Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 8 of 99
"Tafiyar da É—an nisa, ki É—aukko kayanki, inda yaronki yake ya ce mu kai ki"
Ba ta tsaya ta zurfafa tunani ba, ta shiga cikin gidan. Hajara ta ce "Nana yaya?"
"Tafiya zan yi"
"Ki je ina? Wai ni, me ya haÉ—a ki da Buzayen nan ma? An ce mini daga gidan Sultan É—in Agadez aka zo gurinki, me yake faruwa ne?"
"Zan yi miki bayani daga baya, bari na je tukuna" Ta ja jakarta, ta yi waje. Wata irin haÉ—aÉ—É—iyar mota ce, ta haÉ—u ga kyau ga wani daddaÉ—an sanyi da take fitarwa.
Sai dai Nana ba ta tsaya tantance kyan motar ba, lissafinta kawai Muhsin ya zo hannunta, ta gudu. Dan ko me za a yi ba za ta bayar da É—an ta ba, kuma ba za ta bar Nijar ba sai Sayyid ya sake ta.
Sun sha tafiya, kafin su isa wani irin ƙaton gida, sai da ta ga an shiga gidan, ta waiwaya ta ga an rufe jibgegen gate ɗin gidan, sai kuma tsoro ya fara kama ta, dan ta san barin wannan gidan ba abu ne da zai yi sauƙi ba.
Sai dai hanakalinta baki É—aya ya fi karkata, ga ta yi tozali da É—anta, ta san a halin da yake ciki.
Ta sauka daga motar ta tsaya tana rarraba ido, mai rawanin ya yi mata jagora zuwa katafaren falon gidan.
Ya sauke rawanin fuskarsa ya ce "Akwai banɗaki, da abinci, ki yi salla ki ci abinci kafin Imam ya zo" Wata irin muguwar razana Nana ta yi, ta ce "Sule? Kai ne dama? Me yasa..? Ta rasa wace tambayar ma yakamata ta ƙarasa.
"Ki yi haƙuri, ba ni da damar ce miki komai, ki yi salla tukuna" Nana ta ƙara rikicewa kanta ya kulle. Da kyar ta samu ta yi sallolin.
Jikinta sai ciwo yake yi saboda azabar zirga-zirgar tafiya ga cikinta babu komai.
Gaba ɗaya rarraba ido kawai take yi, tana tunanin ta ina za ta ga Muhsin, ga fafur Sule ya ƙi tsayawa ya yi tafiyarsa ya bar ta sai itakaɗai, balle ya yi mata wani gamsashshen bayani.
Jin ana turo ƙofar falon, ya sanya ta miƙe tana ƙara leƙawa ko za ta ga Muhsin.
Sai dai ba ta ga Muhsin ba sai baban Muhsin, yana sanye cikin baƙar jallabiya, ya yafa hirami a kansa, bayansa kuma Mahmoudu ne, wanda ta fi sani da Habu.
Razana ta yi, ta tsaya ƙyam tamkar an dasa ta, ta haɗiye wani abu mai masaifar zafi tamkar wuta a maƙogwaronta zuwa ƙirjinta.
Ya kalli idonta, yana ƙoƙarin tantance wane irin kallo take yi masa, ya rasa ta ina ma zai fara.
"Ina É—a na?" Ta jefa masa maganar a zafafe tana huci.
Habu ya matso gaba ya ce "Nana, ki yi haƙuri ki ci abinci ki huta, ki samu nutsuwa, sai mu yi miki bayani"
"Bayani? Wane bayanin nake buƙata bayan wanda na gani? Kun cuce ni, na ƙarar da lokacina ban tsinana wa rayuwata komai ba, na tsaya na yi biyayyar aure na rabauta, ashe mutumin da nake tausayawa azzalumi ne, kuma mugu ne. Kun zalunce ni kun yaudare ni, kun ɓoye mini abubuwa da dama, ba dan ba ni hakkinku ba Allah ya saka muka haɗu ba, da shikenan haia zan ci gaba da gararamba, ba ni da makoma. Ba zan yafe muku ba. Allah ba zai bar zaluncin da ku ka yi mini ba. Ka bani ɗa na dan ba ɗanka ba ne, baka da hurumi da shi Muhsin ba shi da uba na zaɓi ya tashi da wannan tambarin da ya san ubansa azzalumi ne da ya wofantar da rayuwar mahaifiyarsa".
Wata irin suka maganganun Nana suke yi wa zuciyarsa, amma ya san koma Nanan ta faÉ—a a kansa, ba ta yi laifi ba, ya kuma cancanci hakan daga gare ta.
Mahmoudu ya ce "Nana, kin san wa ki ke gaya wa haka? Mijinki ne fa?"
Cikin kuka ta girgiza kai ta ce "Wannan ba mijina ba ne, mijina Buzu ne da bai san waye shi ba, babu kowa a duniyarsa sai matarsa da ta nuna masa ƙauna saboda Allah. Ba wannan mayaudarin da ya yaudare ni da cewa ni rayuwarsa ce ba, na yi asarar lokacina a kan nemansa ba. Ka bani ɗa na ka haɗa mini da takardar sakina na koma ƙasata na sama wa rayuwata mafita" Ta yi maganar tana riƙe rigarsa tana kuka mai fallasar da dubban damuwoyin da suke binne a ƙarƙashin zuciyarta tsawon lokaci.
"Ma vie" ya furta a kasanlance idanunsa fal hawaye, yana kallon ƙwayar idonta.
"Kar ka sake kira na da wannan sunan da na fi tsanar ji a rayuwata, Ni da nake mummuna, baƙa 'yar Nigeria da ba kowa ba hadima kuma baiwar da ake ci wa mutunci a gaban wanda yake yi mini iƙirarin ni rayuwarsa ce yana ji kuma yana gani. Wataƙila ma alhakin iyayena ne ya kama ni, da na baro su saboda wauta irin ta soyayya da ƙoƙarin sama wa ɗa na mafitar rayuwa. Ka bani ɗa na ka sake ni na koma inda na fito" Ta yi maganar tana zare masa ido tamkar numfashinta zai ɗauke.
Ya saka hannunsa yana ƙoƙarin kamo ta jikinsa, amma ta yi baya tana kai masa duka ta ko ina, cikin kuka tana faɗin "Na tsane ka, na yi nadamar saninka, rayuwata da kai bai amfana mini komai ba, ban taɓa zaton za ku iya haɗa kai ku cutar da ni haka ba, ka bani ɗa na na gaya maka"
Mahmoudu sai da ya tsure, ganin yadda kamaninta har canzawa suka yi saboda faÉ—a, idanunta tamkar ta tauna barkono saboda ja, ga ambaliyar da hawaye suke yi a fuskarta.
A ɗan iya sanin da ya yi mata, tana da sanyin hali, banda tsiwa da ta kan yi wasu lokutan, bai taɓa tunanin za ta iya burkicewa haka ba.
Shi kansa Imam Hammad sai da ya tsorata, yanayin da take ciki ya tabattar masa, sai ya yi aiki tuƙuru kan ma ya samu ta saurare shi.
Ya shammace ta ya damƙe ta, ya nufi wata hanya da ita, ta din ga fizge-fizge, tana ci gaba da kuka da turjewa.
"Ki nutsu, kar ki yi mini asarar cikin da yake jikinki" Wani irin burki ta ci, cike da rikicewa jikinta na tsuma, ji take tamkar ba ta ji daidai ba, sai dai kafin ta tantance, jikinta ya saki ta yi baya za ta faɗi ya riƙe ta.
Jikinta ya yi sanyi ƙalau, sai hawaye da yake fita daga gefen idonta.
Da haka ya yi nasarar shiga da ita É—akin, ya kwantar da ita a kan gadon. Ya zare mata hijjabin jikinta.
Ya zura mata idanunsa, a hankali yake lumshe su yana buÉ—ewa a kan ta.
Ya kamo hannayenta a cikin nasa, ya sumbaci hannayen, sannan ya ce "Duk abin da ki ka yi mini, kuma duk abin da ki ka kira ni da shi, na cancanta, ban kyauta miki ba, na sani ban kyauta ba, amma ki bani dama ko sau ɗaya ne ma viee, sau ɗaya tak, ki bani dama na ce wani abu. Na san ba halinki ba ne, wannan ba halin Husna ta ba ce, amma na karɓi laifina ki yi mini afuwa. Ban yi abin da na yi domin na zalunce ki ba" Ya yi maganar yana kwantar da kansa a ƙirjinta yana sauraren yadda zuciyarta ke bugawa da wani irin matsanancin sauri.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.