Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 48 of 99

Asal kuwa na can a tsaye, tamkar ta haɗiyi taɓarya, idanunta suka sauka a kan agogon bangon ɗakin. Idanunta sun bushe, zuciyarta ta ƙeƙashe sai raɗaɗi da idanun kawai suke yi mata.
Haryanzu ta kasa yadda Hammad ne yake da wata matar, matar ma baƙar fata da a kyau ba ta kai ta komai ba. Babban abin da ya ƙara rikita ta bai wuce batun ɗa da Tafawa ya tabattar mata da Hammad yana da shi ba, har ɗan shekaru biyu ba.
Zuciyarta ta din ga bugawa da sauri da sauri, tsawon lokacin nan ba ta taɓa tunanin son da take yi wa Hammad ya kai haka ba, ashe duk abin da take yi bonono take rufe ƙofa da ɓarawo. Tana zaman zamanta ta janyo masifa da kanta jikinta. Ta din ga tunanin ko dai wata ƙulla-ƙullar ce ta daban aka yi. Sai kuma ta tuna babu yadda za a yi Nana ta samu zarafin shiga har sashen Sultan, su keɓe da Hammad idan ba matarsa ba ce ba. Kenan Sultan ya goyi bayan abin da Hammad ya yi na auren baƙar fata da ba ƙabilarsu ba?. Kawai ta ɗora hannu a ka ta rushe da kuka, hawaye ya ƙi zubo mata sai azabar zafi da zuciyarta take yi.
Gimbiya Bilkisu ce ta shigo É—akin tana faÉ—in "Asal lafiya kuwa?"

"Na shiga uku na lalace Gimbiya, wallahi Hammad ya cuce ni ba zan yafe masa ba. Kuma wallahi sai ya rabu da ita, an cuce ni an cuci rayuwata"

Ta rungume Asal tana rarrashinta, ta ce "Ki yi haƙuri, ki daina wannan kukan kar ki samu matsala, ki kwantar da hankalinki na san Sultan ba zai ƙyale shi ba, zai ɗauki mataki" Asal ta ci gaba da kuka da babu abin da yake ƙara mata sai nauyin zuciya.

*****
Imam Hammad kuwa a hankali ya É—an É—ago fuskar Nana ya ce "Bacci ki ke yi ne?"

Ta girgiza kai alamar a'a.

"To tashi mu ci gaba" Ta noƙe kafaɗa tana ƙara rungume shi.
Ta ce "Imam ka ci gaba mu yi mu bar gurin nan, Aljanun gurin nan sun fara tsorata ni, kar a samu matsala"

"Kina ganinsu ne?"

"Su na bayyana a siffofi daban-daban, tsofaffi tukuf da matasa da wasu halittun daban, duk ina ganinsu addu'a kawai nake yi tun É—azu"

"Ni da ke duniyarm daban take, ƙalubale iri ɗaya, Ubangiji Allah ya bamu lafiya rayuwar Hammad".
Ta sake lafewa a jikinsa ta ce "Ka ci gaba to"

Ya numfasa.

Rayuwa ta ci gaba da tafiya, Hammad na fuskantar suka da ƙalubale kala-kala. A kwana a tashi ya haɗu da larurar zafin jiki, idan jikinsa ya ɗauki zafi tamkar an hura wuta. Babu wanda ya sani sai Asal, dan ya fi kama shi cikin dare, ita ta ɗauka kawai normal zazzaɓi yake yi sai ta yi masa sannu kawai ta ci gaba da sabgoginta.
Sultan ya mallaka masa wannan jakar fatar mai kama da laya, wadda ita ma a cewarsa ta tsari ce, kuma tana ɗauke da aljanun da suke yi wa mamallakanta hidima. Duk lokacin da ya murza zobensa, ya kan gansu a suffar tsuntsaye, irin wanda bai taɓa gani ba a duniya, ko suffar wani abun daban. Wasu lokutan ko be murza zoben ba, ya kan gansu, ko ya din ga ganinsu a barci. Duk da ba shiri suke yi da Yayansa Zahradeen ba, saboda Gimbiya Bilkisu ta shiga tsakaninsu, amma ya taɓa tambayarsa, ko yana ganin wannan tsuntsayen shi ma idan ya murza zobunansa. Zahradeen ya ce masa baya ganin komai, an ce duk mai zoben yana iya ta'amalli da aljanun jikin zoben, amma shi baya ganin komai. Ya tambayi Hammad ko yana gani shi. Ya ce masa aa saboda ya karanta tarihin zobunan a littafin Kundin Agadez ne ya sanya ya tambaye shi. Haka ya tambayi sauran Imam ɗin, su ma dai bai ji alamun akwai wanda yake ganin wani abu ba. Abin da bai sani ba, tun zamanin kakansa, aka canza zobunan, na hannunsa ne kawai na ƙwaran da babu wanda ya sani, sai mahaifinsa da kakansa, sai kuma marigayi Matawalle.
Kwatsam tafiya ta kama Sultan, ga taron sarakuna da za a yi. Sai ya wakilta Hammad ya ce yaje ya wakilce shi. Nan da nan aka hau surutun da me bai wakilta kowa a majalisar sa ba, zai wakilta yaro ƙarami, maimakon ma a ce a cikin Imam ɗin a zaɓi wanda suka fi shi shekaru.
A lokacin Hammad bai daÉ—e da buÉ—e sabon branch É—in gidan abincinsa a MaraÉ—i ba, ya wakilta cousins É—in sa Hasna da Al Hussain a matsayin masu kula da gidan cin abincin.
Babban abin da yake ƙara ɗaga wa masu son ganin bayansa hankali, bai wuce yadda mutane suke son sa ba. Saboda ya iya shugabanci, shi wannan ƙyamar ma da ake nuna wa baƙaƙen buzaye ba ya yi. Yana damuwa da lamuran na ƙarƙashinsa sosai da sosai, wasu lokutan ma kamar ba basarake ba, saboda yadda yake alaƙa da su. Ga kuma girmama shi da suke yi tamkar Sarki. Hasali ya fi nuna saurata da izzarsa a lokacin da yake cikin 'yan uwansa masu Sarauta. Ga shi manyan mutane na son sa, su na son mu'amala da shi, saboda ladabinsa, da iya magana, fiye da sauran Imam, har ma da 'yan majalisar Sultan ɗin, mussaman da duk wanda ya ga Sultan ya ga Hammad, ya san jininsa ne.
Yana ta shirye-shiryen tafiyar taron nan Niemey, a lokacin ga shi nan ne kawai, kansa kamar zai ɓare saboda ciwo.
Yana kwance cikin dare tare da Asal su na bacci, ya yi mafarkin wani sanye da baƙaƙen kaya, yana soka masa allura a ka.
Ya farka a razane, sai dai ya din ga jin raɗaɗin allurar nan a zahiri. Ya sanya hannayensa biyu ya dafe kansa, yana rintse idanunsa yana ambaton Allah, amma kan tamkar zai yi bindiga. Ya tashi zaune da kyar ya yaye bargon da ya rufe jikinsa kawai ya ga wata takarda. Ya ɗauki takardar ya duba sai ya ga hoton ƙwarangwal na ci da wuta, ga sunansa a jiki. Hakan ya yi daidai da sake jin kamar kwanyarsa za ta zazzago.
Ya kifo daga kan gadon ya a rirriƙe kansa, ga jikinsa ya fara wannan zafin. Kawai ya din ga jin idan bai bar garin nan ba, mutuwa zai yi saboda wata irin azaba da yake ji mara misaltuwa.
Ya yinƙura ya tashi da kyar, ya ga Asal a zaune a kan gadon tana kallonsa, ya nufi hanyar fita jikinsa na tsuma, amma kasancewar dishi-dishi yake gani, ya faɗi a gurin.
Washegari ya tashi normal, sai dai jin da yake yi idan bai bar inda yake ba, kamar zai zauce.
Ya yi tafiyarsa É—aya gidan nasa, ko zai daina jin abin da yake ji, amma abu ya din ga jin cigaba, ya din ga jin kamar a cikin wata masifa yake.
Ya yi waya da Mahmoudu a kan tafiyar su, ya ce masa su haÉ—u a É—aya gidan nasa.
Gaba ɗaya ya ji tashin hankalin na ƙara ƙaruwa, ga wata kururuwa da yake ji a cikin kunnuwansa, ganin wasu irin halittu su na yi masa shawagi a kansa. Su na ta watso masa takardun nan na zanen ƙwarangwal. Yana daga kwance ya din ga jin ana kiransa, ana ya tashi ya je gidan ajiye kayan tarihi ana nemansa. Ya toshe kunnunwansa, amma ya gaza daina jin hayaniyar.
Jin da yayi yana neman ya haukace, kawai ya tashi ya fita ya hau tafiya. Duk da da ɗa  nisa daga gidansa na wajen masaruta, haka ya din ga tafiya har ya je gidan tarihin. Yana zuwa mai tsaron ƙofar ya buɗe masa. Da takardar nan mai hoton ƙwarangwal ya sake cin karo,  muraran a zahiri ya din ga ganin aljanun da ke cikin gidan tarihin nan, muraran a siffofi daban-daban. Su na ta fitowa daga cikin ɗakunan nan, wasu su na ratso bango su na fitowa, suka nufo shi su na yi masa wani irin ihu. Ya toshe kunnunwansa, sai ga waɗanda yake gani a suffar tsuntsaye, sun bayyana su na make masu nufo shin. Wata irin guguwa ta tashi a tsakiyar gurin, aka yi wata irin walƙiya mai ban tsoro sai ga Giyaz ya keto ta tsakiyar gidan tarihin ya bayyana a gabansa.
Giyaz ya nufo shi, wannan tsuntsayen suka yi kansa, shi kuma Hammad ya tashi ya fice daga gurin, jiri yana É—ibarsa, ya san ya fito daga gidan tarihin sai dai bai san ina ya nufa ba, kawai ya buÉ—e ido ya gan shi a sahara tare da Mahmoudu.
Ya yi shiru yana kallonsa, sai ga Giyaz ya kuma bayyana a cikin saharar, cikin tsofaffin kayan nan tamkar auduga saboda tsufa. Ga wani irin sauti da saharar take yi, tamkar iskar za ta taso.
Wata irin dariya Giyaz yake yi mai ban tsoro.
Ya ce "Ban sani ba, ko haɗuwa da kai ya sanya na ce na fi kowa sa'a a cikin sararin Duniyar nan, saboda aikin da aka bani a kanka, ya sanya na samu 'yanci. Ni ne Giyaz ibn Jaddul Jinn, ɗaya daga cikin aljanun da suka yi wa kakanninka hidima, daga ƙarshe aka kore shi daga fadar, saboda wani laifi da ya aikata da bai taka kara ya karya ba. Ya tattara iyalansa ya koma Nigeria da zama, ya cigaba da hayyayafa, can ma aka samu waɗanda suka ƙara cutar da shi. Duk da na shafe tsawon shekaru ashirin a tsare, yau wani boka ya bani 'yanci, sannan ya damƙa mini aiki a kanka. Dan haka ko zamu mutu tare sai na cika aikin nan da na karɓa a kan ka" Hammad bai gama gane me Giyaz yake faɗa ba, hankalinsa ya gushe.
Bayan ya sake farfaɗowa, ya sake tozali da Habu, sai dai ya manta a inda ya san shi, ko ya taɓa ganinsa.
Duk iya ƙoƙarinsa ya kasa tuna komai game da kansa. Shi dai ya san shi mutum ne, duk wani abu da ya shafi rayuwa yana iya tuna shi, amma duk wani abu da ya shafe shi, ya manta.
Ko da Habu ya yi yinƙurin mayar da shi Agadez, bin sa kawai yake yi, amma bai san waye shi ba, sai dai su na dosar Agadez Giyaz yake bayyana, yana feso mu wata irin wuta mai ban tsoro, a take sai jikinsa ya ƙara rikicewa ya ji tamkar zai zauce kansa yana wani irin gigitaccen ciwo, bugun zuciyarsa ya ƙaru, ya din ga jin zafin wutar da Giyaz yake feso masa a jikinsa ta na ƙona shi. Gaba ɗaya ya rikicewa Habu. A dole suka bar Agadez suka nufi Nigeria. Su na tafe Hammad yana ganin abubuwan da ya lura abokin tafiyarsa wato Mahmoudu ba ya gani. Duk tambayar da ya yi masa a kan waye shi, ya sunansa ya tuna wani abu game da rayuwarsa amma ya kasa.
Da suka shigo Nigeria, suka samu masauki, bai sake ganin Giyaz ba, sai dai lokaci zuwa lokaci wannan zafin jikin yana tayar masa.
Tun da suka shigo Nigeria, yake mafarkin wata matashiyar budurwa, tare a cikin sahara. Sai ya kwaÉ—aitu da son saninta a zahiri. Idan ya kwanta bacci, ba abin da yake mafarki sai wannan yarinyar. A duk lokacin da ya farka, sai ya din ga jin akwai wani abu mai muhimmanci da yake son haÉ—uwa da shi, duk a duniyar da ya farka, babu wanda ya sani, banda iya mutanen da yake iya gani.
Gurin mai magani na farko da suka fara zuwa da su Habu, wata yarinya ta gifta shi, ya ji wani irin daddaÉ—an sanyi ya ratsa shi, ya din ga jin tamkar ya koma ya bi inda ya ji sanyin nan.
Haka da suka sake haɗuwa a gidan Sarkin baka, bai ga fuskarta ba, amma sanyin nan ya ƙara neman ya zauta shi.
Sai dai ya sha mamaki, da ganin wani zanƙalelen mutum yana bin ta a baya, sai dai baya iya ganin iyakar tsawon mutumin.
Gaba ɗaya ya lura, gane-gane da yake yi,  shikaɗai yake ganin abun sa. Lokaci lokaci ya kan yi mafarki da gidan tarihi, sai dai ya kasa tuna ina ne gurin.
Duk lokacin da ya yi mafarkin yarinyar nan, ya kan tashi da matsanancin farin ciki mara misaltuwa, ya kan ji dama su dauwwama a cikin baccin nasa ba sai ya farka ba.
Tun da suka fara aiki a gidan Alhaji Zailani, duk lokacin da zai gan shi, yana ganin jini yana bin sa, da wasu ƙanan yara, da wasu mutane su na kuka, amma Alhaji Zailani ba ya ganinsu, sauran mutane ma ba sa ganinsu, sai shikaɗai. Hakan ya jefa shi a cikin damuwa, da jin cewa shi wata halittar ne daban, da sauran mutane.
Sai dai babu zato babu tsammani, ya yi ido huÉ—u da ita, da wani yammaci ta fito daga cikin gidan, wannan dogon mutumin yana biye da ita, sai dai ya ga wannan tsohon ne ya dawo matashi, bai bayyana a suffarsa ta tsohon da ya saba fitowa ba.
Sanyin da ya ji ya ratsa shi ya sanya ya rikice, ya ƙudurce a ransa akwai wani abu da bai sani ba, ko yakamata ya sani, kuma wataƙila wannan da suke tare zai iya gaya masa waye shi, kuma daga ina yake!.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.