Romantic Hausa Novels

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 80 of 81

*ZUMA A BAKI...!*🌹
{ Painful love Story }

_Shine sabon littafina da ze soma zuwa da zarar na kammale wannan kedai/kaidai maza ka hanzarta ka biya naka domin tun kafin na soma posting ɗinshi zan soma karɓar kuɗin masu son karantawa kai dagajin sunan kasan akwai rikita rikita wadda bazan ce komai ba amman rubutuna ze bayyana muku *Zuma A Baki* comming soon da izinin Allah ƙofa a buɗe take masu soma payment_

*ÆŠAN ÆŠANO*!
_Wannan karon tafiya nai mai mugun nisa har naje na zaƙulo muku ƙayataccen labarin masoya Biyu *Umar Muhammadu Sarkin-Gida* wanda jama'ar unguwa da abokai ke masa laƙani da ( *Cika Daji* ) Eh cika dajin ne mana sabida duk umar ba,a rago to hakance ta kasance ga shalelen inna kuma autanta wanda ya tsunduma a dafkin kogon soyayya da *Aishatul humaira* ɗiyar anty Har soyayyar tasu ta zamewa kowannen su *ZUMA A BAKI* Tabbas tunda nake rubutuna bantaɓa katari da labarin daya kwantamin ya tsayamin kamar ZUMA A BAKI ba! tabbas kodaga jin sunan kasan akwai rikita rikita kuda kawai kubiyoni nasan insha Allah bazan baku kunya ba_

*Hohoho! my fans nace muku painful wallahi da gaske wannan soyayyar mai zafice mai raÉ—aÉ—i ce duk wani masoyi yaci katari da wannan labarin nawa seya dara seya koka seya warwasa labarin ze Æ™ayatar ze tsaya arai ze nishaÉ—antar ze wa'azantar ze ilimantar kudai kubiyoni kawai*💃💃💃💃ðŸ¤ðŸ»

_kai ƙoƙarin ganin kayi payement domin zan soma sakin sane da zarar na kammale wagga_
~N~ *300*# *ta wannan account numbern 0078174806 starling bank show me your evidance of payment ta wagga numbern 08142105218 love you my Æ´an amana my Æ´an iya wuyata*

"Ka ganshi sunanshi ZUMA A BAKI dan Allah oga sunan bai burgeka ba kuma nasan labaranta na karanta naji tabbas baxata bamu kunya ba, shiyasa zanyi maza na tura mata 300naira ɗinnan domin naji da sauƙi ma kuɗin littafin domin naga wata frnd ɗita tana cewa ita tunima ta tura mata nata kudin harta tsunduma ta a grp na ZUMA A BAKI wanda zata fara post da zarar ta kammale wannan"
Zee takai maganar tana kallonshi.
"Ah lallai cwt zamusha karatu maza sender mata 300 ta domin ta sakaki afara ZUMA A BAKI damu domin har na matsu naji labarin UMAR dan tunda naji ance CIKA DAJI nasan wannan ba ragon maza bane".
Dariya zee tai tana kallon yadda usman ke zubo zance.
"Ai daman yanzun nan zan mata transper ta hanyar data nuna mana a tallen nata domin a dama dani".
Zee ta faÉ—a tana kallon Bebi wadda ta mike tare da cewa.
"Kai anty zee gaskiya kin tsumani Allah ya bani waya nima na biya na karanta amman dai bara naje da waÉ—an nan É—in domin yau zan karance su insha Allahu".
"Karki damu kanwata se goben kenan?"
ÆŠaga mata kai tayi alamun Eh sannan ta fita daga falon tanajin kaso goma na cikin damuwar Aliyu ya fita daga ranta.

Koda taje falon Ammi zaune ta tarar dasu harda matarsa wadda suke zaune kujera guda ammi kuma tana saman É—ayar.
Rannan nashi a haÉ—e tamau tana sallama yana harararta a fakaice.
"Harkin dawo?"
Ammi ta faÉ—a mata cikin kulawa.
"Eh ammi na dawo da acan ma zan kwana wallahi sena tuna kuma karkiji shuru shiyasa na dawo É—in"
Tafaɗi maganar da gayya tare da raɓesu ta wuce ɗakin ammi batare data yiwa kowa magana acikinsu ba...........
11/14/21, 3:21 PM - Allah Akbar: *101*

Sosai tabaiwa Aliyu mamakin yadda tai masa wannan shariya, zufar data karyo masa ya saka tissue ya goge duk da azabar sanyin AC'n dake ratsa ilahirin É—akin.
Murmushi Ammi tayi sabida tagama hasashen komai ta riga data gane cewar kishine ke É—awainiya da ita, tashi tayi ta bar musu wajan tai shigewarta É—akin dake kusada nata.
Hamma dija tayi cikin salon kirsa ta dubesa.
"Dear ya kamata ka fito mana da amarya mu wuce naga kamar ma bata lura damu ba".
Tsaki yaÉ—an ja Afili.
"Rabu da ita goben kawai ta koma ta kwana anan"
ÆŠan murmushin jin daÉ—i ta kumayi.
"Haba dear yakamata itama ta kwana a É—akinta tunda ammi ta amince kawai tazo muje na haÉ—a mana dinner"
Kallonta yayi tare da yaba halinta tabbas dija mace ce mai kawaici.
Cikin jin daɗin kalamin nata ya mike da ƙarfin gwiwa ya nufi ɗakin Ammi itako dija zazzafan kishinta ta danne tare da kafe kofar daya shiga da idanunta.
Tura É—akin yayi ciki-ciki yay mata sallama, tana zaune a gefe gado ta kafawa littafin da zee ta bata idanu sosai takejin daÉ—in karatun sabida yadda take fahimtar girke-girken ciki dalla-dalla.
Ƙamshin mayen turarensa shiya bata tabbacin zuwansa, amman setai kamar ma batasan Allah yay ruwan sa a gurinba.
"Madam yakamata ki daina fushi dani hakan nan domin ina azabtuwa"
YafaÉ—a cikin rashin sabo da rarrashin mace.
Banza tayi dashi batare data tanka mai ba.
Riƙo hannunta yayi wanda bata rike littafin dashiba yana matsa matashi cikin wani irin salo.
Ture hannun nashi tai da É—ayan hannunta tare da juya mai baya.
Gaba É—aya tafikan hannayenshi ya zube saman gadon bayanta yana shafowa.
Can cikin ƙasan maƙoshinsa kamar ze saka mata kuka! yace.
"Wai dan Allah mai nayi miki duk kinbi kin É—agamin hankali ki taso mutafi part É—inmmu"
YafaÉ—a yana juyo da fuskarta saitin tasa fuskar yana mai kafeta da idanunshi dasu kai jajur sabida damuwa.
Hawaye ne yasoma zarya a saman fuskarta.
Anan nai kallon kiÉ—ima sabida atake Aliyu yay wata irin dira a gabanta hannayenshi ya saka ya tallafo ta tare da fito da harshen shi yana lashe mata hawayen nata kamar ze tsotse dukkan fuskar gabaki É—aya.
"Nika rabu dani kuma Allah sena gudu wurin mama tunda muka tawo kake hantara ta tunda kazo kai tafiyarka baka kuma waiwaye naba yanzu kuma kazomin da matarka dan Allah ka rabu dani da abinda nakeji a zuciyata".
TafaÉ—a cikin kuka!
Dafe kanshi yayi duk jikinshi yana wani irin rawa gaba É—aya ya gigice ya daburce.
Rungumota yayi gaba É—aya zuwa saman faffaÉ—an kirjinshi hannunshi ya saka yana shafa saman gadon bayanta har zuwa mazaunanta.
Kafin ya lalubo cikin kunnenta ya soma raÉ—a mata kalamai masu kwantar da hankali.
"Haba sarauniyata haba masoyiyata akanki fa ina kasa bacci yanzu tsakani da Allah ke bazaki min uzuriba nazo ban sami hutu ba ina ta zirga-zirga shine naje É—akin dija na kwanta yanzu kuma munfi awa anan muna jiranki ni banyi fushin fitar da kikai babu izinina ba seke haba tawan kada na kumaji kince zaki tafi gidan mama batare da izinina ba keda gidan mama semun je ziyara"
yafaÉ—a mata hakan cikin shaukin soyayyarta.
Jin zuciyarta tayi tai mata sanyi amman duk da hakan bata nuna mashi ba.
Mikewa tsaye yayi tare da zube hannayenshi acikin pocket É—inshi yana mai zuba mata narkakkun idanunshi.
"Tashi mutafi kinsan dija ta bamu sati guda still wai muci amarcinmu a gida".
Haushine ya kuma kamata jin ya ambaci sunan matarshi amman ganin yadda duk ya lanjare mata kamar maraya yasa ta mike tana tura bakinta gaba.
"Toni kai gaba ganinan"
TafaÉ—a cikin É—aure rai.
Murmushi yayi tare dayin gaba kamar yadda tace É—in yana jin jina rigimarta.
Seda tagama yangarta sannan ta bishi yana tsaye a falon shi kaÉ—ai bataga matarshi ba kuma bata tambayeshi ba.
"Ina ammi nai mata sallama?"
Ɗan ranƙwabowa yayi gabanta sabida yafita tsayi nesa ba kusaba.
"Ammi tana wajan mijinta tana basa kulawa kema ya kamata kiji dani"
YafaÉ—a mata hakan yana kanne mata idanunta guda É—aya.
Bai bata izinin magana ba ya kama hannunta suka wuce.
Fita sukai daga falon duk yawani shige mata jikinta shi ko kunyar wani ya wuce ya gansu ba yay kasancewar gidan akwai wadatar haske kamar rana.
Gaban gate É—in part É—inshi ya karasa shiya buÉ—e musu gate É—in suka shiga tana mai karanto addu'a acikin bakinta.
Sosai tsarin falon ƙasan ya burgeta wanda babu komai cikinsa se manyan saitin kujeru na royal masu kalar royal blue.
Step suka haye cikin nutsuwa ya bude kofar glass É—in dake saman ya kama hannunta suka shiga cikin babban falon daya gama tsaruwa da wasu shegun kujeru masu azababban kyau na fitar hankali.
Ƙafafun Bebi suka nutse cikin lallausan carpet ɗin dake falon ga wani kamshi da sanyin Ac sun gama kashe mata jikinta.
Kallo É—aya taiwa falon idanunta yasan an narka dukiya acikinsa.
Ƙofar dake gefe wadda ta kasance itace ta room ɗinta ya bude suka shiga falone a farko wanda aka jera fararen kujeru marasa girma se Tv tare da frij, da wani ɗan table a tsakiya kofar bedroom ya bude suka shiga wanda ya kasance katon gaske wanda yaji saitin kayan gado farare babu abinda yafi burgeta ga wajan face tsarin gado mai uban kyau da ɗaukar hankali kofar dake hagu itace ta bathroom ɗinta.
Sakin hannunta yayi yana mai kallonta.
"Well come to the mai atamfa estate mrs Aliyu idriss mai atamfa Allah ya albarkaci rayuwar auren mu"
YafaÉ—a yana kashe mata idanu guda É—aya zama tai a gefen gadon tana lumshe idanunta domin mugun baccin daya kama idanunta.
"Bacci kike ji? ina zuwa"
YafaÉ—a yana fita daga É—akin.
Kansa tsaye É—akin khadija ya nufa ya sameta zaune gaban madubi ta kifa kanta alamun tunani.
Sallamarshi ita ta dawo da ita daga duniyar tunanin data afka.
Gabanta ya karasa tare da É—agota ya manna da kirjinshi.
"Dija why kika baro falon ammi bayan kince zamuje mu tawo da Beby?'
Yafaɗa mata murya ƙasa-ƙasa.
"Dole na baro can mana sabida naga kiri kiri kana nuna ban bamci a tsakanina da ita alhalin bata fini da komi ba"
Murmushi yayi lallai mata biyu gobara, yagama da waccan ya dawowa wannan.
"Kiyi hakuri ba nufina kenan ba, amman bakiga tana da lalura ba komai sena bita asannu, yanzu dai kiyi hakuri nazo nai miki sallama ne kamar yadda kikace kin bani sati É—aya".
Harara ta dalla mai tana jin dama batai ɓarin zancen faɗin hakan ba.
"Hmm shine yasa naga jikinka yana rawa akan Æ´ar cikinka?"
A wannan karon haÉ—e ransa yayi tamau tare da zareta ajikinshi.
"Ke khadija kada kikaga ina bin ta taki kinemi gayan magana bazan juri cin zarafi daga garekiba koma miye ai ke kika ce nai satin in kuma baki amince ba zan kwanta a É—akin ki domin a lissafi yau kece dani"
Murmushin yake tayi.
"A,a Allah ya raka taki gona ni jini nake bana bukatarka wadda kakeso ka É—irkawa ciki kaje taji da jarabarka ni bazan iya ba".
TafaÉ—a tare da banka kofar toilet ta datsota sanin ze iya kai mata duka.
Dafe kanshi yayi cike da ɓacin rai ya nufi ɗakinsa faɗawa saman gado yayi tare da dafe saitin zuciyarshi yana mamakin yadda dija take gasa masa baƙaƙen maganganu a ɗazu, tabbas bada ban bai da tsarin dukan mace ba daseta raina kanta.
Yajima yana saƙawa da kwancewa acikin zuciyarshi kafin ya mike dukkan jikinshi a kasalance ya nufi bathroom wanka yayi tare da saka singlet and boxer ya feshe jikinshi da turare tare da fita daga ɗakin.
ÆŠakin bebi ya nufa wadda ya tarar da ita,kwance saman gado da alamun baccinta yayi nisa.
Ɗagata yayi tare da kwantar da ita sosai a saman gadon, hayewa yayi gefenta ya janyota jikinshi ya rungumeta da dubara ya zare mata hijabin jikinta tai saura daga ita se doguwar rigar jikinta,bai son ya tasheta sabida yadda doctor yace ba,a tashin mace mai ciki in tana bacci, sosai ya saka ta ajikinshi ɗumin jikinta ya haɗu dana shi wanda hakan ya haifar masa da wata azababbiyar sha'awarta, hannunshi ya zira cikin rigarta ya fiddo da abinda yake muradi wasa yasoma yi dashi cikin maitarsa kafin ya ɗora bakinshi akai yana wani irin zuƙa kamar ze cire mata shi.
Cikin baccinta taji yana ruÉ—a mata jikinta da salonshi, gantsaro mai tai gaba É—aya sabida tana muradin hakan batare da bata lokaciba ya rabeta da kayan dake jikinta yasoma yi mata wasannin data kusan zautuwa.
Tunda take bata taɓajin kamar na yauba sabida yau yay mata abinda tunda mama ta haifeta bata taɓajin irin daɗinshi ba ya nuna mata yes ita mace ce mai daraja a wurinshi.
Sosai yake mika hannunshi akan dukkan inda yasan ze kunno mata wutarta, kafin ya É—agata ya dangana bakinshi zuwa ma'aikatarta wanda atake anan ta saka wani irin ihun daya amsa ilahirin É—akin babu abinda kakeji se nishinsu,sosai ya zage É—amtse wajan faranta mata seda ya tabbatar daya wanke dukkan fushinta na É—azu sannan ya sarara mata É—aukarta yayi cak, kamar Æ´ar bebi ya kaita can toilet suka tsaftace jikinsu kafin ya naÉ—ota ya dawo da ita É—aki, kaya suka sauya kana suka koma baccinsu cike da nutsuwa.
Basu farkaba seda asubahi shiya soma tashi yaje yay wanka yay alwala tare da shinfiɗa abin sallah ya soma gabatar da nafila, lokacin daya idar ana kiran sallar assalatu, Alokacin ya tayar da ita inda shikuma ya nufi masallaci bugun duniya yayma dija domin ta bude ƙofa tai sallah yaji shuru ganin yana ɓata lokacinshine yasa ya wuce masallaci abunshi.
Ahanya suka haÉ—u da abba dasu usman kamar koda yaushe gaisawa sukai ya wuce part É—in ammi har wurin shida yana wajanta.
Kafin ya mike domin yana son fita office anjima.
Bebi kuwa yana fita tai bayi alwala tayo tare da fitowa ta soma gabatar da sallah.
Bayan ta idar azkar tai tare da mikewa ta faÉ—a wanka, bayan ta fito kaya ta sauya masu kyau wadda tai adonta cikin doguwar rigar shadda marar nauyi.
Fita tai zuwa falo da karan bani ta nemi kicin.
Sabida yadda umman mufida kullum ke mata lecture akan tsafta kwalliya da kuma iya girki tare da kula da miji,maganar umman mufida batai tasiri a wurinta ba se yau dataga matarsa hankalinta ya kuma tashi taji zata iya bawa mijinta dukkan kulawarta matukar tana son zaman lafiya dashi seta mike ta cire dukkan gandar dake zuciyarta, ada in mama na mata faÉ—a seta É—auki abin a wasa amman kam yanzu tagane cewar sefa ta mike tsaye inba hakaba duk son dayake mata ze tashi a banza ne.
Cikin nutsuwa ta kunna gas kana ta ɗora ruwan tea duk da yadda bata son warinshi amman haka ta daure ta haɗa komai na tea ɗin bayan ta gama ta fita main falo ta zauna carbi a hannunta tanaja gaba ɗaya nutsuwa ta sauka ajikinta tamkar ba bebin daba lallai zama da nitsatstse shike sakawa kaima kaji kazama nitsatstsen cikin zuciyarta take raya hakan domin zamanta da Aliyu ta ƙaru da abubuwa kala-kala na cigaban rayuwarta.
Zamanta da kamar mintuna uku taji karar bude kofa bata É—agoba sabida taji kamar matarsa ce.
Cikin wulakanci dija take kallon yadda aka É—ora mata tukunya akan gas É—inta kuma tasan ba kowa bace ba face amaryar Aliyu.
cike da gadara ta dawo falon tana wani bude hanci a tsaye ta tsaya akan bebi.
"Ke ƴar matsiyata ubanwa yace uwarki taƙi haɗoki da tukunya setawa zaki ɗauka angaya miki kayana na matsiyatane irin......, Ai bata barta ta karasaba cikin tashin hankalin jin wannan furuci Bebi ta mike ta kwashe dija da mari wanda hakan yay dai dai da shigowar Aliyu,cikin wani irin yanayi Dija ta ɗago a firgice zata zubawa bebi marin domin ta rama.
Cak ya rike hannunta Bebi batai aune ba taji tagwayen marukan Aliyu a fuskarta har guda biyu.
"This is the first and last dazan kuma ganin kin marar min matata duk da ina nuna miki so wallahi baki isa kin takan itaba wannan ƙanwatace ta jini and kuma matata uwar gidana sabida haka banga dalilin dazakiga fuskar marinta ba".
YafaÉ—a mata cikin tsananin zafin rai.
Dafe kuncinta tai cikin mamaki take kallonshi.
Murmushin dole ta saki, tana kuma ganin yadda khadija ke mata gwalo batare data bar Aliyun ya ganiba.
Da sauri Bebi tai É—akinta jikinta yana matukar rawa.
Har wani jiri take gani.
Hijab É—inta ta É—auka ta saka tare da takalmi kana ta fito falon tarar dashi tai tsaye ya goya hannunshi a baya yana kaiwa da komowa A falon alamun komai ya tsaya mai cak!
Matarsa kwa tana saman kujera tana wani hura hanci.
Rabeshi tayi ta wuce sabida babu abinda ze saka ta zauna tanaji gwara ta koma gaban mahaifiyarta taji da abinda ke damunta.
Cikin zafin nama yasha gabanta.
"Kada ki sauka Beby wallahi ranki zeyi mugun ɓaci in kika bude kofar nan"
YafaÉ—a cikin tsawar data saka hatta dija seda ta tsorata dashi.
Wawan tsaki taja tare da nufar kofar ko kallonshi batai ba.
"Wallahi sedai komai zakai kayi amman sena fita"
TafaÉ—a kanta tsaye.
Hannunta yaja da ƙarfi yay bedroom ɗinshi da ita yabar dija da leken kofa datse kofar yayi tare da tsayawa a gabanta yana faman zuba uban huci, ƙam ta tsaya a gabansa gaba ɗaya hawaye ya gama jiƙa mata fuskarta.
"Kaban guri malam zan fita ai nan É—in ba É—akin ubana bane zan tafi na barka da uwargidanka kuma kanwarka ni bare banga amfanin zama dakai ba kamatsa min na fita" tafaÉ—a tana mai kai mai duka a saman kirjinshi jijjigashi take da iya karfinta amman shiko ko gezau yama zuba mata jajayen idanunshi kawai yana kallonta.
Seda ta jigata dan kanta sannan ta daina ta soma zuba uban huci!
Riko tsintsiyar hannunta yay rikon tsauri gam yana mai zuba mata zafafan idanunshi masu uban girma da kaifi waÉ—anda sukai wani irin jajur fuskarshi babu alamun sassauci yake kallonta.
"Bilkisuu"!
YafaÉ—i sunan adake.
"Dan kinga ina sonki shine zaki nemi takamin matata? ko dija bata rigaki aurena ba ai agirme ta girmeki ni ba lusarin namiji bane bazan yarda da sakarci acikin gidana ba"
Kokarin tureshi take amman yaki bata damar hakan.
"Nida tacemin Æ´ar matsiyata ta zagi mahaifiyata akan na É—ora maka ruwan shayi a tukunyarta baka É—auki mataki ba se ita dayake kanwarka ce tonima Allah yasa iyayena basu haifan ni kaÉ—aiba"
TafaÉ—a tana murguÉ—a mashi bakinta gaba.
Kana ta cigaba dayi mai bayanin duk abinda ya faru cikin kuka!
Jikinshi ne yay wani irin sanyi zubewa yay a wajan ya janyota jikinshi ya rungumeta kafin ya É—agota.
"In dai marina ze sakaki jin dadi ga fuskata kita mari har kiji zuciyarki tai sanyi pls am very sorry wallahi laifina ne da ban nemi ba'asi ba"
YafaÉ—a muryarshi na rawa kamar zeyi mata kuka!
Tureshi tai tana kuka"kaima kasan bazan iya marinka ba, amman nima kabani waya na kira mama ta saimin tukunya sabida adaina min gori" tsananin tausayin maganarta yaji har ransa.
"Ummi nine mamanki nine abbanki nine yayanki nine ƙaninki sabida haka komai kikeso zanyi miki indai kicin ne da kayan kicin duk zan miki kinji kanwata".
YafaÉ—a yana mai É—agota hanyar waje suka nufa a falo suka tarar da dija tana faman kai komo.
"Dija zauna xamuyi magana"
YafaÉ—a fuskarshi babu sukuni, zama tayi a gefen kujera inda ya zaunar da bebi a kusa dashi.
"Ummi ki faÉ—i abinda ya faru a tsakaninku keda dija har kika É—auki hannu kika mareta?".
Batare da tsoro ko fargaba ba bebi ta mayar mai da duk yadda akai sannan ta É—ora da cewa........
"In kuma karya nake aje a duba kicin akwai tukunyar dana É—ora akan gas É—in".
"Ke dija mai yasa kikai mata haka? bayan kinsan komai na gidan nan mallakina ne haka zalika mallakin dukkan matar dana aurone? mai yasa kina babba bazaki assasa zaman lafiya agidan nan ba?"
Sosai yake mata faÉ—a wanda seda ta raina kanta.
Sannan ya juya ga Bebi itama yahau yi mata nata faÉ—an, akan me zata mari dija mai yasa bazata bari ya dawo ta gaya masa ba? daga karshe ya É—ora da cewa.
"Dukkan ku kunyi kuskure amman ninafi ku yi domin ban tsaya naji ba'asin komi ba na É—auki hukunci dakaina, sabida haka ina son daga yau kada wadda ta kuma tayar min da husuma ke anjima zan saka a gyara wancan extra room É—in a maida miki dashi kicin É—inki and store anan zakina girkin ki dan Allah ina son ku haÉ—e min kanku bana son tashin hankalinku pls".
YafaÉ—a yana mikewa ya nufi dakinshi shirin office yayi ya fito anan ya sami dija itako Bebi tana É—akinta tana baccin daya zame mata jiki.
Sallama yay mata ya wuce.
Acikin satin kullum Aliyu yana like da bebi kamar cimgam yasa an gyara mata kicin É—in dayace sabida haka yanzu babu zancen shiga kicin É—in dija.
Kowa girkinshi yakeyi.
Seda tai sati guda sannan aka raba girki inda in yay kwana biyu a É—akinta zeje na khadija yay biyu dayake ma shi baya bin É—aki sedai kowacce ranar girkinta taje gareshi.
Zaman gidan Aliyu ya koma kamar gasa domin ko wacce ta mike sotake taga ta ƙwaci kambun so wurin mijinta musamman a yanzu dayake kokarin nuna adalci a tsakaninsu domin duk son dayakewa Bebi baya yarda ya tauyewa dija hakkinta babu ta inba baya kyautata mata amman ita a nata ɓangaren kullum korafinta yaki yay mata ciki.
Kwanan Bebi goma agidan ta saba da mutanan gidan domin sun ƙulle ita da zee matar usman haka nan sunyi sabo dasu amina domin kusan kullum tana wajan ammi tana koyon girke girke wajanta awajan su amina ko ta iya gayu ta ƙara koyar abubuwa na kwalliya haka nan zee matar usman ita take bata kayan gyara namu na mata da abubuwan rikita oga, Alhaji babba kuwa kusan duk girkin dazatai seta zuba takai masa wanda hakan yasa yaji yana mata wani irin so wanda ko ganinta in bai ba seyayta cewa hajiya matarsa ina ƴar albarkata yau ban ganta ba.
Lokacin bikinsu hassana yayi wanda yazo kusan ɗaya dana ƙannenshi komai na hidimar da uba kewa ƴaƴa Aliyu yay musu amman abin takaici bai gayawa Bebi ko bikin ba har akai bikin aka gama bebi bata saniba.
Haka nan aka faÉ—a bikin amina dana su hassana wanda a daran da za,ai mothers event ammi ta mikawa Bebi nata lefen da basuyi mata ba, akwatina ne saiti biyu haka ma dija akai mata na faÉ—ar kishiya sosai Bebi tai murna.
Tare da zee suka É—auke kayan sukai part É—inta dashi, abin takaici duk hidimar da akai Aliyu ya hanata ko leke wai acewarsa kada ta wahalar mai da bebinsa haka ze sakata a daki yayta faman abu É—aya.
Har akai biki aka gama Æ´an uwa na nesa dana kusa suka tafi a wannan bikin Bebi taga nusaiba mai kama da Aliyu sak sannan suka gaisa da ya umar sabida ba'ai taro a sunan zee ba yasa basu zoba.
Tunda anty ruma tazo biki taga bebi da ciki take faman zuga khadija akan damme ita tana zaune wata zatazo ta rigata haihuwa agidan, to hakance ta saka dija tai muguwar sauyawa Aliyu komi yace mata setace bazatai ba rashin kirki kala kala take masa abin da yasa yake rabuwa da ita sabida kar ace dan yay aurene ze wulakanta tata.
BAYAN WATA BIYAR
Lokacin cikin Bebi yana wata shida sosai yay wata irin girman dayake bawa kowa tsoro alokacin ta kafa mashi rigimar seya kaita wajan mama, seda ammi tasa baki sannan ta haƙura da maganar, lokacin ma yawanci tafi zaman wajan ammi domin shi baya samun zama sabida ya riga ya bude kamfaninshi na TOKARAWA wanda tuni har an soma aiki acikinshi wanda ya ɗora goma da baban nazir a matsayin manajojinshi,wannan dalilin yasa bai fiye samun zama ba.
Matar goma ma tazo mata kusan ma tana yawan zuwa sabida tana mata kitso da kunshi, cikin wannan lokacin ne Allah yaywa Alhaji babba rasuwa mutuwar data girgiza ilahirin zuri'ar mai atamfa sosai Bebi ta dinga kuka! ranar uku mama tazo gidan tare dasu hassana da iya da sadiya da baba matar malam da wasu mata da bebi bata sansu ba, a part É—in ammi suka zauna lokacin da bebi taga mama kuka ta saka mata sedai abinda ya bata mamaki sauyin dataga kowa yayi hatta su hassana sunyi wani irin kyau seda ammi ta basu wuri sannan mama take bata labarin duk abubuwan dasuka faru, awajan gaya mata bikinsu hassana ne tahau kukan mai yasa ba,a gaya mata ba dariya mama tai tare da ce mata ai mijinta ne yace kada agaya mata ga sadiya nan ma bikinta sauran wata É—aya, sosai Bebi take dariya ganin yadda su hassana sukai wata kiba wadda kallo É—aya xakai musu kasan sunada shigar ciki.
Shahid ta tambaya wanda mama tace mata ai yana ta zuwa aikinshi wajan Aliyu yana kuma zuwa makaranta, sosai bebi take mamakin zurfin cikinsa ko kaÉ—an bai taba gaya mata dukkan waÉ—annan lamura ba.
Bata tsinke da lamarin bama seda mama take bata labarin case É—in khalifa da rasuwar mahaifinshi dakuma belinshi da Aliyu ya karbo sabida tausayin daya basa, yanzu haka wai khalifa ya shiryu daman can babansa ke É—aure masa gindin rashin mutunci.
Kuma yanxu haka an mayar da auren shi da ladi tunda daman saki biyu yay mata kuma Aliyu ya É—aukeshi aiki a kamfaninshi haka nan ta zayyane mata zancen shirinsu da dangin mahaifinsu tare da gabatar mata da waÉ—annan matan inna suwaiba kanwar abbansu dakuma matan su kawu tasi'u sosai bebi ta sake dasu tana kuma gaisarsu domin tasan baka mayar da sharri ga duk wanda yay maka shi kuma nagaba ai yayi gaba na baya se labari.
Mama ta kara mata da nasiha.
"Dan Allah bebi ki rufa mana asiri ki zauna lafiya agidan ki duk da naga sauyi sosai atare dake kuma ki kara yi masa godiya bakiga gidanmu ba yanzufa sekin ɓata in kikazo gaskiya Allah ya sakawa da wannan yaron da alkairinshi amin"
Sosai jikin bebi yakuma yin sanyi takuma jin kaunar Aliyu har ranta wanda yazama HASKE gareta yazama HASKE ga ahalinta bata da abinda zata ce masa sedai fatan addu'a da kuma fatan nasara arayuwarsu.
Har dare su mama suna gidan sosai ta sake dasu hassana sunata hirarsu,anan taji labarin tafiyar hussaina abuja sabida transper da ya nura ya samu zuwa babbar kotun kasa dake birnin taraiya.
Har kuka bebi tai dataji irin dadin da ƴan uwanta da mahaifiyarta suke ji lallai rayuwa babu tabbas kuma dukkan tsanani yana tare da sauƙi komai nisan jifa dole ƙasa ze sauka ada sun taso a kunci amman da sannu komai ya koma tarihi.
Yanzu mama bata da wata matsala su ihsan ma suna ta makarantar su batare da wata matsala ba.
Da kansa ya zuba su mama a motarshi ya kaisu gida wanda tun a mota suka tsinke da daular da sukaga Bebi acikinta lallai Bebi ta taka ƙasa ta shiga jerin manyan mata, washe garima sega wata tawagar nan daga wajansu kawu tasi'u domin ilahirin zuri'arsu seda sukazo gaisuwa harda khalifa da ladi wanda seda ya saka aka kira mai bebi yayta mata godiya har yana ce mata ba daban Aliyu ba da sun shiga taskun rayuwa sabida bashin bankin da mahaifinshi yaci wanda hatta gidansu seda aka ɗaga aka siyar duk yana gidan yari bai saniba rayuwa taiwa mahaifiyarshi da kannenshi zafi cikin hukuncin Allah da taimakon Aliyu ya sai musu gida yay belinsa harya samu ya ɗaukeshi aiki har zuwa yanzu da komai yake warware musu,yanzu haka suna zaune gida ɗayane shida mahaifiyarshi da kannenshi da ladi matarsa inda shi kuma yake zuwa tokarawa aiki a karkashin kamfanin Aliyun.
Haka nan su kawu tasi'u suka hau neman afuwarta tare dayi mata godiya akan hidimar mijinta garesu abin har kunya ya bata haka dai aka rabu cikin jin dadi da farin ciki.
Har tsayin kwanaki bakwai ana faman karbar gaisuwa acikin gidan wanda Æ´an uwan bebi sukai mata kara wajan zuwa kullum kuma da kular abinci abin mamaki kuma arana mutum kusan goma ke zuwa.
Ranar da akai bakwai da yamma shahid shima yazo sabida suna exams bai sami damar zuwa ba sosai bebi tai mamakin yadda shahid ya zama magidanci yay wani irin girma da kyau, a falonta suka zauna suna hira duk farin ciki ya cika Bebi se wajan magariba ya tafi washe garima sega hassana hussaina ihsan da arfa anan suka wuni ihsan an zama Æ´an mata se wani iyayi take wai ita likita zata karanta ita tai musu girki.
Ran bebi wasai gata cikin Æ´an uwanta nanfa hira ta kaure musu koda Aliyu ya dawo daga office shiya É—aukesu ya kaisu gida ya haÉ—asu da shatara ta arzki.
Adaren ranar Bebi taci adonta na bam mamaki daman ranar ita ce dashi soyayya mai tsayawa arai ta nuna masa tana mai kuka akan abinda yaywa danginta daga karshe tace.
"Tabbas kacika masoyi na hakika Allah ya bani ikon faranta ranka"
"Karki damu mai sona komai nai maki ban faÉ—iba"
YafaÉ—a yana haÉ—e jikinsu wuri guda aranar sunyi soyayya mai narkar da zuciya.
Tsayin kwanaki ana amsar gaisuwar alhaji babba har zuwa sanda komi ya lafa rasuwar ta xama tarihi.
Cikin wannan lokaci cikin bebi ya shiga wata na bakwai.
Alokacin kuma Allah yaywa malam shima rasuwa sakamakon mura dayay fama da ita wannan karon seda Aliyu ya kai bebi gida.
Anan gidan malam akaita amsar gaisuwa ammi tazo abba yazo da sauran Æ´an uwanshi.
Ranar bakwai da yamma bebi ta koma gidansu sosai tai mamakin yadda aka ƙere musu gidan nasu abin yay matukar burgeta adaren ranar Aliyu yazo suka wuce gida.
Abin mamaki kaca kaca suka tarar da falon kamar anyi barin kayan falon wucewa É—aki bebi tayi Aliyu kuma ya wuce É—akin dija, tarar da komi yay a watse kanshi tsaye sauka yayi kasa ya wuce part É—in ummnta anan ya tarar da ita a zaune tana kuka umman ta na bata baki.
Tambayar mai yake damunta yaywa umma, amma ga mamakinsa se umma tahau tijara tana aibatashi sosai ransa ya ɓaci amman seya mike baice mata komiba ya wuce wajan abba anan yake masa bayani cewar ya dawo baiga khadija ba ya bita part ɗinsu ummanta tai masa rashin kirki.
Abbane yasa aka kira abban bauchi tare da umman khadija da ammi koda sukazo abban bauchi ya tambayi khadija shin Aliyu yana mata wani abunne.
BuÉ—ar bakinta tace.
Ba rashin ci bana sha ita dai haihuwa takeso.
Kallonta abba yayi.
"khadija aure da haihuwa da mutuwa lokacine na Allah sabida haka ki kwantar da hankalinki in Allah ya yarda kema zaki haihu"
Amman ga mamakinsu se umman tace.
"Kaga ya idriss nagaji ya sakarmin ƴata kawai ai wadda yake so yaywa ciki amman ita gata har yau ko ɓatan wata"
Kunyace ta kama Aliyu ya sada kansa a ƙasa baice komiba.
"Abba nidai ya sakeni kawai bana bukatar xamana dashi"
"To kai Aliyu kanaji fa"
Cikin kwantar da murya yace.
"Khadija kiyi hakuri har yau aurenmu bai shekaraba kema zaki haihu insha Allahu"
Duk yadda abba yaso su fuskanci komai amman sunki hakan yasa abban bauchi ya fusata.
"wato ke khadija daman ba domin Allah kike son baba Ali ba? in bada wata manufa kike sonshiba tayaya zaki nuna ke haihuwa kike so in sonki domin Allah ne ai bazaki dage sekin haihuba wannan maganar banza ce kai baba ali saketa nace ai ba tare kukazo duniya ba Allah ya gani baka shiga hakkinta ba"
Atake anan Aliyu yay mata saki É—aya wai kuma seta saka kuka abban bauchi tsaki yay yabar wajan shima Aliyun tashi yay duk baiji dadi ba haka yabar falon.
Koda ya koma bai gayawa bebi ba haka yasa aka gyara falon kamar da sukaci gaba da zamansu seda ta matsa masa da tambaya sannan ya zauna yay mata bayanin komi.
Har ranta bataji dadi ba amman addu'ar alkairi taiwa dijan sannan ta cigaba da harkokinta.
Soyayya mai kyau suke gudanarwa ita dashi lokacin da watan azumi yazo cikinta ya shiga wata na tara gashi zasu tafi umara shida ammi da usman harda mamanta, hakan yasa baba matar malam tazo suka zauna tare, tunda ya tafi kullum addu'arshi akan Allah ya raba bebi da cikin jikinta lafiya take.
Ranar sallah suka dawo da asuba kuma aranar nakuda ta kama bebi wadda bata wani sha wuyaba Allah ya sauketa lafiya a part É—in ammi.
Ta haifo É—anta namiji mai kama da Aliyu sak sedai farar fatar bebi daya É—auko, zokuga farin ciki wajanshi kamar ze mayar da É—an nan ciki gyarata akai kana aka wuce da ita part É—inta anan baba tacigaba da kula da ita.
Ranar suna yaro yaci suna Musa sunan babansu bebi sosai akai shagali a wannan rana kamar babu gobe.
Washe garin sunan dija tazo ganin yaron harda ummanta cikin mutunci suka gaisa sun jima anan kafin sutafi.
Haka baba tacigaba da kula da bebi da sahib,har tsayin kwanaki arba'in ranar kwana na arba'in da biyar bebi ta tafi gida bayan sun aje baba agidanta sun cika ta da kayan abin arziki.
Kwanan bebi biyar a wajan mama ta zaga dangi taje gidan hassana husaina tana abuja taje gidan sadiya taje gidan iya ta zaga ko ina har gidan ladi taje anan ta wunima washe gari a gidan kakan ninta na ƴan kusa ta wuni gidansu kawu tasi'u kenan wanda aka gyara gidan yazama na zamani sabida yanzu haka duk samarin gidan suna aikine a kamfanin Aliyu sosai taga gata dangin mama ma na nan ɗin ta kai musu ziyara sabida daman su tun fil azal basu wulakanta suba kuma suma sun mata godiyar hidimar da mama ke musu domin duk abinda mama ta samu bata taɓa mantawa da danginta ba suma tana musu yadda ya kamata.
Bata dawo gidaba se dare ita da ihsan duk sun gaji basu sami mama agida ba tana wajan kayanta dasuka zo sabida mama mai neman na kanta ce wannan dalilin yasa bata rabu da Æ´an buga bugarta ba yanxu haka shinkafa ake kawo mata Æ´ar hausa take rabawa mata masu abinci da masu awo a wata su haÉ—a mata kudinta, sannan tana saida kayan yaji agidanta.
Bayan mama ta dawo zagewa tai tasoma gyara bebi ciki da waje na tsayin kwanaki biyu hatta fatar bebi seda ta sauya, tunda yazo É—aukarta yake É—aukinta dan haka koda suka koma gida sahib wajan ammi aka barsa ya dauketa se master room.
Sosai ya gigice ya susuce akanta ya shiga rudu wanda harda yi mata kyautar kujerar hajji a wannan rana sabida yajita xam zam kamar bata haihuba.
BAYAN SHEKARU BIYAR.
Abubuwa masu dadi da rashin daÉ—i sun faru.
Rasuwar abban Aliyu data girgiza kowa rasuwar kawu tasi'u da kawu sani rasuwa baba matar malam.WaÉ—annan sune abubuwa marasa dadi dasuka faru domin zaman duniya daman akwai dadi ne akwai rashinsa

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.