Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 40 of 99
Ta girgiza kai ta ce "Abokiyar zamana ce"
"Allah sarki, gaskiya daga ji tana sonki sosai ji yadda ta rikice" Shukura ta yi murmushi kawai. Sai dai ta tafi tunanin ta yadda za ta fuskanci Duniya ta sanar da cewa mahaifinta shi ke da alhakin sace ta, da salwantar mata da É—a, da kuma mummunan zaluncin da ya yi wa mahaifiyarta da wadda yake tare da ita yanzu. Ita gaba É—aya ma ba ta san ta ina zata fara bayanin miyagun ayyukansa a idon duniya ba a matsayinsa na mahaifinta.
****
Nana tana son ta ga Sarkin Baka, akwai maganganu da dama a bakinta, amma ƙiri-ƙiri Sayyid ya hana. Ga shi ba ta da damar fita idan ba umarnin hakan a ka ba ta ba, tana son sake ganin Nene ma amma babu halin fita.
Zaman Nana a guri ɗaya, ba fita daga ci sai sha da kwanciya, ya sanya ta ƙara yin kyau, ga lafiyayyen Abinci. Sai dai haryanzu kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya ne ba ta da shi.
Tana zaune tana zancen zuci, har bacci ya fara sace ta, ta ji an taɓa ta. Ta tashi da sauri tana kallonsa.
"Har kin fara bacci ba ki jira ni ba?"
"Eh, na zata a gurinta zaka kwana ai"
"Idan ma na kwana a can É—in, ai ke ki ka ja, kin daina damuwa da ni, ko tausayina ba kya ji"
Ta kwaɓe baki ta ce "Garin tausayinka, na kwashi wani cikin na haihu ku kaɗa ni Nigeria"
Ya É—an marairaice murya ya ce "Haba Ma vie, Sayyid É—inki ne fa, ke ba kya kewar É—umin jikina ne"
Nana ta kalle shi ta ce "Wane É—umin, ai yanzu jikinka ba wani É—umi idan ba azaba ba"
Ya rausayar da kai ya ce "Da É—in ma akwai, kuma kina jurewa"
Ta girgiza kai ta ce "Amma bai kai na nan ba"
"To ni ki bani Sanyin dan Allah"
Ta tsuke fuska ta ce "Sayyid ka daina taɓa ni dan Allah, ni ba ƙin ka nake yi ba, amma ka tausaya mini inga yadda al'amuran za su kaya tukuna, ka san dambarwar da ake ta yi haryanzu ni tsoro nake ji kar a yi mini yadda aka yi wa Nene"
Ya kwanta a gefenta ya numfasa ya ce "Ta baki labari kenan?"
Ta jinjina masa kai alamar eh.
"In sha Allah a kanmu wannan muguwar al'adar za ta zama tarihi, dan ba zan yarda na rabu da rayuwata ba"
Nana ta zumɓura baki tana kallonsa, ya ce "Da gaske nake Ma vie" Ya yi maganar sumbatar hannunta.
Ta É—an lumshe ido tana kallonsa. Ya ce "Tashi mu je"
"Ina?"
"Zo mu je ki gani mana, ko zan cinye ki ne" Ya yi maganar daga kwnace yana ci gaba da kallonta.
Ta tashi zaune tana faÉ—in "Na sani, ko cinye nin zaka yi. To ka tashi mana kuma ka kwanta"
Ya yi shiru bai ce mata komai ba. Ta waiwaya ta kalle shi, ta ga yana yi mata wannan kallon yana shafa bayanta.
Ta ce "Yane? Ko in kwanciyata ne?"
Ya ce "Allah sarki Hammad bawan Allah, kowa baya so na" Ya yi maganar yana tashi zaune.
Nana ta yi murmushi ta kai hannu ta shafa gashinsa ta ce "To dama wa zai so rigimamme"
"Allah sarki, Ina kewar Ma vie É—ina ta da, mai so na da tausayina, ko motsi na yi hankalinta yana kai na, Allah sarki Asmyna ta Nigeria, soyayyarta ta daban ce a cikin zuciyata"
Nana ta ce "Allah sarki Sayyid ɗina na Nigeria, da baya ganin kowa a duniyarsa sai Asmynsa kaɗai. Mai kallona da idon tausayi, wanda nake iya gano ƙaunata da tausayina a idanunsa, mai yaba duk wani motsina da ƙoƙarina. Ina kewar Sayyid ɗina na Nigeria"
Ya lumshe idanunsa ya buÉ—e ya ce "Wannan Imam É—in na Agadez fa?"
Ta kalle shi ta ce "To ga shi nan dai, ban ma san inda ya dosa ba" Ta ƙarasa maganar tana murguɗa baki.
Ya yi dariya ya ce "Haka za ki ce ko? Ni É—in ko? Sayyid É—inki ne fa"
"Sayyid nawa, Hammad na Asal"
Ya ce "Wow, sake faɗar sunan na ji?" Ta noƙe masa kafaɗa.
Ya ce "Shikenan ma, dama Asal ta fiki iya faɗar sunan" Ta harare shi, tare da sauka daga kan gadon. Shi ma saukkowar ya yi, ya wuce gaba ta bi shi a baya. Daga bisani ya jira ta, suka tafi tare. Ƙofar nan da suke bi su fita hanyar saharar nan, suka shiga, sai dai wannan karon canza akalar hanya, zuwa wata matattakala. Tsoro ya fara kama Nana, amma ta kasa magana, sai rarraba ido kawai da take yi.
Wata ƙofa suka iso, ya ce "Kin san ina ne nan muka ɓullo?"
Ta ce "A'a"
"Gidan tarihi ne na masarautar Agadez"
Nana ta ce"Wannan dutsen da nake hangowa?"
Ya jinjina kai ya ce "Eh nan ne"
Wani takurarren tsoho suka tarar a bakin ƙofar shiga gurin, yanayin ƙofar ya bayyanar da tsufan da ta yi a Duniya.
Tsohon ya miƙe jikinsa na rawa, ya risuna yana gaida Imam Hammad.
Hammad ya amsa cikin girmamawa. Nana ta ɗan tsaya ta yi shiru, tana nazarin ƙamshin turaren da ta ji a gurin, kamar ta taɓa jin sa a jikin wani, sai dai ba ta ga alamun a jikin wannan tsohon wannan ƙamshin yake tashi ba.
Ya buɗe musu ƙofar, suka shiga. Ya kunna makunni, sai ga hasken fitilun ya haske gurin.
Ya ci sunansa gidan tarihi, Nana ta faɗa a zuciyarta. Wani irin ƙaton guri ne mai kama da falo, da ƙofofi kashi-kashi a gurin.
"Wannan gurin kamar Libraryn Ƙaisar saboda tsufa" Ta ɗaga kai tana kallon tsawon gurin, jikin dutse ne aka rarake aka yi wannan ginin da ƙofofi. Kanta ne ya sara ta yi shiru tana tunanin kamar ta san gurin nan, ta taɓa ganin gurin. A take ta fara jiyo wannan ƙamshin da take ji idan ta gan su a wannan ɗakin tare da Sayyid.
Hammad ya kama hannunta ɗaya, ya buɗe ƙofa suka shiga, a take ta sske rikicewa, jikinta ya hau rawa ta kalle shi ta kalli ɗakin, ta sake kallonsa ta kalli ɗakin.
"Sayyid wannan É—akin"
"ÆŠakin da muke zuwa ko?" Ya yi maganar yana yi mata murmushi.
Ta kalli gadon, da mudubin ɗakin, komai irin na da sosai da sosai, sai dai yanayin kayan ya nuna, wanda suka yi amfani da ɗakin masu faɗa a ji ne. Ta dafe kanta da take jin wata irin ƙara a ciki, ga ƙamshin turaren nan ya cika ilahirin gurin.
"Sayyid wai ya aka yi haka ta faru a zahiri? Kar daga baya ka ce mini mafarki ne, ka fita da ni daga gurin nan kar na haukace Sayyid"
"Ba za ki haukace ba, ki tsaya na yi miki bayani"
Wani irin jiri ne ya din ga É—ibarta, ta din ga ganin wasu irin halittu na shawagi a É—akin, ga hayaniya da suke yi cikin sauti mara daÉ—in ji.
Jikin Nana na tsuma ta ce "Ka fita da ni daga gurin nan, wasu abubuwa nake gani ka fita da ni"
"Babu wani abun tsoro fa a gurin nan, ki nutsu zan gaya miki komai daki-daki ciki har da abubuwan da suke shige miki duhu a kaina"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.