Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 10 of 81
     NA
*AUTAR MANYA*
_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._
             Â
*11*
"Oga Aliyu" yaji an kirawo sunansa gabaki ɗayansu basuji sallamarta ba bare suji buɗewar ƙofarta illa ganin ta dasukai akansu.
Wani irin wawan tsaki yaja tare da mayar da kansa ga aikin gabansa, Usman ne ya dubeta tare da cewa, "A,a lina har kun tashi kenan haka da wuri hope dai babu wani matsala?" matsowa tayi gaban table ɗin daya sada kansa tana aika masa da wani irin shu'umin kallo tamkar zata lashe shi tunda take bata taɓa ganin haɗaɗɗan namiji kamar *HAIDARA* ba tana kwaɗayinsa tana buƙatar sa ajikinta tana son taji ta rabu acikin faffaɗan kirjinsa wanda take ayya irin raɓar dazata kwasa a wajan sedai kash ta makaro domin shi ko kallo bai yarda ya haɗasu ba.
"O.g.a.A.l.i.y.u" ta kuma faÉ—i a rarrabe batare data baiwa usman amsar tambayar dayake mata ba, É—ago idanunsa yayi a karo na biyu tun bayan shigowarta tare da zaro mata manyan idanunsa waÉ—anda suka kuma firfitowa fuskarsa babu alamun sassauci bare taga waje.
"Ke! stay out from my office"! yafaɗa yana watsa mata wani banzan kallo, ganin tana binsa da idanunta yasa ya kuma ɗagowa "I say get out!"yafaɗa tare da dukan table ɗin da ɗan ƙarfi kaɗan yanajin zuciyarsa tana bugawa da ƙarfi kamar wanda yay gudu.
Jiki na rawa ta raɓe fitt ta fice a office ɗin cikin jin haushi.
Tana fita yaja ajiyar zuciyar tare da lumshe idanunsa ya mayar da kansa jikin kujerar yana jin kansa yana sara masa wannan wani irin masiface agida ba,a barka ba a office ma haka yarasa me mata ke gani a tare dashi suke liƙe masa.
"Tuzurun ammi yakamata ka dai naiwa lina hakafa sabida kaga ba musulma bace kada taga kamar kana jin ƙyamar addininta ne".
Yaji muryar usman cikin dodon kunnensa.
ÆŠago idanunsa yay tare da zubawa usman batare daya ce masa komai ba amman tabbas! bada ban usman É—an uwanshi bane daseya gaya mashi magana mai zafi.
"Wannan tsarin naka bai ba, shin waikai bakada feeling ne kamar sauran mutane?".
Still usman ya kuma jefa masa wannan tambayar.
"Eh bani da dutse ne ni, ko angaya maka kowa sarkin kwashe, kwashe ne kamar kai?, Ok ba matsala xaka iya ƙarama zainab ay da wannan ɗin".
Yafaɗa tare da mayar da kansa ƙasa.
Wata shegiyar dariya usman ya saki tare da cewa.
"Aikam kaima kasan gaf nake danni senai huɗu ciff waya gaya maka kowa irinka ne ai wallahi senasa ammi ta ɗauko maka mai roƙiya kai ace baka da abinki se wadda tace tana sonka, yanxu dai ai abba ya gama komai nan da ƴan kwanaki kaɗan kazama na khadija".
YafaÉ—a yana dariya........
"Ni wallahi dama ni aka haÉ—a da ita dase nai tsalle amman kai ka samu kana yanga".
Wata harara ya zabga masa tare da miƙewa cikin wannan ɗan room ɗin ya shige yabar usman a tsaye sake da baki.
Mintuna kamar biyar ya fito hannun rigarsa a tattare kansa jiƙe da ruwa da alamun alwala yayo.
Batare daya kula usman ba yabar masa office É—in.
Fita yay daga section É—in nasu baki É—aya É—ayan section É—in ya shiga inda anan ma'aikatan kamfanin ke da office kuma sannan anan ake fidda komai a shigo da komai, haka zalika masallacinsu shima duk anan yake kasancewar section É—in yanada mahaukacin girma.
Tunda ya fito suke masa barka da fitowa harya ƙarasa cikin babban masallacin abin mamaki yawanci ma'aikan duk suna zaune aciki yana zuwa suka miƙe gabansu ya shiga yaja musu jam'i cikin daddaɗar muryarsa cike da nutsuwa yake jansu har suka iddar da sallar, bayan anyi addu,a an shafa ya gaggaisa da jama'ar masallacin kana yabaro nan ya taho wajan daya kasance muhallinsa anan ma'aikatar.
Baiga usman ba dan haka ya ƙara gudun AC'n cikin office ɗin yacigaba da aikin gabansa.
Ƙarfe huɗu ya kuma kowama cikin masallacin sukai sallah sannan ya dawo office aiki yake da ƙarfinsa da lafiyar da Allah ya bashi.
Ƙarfe biyar da kwata usman ya shigo tare da azalzalarshi akan yazo su tafi gida shi yana da wadda take waiting ɗinsa..
Murmushi kawai yay bayan yagama jin tabakin usmanÉ—in wanda murmushin yay mugun yimasa kyau batare dayace komai ba, yaÉ—auki laptop É—inshi daya bari jiya tare da wayoyinshi.
Gaba yay yabar usman batare daya kulashiba da nura sakatare sukaci karo wanda yake ƙoƙarin amsar laptop ɗin cikin kulawa ya dubi nura.
"No barshi jeka kulle office akwai key a saman table and pls kaje gareji ka amsomin motana ka kawomin gida pls".
"Angama mai gida".
Nura ya faɗa cikin kulawa sannan shikuma Aliyun ya wuce da ƙyar usman ya cim masa acan farfajiyar kamfanin sabida Aliyu yana da zafi shiyasa komai nasa yake da zafi zafi baya sanya namijine na gasken gaske.
"Kai dallah ina can sake da baki ashe kayo gaba ka barni".
Usman ya faɗa cikin ƙufula bai kula shiba illah gaban daya kumayi cikin sauri.
Gaban wata ash corolla, suka nufa usman ya zauna a driver seat shikuma ya zauna a front seat batare da ɓata lokaciba security's suka buɗe masu gate ɗin tare da ɗaga musu hannu.
Usman kaɗai ya maida musu shikam ƙasa yay da kansa yana danna wayarsa.
"Amman yakamata ka fito kaiwa su abba bayani sabida gudun matsala".
Cewar usman wanda hankalinsa ke kan titi, wanda kai tsaye titin yahaya gusau ya É—auka.
Ɗage girarshi yay ta ƙasa alamun bai gane ba tare da kumayin ƙasa da kansa.
"Ina nufin kacewa abba baka da lafiya a nema maka magani, gudun kada ka cutar mana da ƙanwa".
Usman ya faÉ—i yana guntse dariyarsa.
Hannunsa yasaka yaÉ—an shafo gemunsa kaÉ—an yana sakin wani irin killer smile wanda na kasa gane na komaye batare kuma daya tankawa usman ba........
*INA MASOYANA MASU BIBIYAR LITTATTAFAINA YAUMA TAFE NAKE DAWANI ALBISHIR GAREKU KO SHIN KUNSAN NA SAKI ZAFAFAN LITTATTAFAINA GUDA BIYAR AKAN FARASHI NAIRA DUBU ÆŠAYA? WAÆŠANDA SUKE HAÆŠE COMPLT A DOCUMENT ÆŠINSU DA KIN SIYA SE KARATU*
*ÆŠAN MAJALISSA*
*KOBA SO*
*HASKE*
*RABON WANI*
*DA IZZATA*
*DUKKANSU AKAN FARASHIN NAIRA DUBU ÆŠAYA COMPLT GAMAI SO YA KARANTA SEYAY MIN MAGANA TA WATSAPP NUMBERTA KAMAR HAKA 08142105218*
11/14/21, 3:06 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
{ _HOT LOVE_ }
NA
*AUTAR MANYA*
_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._
*12*
"Hmmmm kaji wasan yafi ƙarfin kanka ko?, aidaman nasan bazaka ce komai ba tunda kai dai bakada kuzari anan wajan".cewar usman wanda gabaki ɗaya hankalinsa yana kan titi amman tsabar jarabar surutunsa yasa yana tuƙin yana magana, tsaki *Haidara* yaja kaɗan tare da mayar da hankalinsa bisa kwalta yana kallon yadda motoci da adai dai ta sahu da babura ke shawagi akan babban titin sharaɗa yahaya gusau.
Tabbas kano tacika babban birni gari mai tarin albarka kano ta dabo cigari kano ta dabo tunbin giwa kodame kazo anfika, lumshe manyan idanunsa yay yana ayyana yadda yake matuƙar son wannan gari mai tarin albarka.
"Wai ni kamayar É—an iska inata surutun banza ko?, kayimin banza sabida rainin wayo waikai dan Allah bakajin bakinka yana wari?".
Cewar Usman wanda yake kallon Haidara cike da takaicin wannan muskilancin nasa.
"A,a to mezan ce maka?, kayi tambayarka kuma kabawa kanka amsa to kuma maiyay saura, nikam surutu baya cikin tsarina gwara naita yiwa ubangijin girma tasbihi ana taramin ladan akan naita surutun da baida amfani, wanima idan nayi zunubi xa,a rubutamin".
Yafaɗa tare da jingina kansa ajikin seat yana motsa bakinsa alamun tasbihi yake ga sarki buwayi gagara misali maikowa mai komai maƙagin sammai da ƙassai wanda mulkinsa baya ƙarewa.
"Kai masha Allahu wallahi Kanafa burgeni mutumina ɗabi'unka abin koyine ina godiya ga sarki Allah dayasa kazo acikin zuri'armu Allah ya ƙara mana suttura da'ima".
Cewar usman ya faɗi hakan yana maijin daɗi acikin ransa shi kansa ɗabi'un Aliyu yana burgeshi mutum ne nutsatstse mai hankali da kamala sam baya da hayaniya bare yawan magana idan yana office zaka gansa zaune yana aikinsa, idan yana gida zaka ganshi a ɗakinsa riƙe da alkur'ani mai girma yana karatunsa, kokuma ka ganshi zaune akan sallaya yana nafilfilunsa, sedai fa akwai tsare gida da miskilanci haɗi da mugun taurinkai da saurin zuciya abu kaɗan kesaka ALI fushi musamman akan ƙannansu suna mugun shakkarshi hatta yayyenma suna shakkarsa sabida bai cika sakin fuskarsaba bare ka, kawo masa raini, amman ga wanda yasanshi shiɗin mutum ne mai daraja ɗan adam sam baison yaga wani ya wulaƙanta yana da mugun tausayi da rauni, shiyasa sam abin hannunshi bai rufe mashi idanunshi ba idan ya maka wata kyautar wallahi sekai kukan daɗi sabida bai iya kyauta kaɗan ba.
Da kallo Haidara yabi usman ganin yay shuru kamar yana nazari, ɗan taɓoshi yay kaɗan"Hy malam kada ka zubda mufa, gwarakai ana shirin juye maka nikam banga komai ba". yafaɗi maganar a fusge kamar ba shiba.
Jan ajiyar zuciya usman yayi tare da kallon Haidara kaÉ—an sannan yace"Wallahi Man kawai tunanin irin kyawun É—abi'unka nake wallahi kaji daÉ—inka fa".Usman yafaÉ—a yana mai karya kwanar dazasu shiga tare da danna hancin motarsa cikin kwanar.
"Hmmm É—abi'una idan har masu kyaune to ba burgeka nake son suyi kaÉ—ai ba No ina son ka koyesu, musamman ma wannan surutun naka dan Allah ka rageshi haba mutum kamar aku"
YafaÉ—a yana Æ´ar dariya kaÉ—an.
Wani irin kyau dariyar tayi masa musamman yadda dimple point ɗinsa suka lotsa kaɗan ga fararen haƙoransa sun ƙara wani haske tamkar ƙanƙara.
Sakin baki usman yay sabida daman idan kaji Haidara na irin wannan dariyar tofa yaÉ—an kunno usman ne.
"Aikuwa kayimin one zero wato nikeda surutu ko?, hmm zamu haɗu next wallahi sena rama" usman yafaɗa tare da karya wata kwanar still wanda cikin layin da suka shiga ya kasance tsitt babu alamun hayaniya ko kaɗan tafiya mai ɗan nisa sukai tare da nufar wani mahaukacin tangamemen baƙin gate wanda aka rubuta *ALHAJI GIƊAƊO MAI ATAMFA ESSTATE* da manyan baƙi tundaga nesa da gate usman kefaman zuba uban horn cikin sauri wasu ƙartin sojoji suka tawo cike da ƙarfi da zafin nama suka wangale ƙaton gate ɗin aguje motar usman ta faɗa cikin farfajiyar wannan gate wanda cikinsa yay kama da wata anguwar sabida girman esstate ɗin.
Wajan adana motoci ya nufa waɗanda su kansu motocin gasunan burjik kamar banxa kowacce da kalarta parking ya gyara tare da kashe motar sannan ya dubi Haidara,"Malam seka sauka ka ƙarasa part ɗinku da ƙafarka dan wallahi bazan ƙarasar da kaiba anan parking lot ɗin naga damar ajeka" batare daya tankawa usman ba ya buɗe ya fita yana mai shaƙar iskar waje ƙafafunshi ya taka har cikin part ɗinsu hannunsa riƙe da system ɗinsa wanda daga parking space ɗin zuwa cikin part ɗin akwai ƴar banxar tafiya anan na fuskanci ashe esstate ne ƙaton gaske mai ɗauke da part kusan bakwai, daga gate ɗin farko kenan wanda ya kasance na iyaye domin shi Haidara part ɗin farko ya shiga shikuwa usman gate na biyun ya nufa wanda nake tunanin ko anan sukesu.
Gaban wani ɗan medium size gate ya tsaya tare da saka hannu yaja shi ya buɗe ya shiga babban gidane wanda ya tsaru ya haɗu ƙofar farko ya buɗe wadda ta kasance kana shiga xakaga katon falo wanda yasami nasarar lamushe manyan saitin kujeru kusan uku, zube ƙafafunshi yayi asaman lallausan carnies carpet ɗin dake malale a tsakiyar falon bai tsaya anan ba wani corridow yabi wanda yayi ƴar tafiya kaɗan daga gefan corridow ɗin ƙofar wani falonce still, sekuma step ɗin bene wanda nan naga ya haye yana tafiya da zafi-zafi hannu ya saka ya buɗe ƙofar falon saman tare dayin sallama abakinsa ƙaton falone wanda yaci kujeru saiti biyu se babbar tv plazma, ƙatuwa akan tv stand se two bedroom dake cikin falon tare da ƴar wata ƙofa a gefe wadda nake zargin ko ɗakin da furji yakene.
Room ɗin farko ya tura ya buɗe ƙofar tare dayin sallama sannan ya shiga ciki wani irin ƙamshine mai sanyi ya shige masa jikinsa tare da daddaɗan sanyi mai ratsa ɓargon jiki.
Kan ɗan medium table ɗin dake tsakiyar ɗakin ya aje system ɗinshi tare da wayoyinshi, se asannan nabi ɗakin da kallo babbane sosai babu wani shirgi cikinsa daga ƙaton close set se wani lafiyayyan bed mai girman gaske wanda aka ƙawatashi da white bedshit da pillows masu kyau, ɗan dressing mirrow ne a gefe wanda aka aje hand drayer tare da cream, se sopa da wannan table ɗin se Bathroom ɗin dake gefe daga wani ɗan kwana.
Botiran gaban rigarshi ya fara buÉ—ewa...........
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.