
"Wanne ki ke aure? Kuma kaf cikinsu waye ba shi da É—a ban da mijinki?"
Cikin kuka ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na shiga uku na lalace. Abba ya zan yi, ni Hammad zai yi wa haka? A ina yake da É—an?"
"Ki nutsu ki kwantar da hankalinki, haryanzu ban tabattar ba tukuna, ina ga faɗa kawai ya yi dan ya huce takaicinsa, kuma saboda tsagwaron munafunci aka sallami kowa daga zaman, ba a bari na ji ƙarshen zancen ba, amma zan bincika na tabattar da gaskiyar maganar?"
Ba ta iya tantance sauran abin da yake faɗa ba, ta kashe wayar jikinta yana rawa, ta hau kiran lambar Hammad, sai dai shiru wayarsa ba ta shiga, ta kira ya kusa sau hamsin, amma shiru ba ta shiga. Ta yi jifa da wayar tana huci. "Wallahi Hammad, zancen nan ko ba gaskiya ba ne ba, sai ka fuskanci mummunan tashin hankali da abin da ba ka taɓa zato ba. Wallahi ta tabatta ka haihu da wata mace, sai an mutu har Liman." Ta zauna Jikinta yana wata irin tsuma ta tashin hankali.
Sultan kansa ya kasa zaune ya kasa tsaye, dan babu yadda ba su yi da shi ya yi magana ba, bayan tafiyar Nana ba amma ya ƙi.
Hankalin Sultan ya yi mummunan tashi, Abduou matawalle ne ya din ga rarrashin sa yana kwantar masa da hankalin a kan su bi komai a hankali, har su samu Hammad ya yi musu bayani dalla-dalla.
Sultan ya ce "Matawalle, a tsorace nake, Tafawa ya yi nasara, ya yi nasarar tabattar wa da Duniya cewar Hammad mahaukaci ne, idan ba haka ba ta yaya zai zo ya ce yana da ɗa, ɗan ma ba da buzuwa ba, 'yar wata ƙasar bayan ya san me hakan yake nufi.
Tafawa ya ce "Kar ka yi mamaki, yanzu dole mu jira ya yi magana, mu É—an ba shi lokaci ya nutsu, dan mu tabattar jikin ne, ko kuma da gaske yake. Kar ka manta tsawon lokacin da ya shafe ba tare da mu ba, bamu san me da me ya faru ba, kuma kar ka manta a Nigeria a ka gano mana shi"
Sultan ya goge gumin da yake tsatstsafo masa ya ce "Matawalle, akwai gagarumar matsala, babu buƙatar mu ba shi wani lokaci na daban, dole ya warware mana zare da abawa mu ji yadda aka haihu a ragaya. Kira mini wayarsa, duk inda yake a nemo shi, kuma a kira mini yarinyar ma"
Matawalle ya ce "Haka ne, kuma a nemo wannan munufukin yaron Mahmoudu, domin tabbas ya san komai, ya san duk abin da ya faru"
"Wai ni ita yarinyar ma, ni kamar na taɓa ganinta, a ina aka samo ta ne?"
Matawalle ya ce "Eh, lokacin da Hammad ya dawo, tana cikin waÉ—anda suka yi girki, wai Gimbiya Asal ce ta kawo ta"
"Asal kuma?" Sultan ya yi maganar yana nazari.
Sai dai duk tarin kiran wayar da aka yi wa Imam Hammad, ko sau É—aya wayar ba ta shiga ba.
Hakan ya ƙara jefa su a tashin hankali.
A hankali Nana ta yi miƙa, dan tamkar ta ci wani abu, haka ta yi wani irin nannauyan bacci. Cikinta ne yake wata irin ƙara, saboda azabar yunwar da take ji.
Ta yinƙura da ƙyar, za ta tashi zaune, ta yi tozali da kyakykywar fuskarsa, yana kallonta. Ja da baya ta yi tamkar ta yi tozali da wanda ba muharraminta ba. Ta kalli jikinta babu hijjabi, rigar jikinta ma an canza mata wata.
"Kin tashi?"
"Ina ɗa na yake? Kuma waye ya ce ka taɓa ni ka canza mini riga, waye ya baka wannan damar?"
"Sadakina" ya ba ta amsa kai tsaye. Ita tsantsar mamakin halayyarsa take yi ma a yanzu, gaba É—aya ya canza mata.
"Na haɗa ka da girman Allah, ka bani ɗa na, ka bani ɗa na, ni ban sanka ba, ɗana kuma ba ɗan ka ba ne, dan Allah ka bani yarona na tafi, dan Allah ka taimaka mini, na karɓi yarona na koma ƙasata" Ta yi maganar hawaye na bin fuskarta.
Ya wani lumshe ido yana murmushi ya ce "To ni kuma ina za ki kai ni idan ki ka tafi?"
"Ni ban sanka ba"
"Haba?" Yayi maganar yana ƙanƙance idanunsa. Wani marurun takaici ne ya ƙule Nana.
"Ki tsaya ki saurare ni, na yi miki bayani"
"Ni ba zan ji wani bayaninka ba, duk abin da zai fito daga bakinka, ba zan taɓa yarda da shi ba. Ka bani ɗa na na tafi"
Sayyid ya yi ajiyar zuciya ya ce "To ki bari ki haifa mini abin da yake cikinki, ki bani abina, sai mu san abin yi"
Daina ganewa Nana ta yi na wani É—an lokaci, ta yi shiru ta tuna ya ce mata tana É—auke da juna biyu ma É—azu. Ta kalli cikinta, ta É—ago ta kalle shi, ya É—age mata girarsa É—aya.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.