Romantic Hausa Novels

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 59 of 81

Yana gama faÉ—in hakan yaja hannun malam suka bar wajan.
Cikin sauri wannan mutumin ya lalubo lambar wayar Alhaji idiris ya soma kira amsar ɗayace wayar tana kashe dafe kanshi yayi tare da kiran md ɗin abba nacan abuja shima wayarshi akashe take bashida number kowa a ƴaƴan abba kuma sunɗan jima basu haɗuba dan haka yaja tsuka tare da kallon alhaji mai gwall wanda ranshi yay ƙololuwar ɓaci.
"Yallaɓai wannan magana fa zata iya xama gaske kasan alhaji idi akwai tausayi a shawarce kawai a janye wannan magana sabida kaima sanin kanka ɗan alhaji idi kaɗai baka isa kaja dashi ba bare kuma shiɗin kansa dan haka kasan yadda zakai da lamarin nan danni tunda naji an ambaci mai atamfa jikina yay sanyi alhaji".
Cikin tsabar takaicin yadda aka kunyatashi ya juyo ga wannan mutumin.
"Wato alhaji isyaku na rantse da Allah bantaɓa jin takaici irin wannnan ba tabbas wannan bawan Allah ya yaudaren sabida tsabar son abin duniyarsa inaga yaje ya bawa mai atamfa yarinyar sabida yafini kuɗi".
Cikin lokaci kaÉ—an magana tacika unguwa tuni mutane sukaita darewa suna watsewa.
Ƴan tsiraru suka rage se khaleepha dake faman danna ashar kamar ze doki kawu tasi'u.
Cikin zafin zuciya alhaji mai gwall ya dubi tasi'u wanda gumi ke faman keto masa kamar an masa wanka da ruwan É—umi.
"Wallahi bakaci banza ba kai gaba ɗayanku ma zakusan kunyi dani sabida haka ina son ka tattaron komai nawa daka san kaci hatta lefene na jiya da aka kawo ka mikomin sannan zan dokaku ƙara a kotu wallahi bazan yarda ba".
Cikin sauri Rabi'u ya riƙe babbar rigar alhaji mai gwall yana masa magiya.
"Tabbas munsan mun tozartaka alhaji agaban mutananka ƴan uwanka abokanka dan Allah kai haƙuri muma bamu san da wannan magaba seda mukazo amman acikin ƴaƴan tasi'u akwai manyan ƴammata da basuyi aure ba meze hana a bashi ɗaya tunda duk suna nan gundum gundum babu aure dan Allah ka duba lamarin".
Cikin firgicin maganar Rabi'u Tasi'un ya rarrafo.
"Kaimin rai alhaji kada ka haɗa auren ƴata mai mutuncin da wancan......seyay shuru sabida ya tuna katoɓarar dazeyi.
Murmushi Alhaji mai gwall yay.
"Oh wato duk abinda nake maka kallona kake shasha wato ɗan nawane ɗan iska malam liman dawo ga sabon ɗaurin aure nan wallahi seka ɗaura auren ƴarka da khaleepha ka zaɓi ɗaya kokuma na makaka a kotu ka biyani duk abinda kaci'.
Wannan shine ga ƙoshi ga kwanan yuwan mugunta fitsarin faƙo inji bahaushe kawu tasi'u yayi gudun gara ya tarar da zago domin bashida kuɗin biyan alhaji kuma baya son ƴarsa ta faɗa hannun khaleepha sabida yafi kowa sanin illar yaron.
Yanaji yana kuma gani shedu suka shaida ɗaurin auren ƴarsa ladi da khaleepha a kuma ƙofar gidansu Bebi wanda kafin ma a gama ɗaurin auren zuciyar kawu tasi'u tai wani irin zafi kansa ya ɗau ciwo ana gama ɗaura auren yana zube a wajan sumamme
Cikin ko in kula alhaji mai gwall ya tsallakeshi ya wuce yana bada order aje can gidan tasi'un a É—auko musu amarya sesu Rabi'une suka tarairayeshi suka É—auko É—an sahu suka sakashi aciki sukai gida cike da mutuwar jiki.
*Koba ba'a mutuba tofa akwai hisabi tun a duniya wanda yake aikata ba dai daiba yana da kyau ya gyara tun aduniya kafin ya rasu sabida ita duniya darasi gareta wannan ya kasance iznah ga masu hali irin na su kawu tasi'u tabbas wanda Allah ya kare babu wanda ya isa ya cutar kazama mai sanya Allah cikin lamuranka domin shine maji roƙo mai ƙarfin mulkin da babu irinshi ko alhaji mai gwall bai shari'a dasu tasi'u ba wannan haɗin auren da ƴar tasi'u kaɗai ya isa yazama darasi garesu duk yadda tasi'u yay gudun yarsa ga wannan aure seda ya faru ta hanya mai sauki wadda da yay niyyar cutar da marainiyar Allah ne lallai Allah mai ikone mabuwayine kuma mamallakin komai da kowa tabbas shi alkairi ɗanƙone hakannan sharri ɗan aikene babu wanda ze alkairi ya tafi a banza babu kuma wanda ze sharri ya xauna lafiya dukkanin waɗannan biyun kana girbansune ko a duniya ko a lahira Allah kasa mudace amin*!
Cikin lokaci kaÉ—an labarin wannan lamari ya cika anguwa motoci kimanin guda uku alhaji mai gwall ya tura can gidansu tasi'un wanda sam matansu basuda masaniyar hakan se ganin motoci sukai a kofar gidansu.............
# *Autar Manya*
11/14/21, 3:13 PM - Allah Akbar: *PART* 2

NAKUÆŠINE

                                *80*

Abakin ƙofar gidansu kawu tasi'u motocin suka dakata cikin sauri drivern alhaji mai gwall wanda daman shi tuni yasan gidan sabida dashi aka kawo lefe sannan kuma shi alhaji mai gwall ya turo suzo su ɗauki amarya ya buɗe marufin motar daya tuƙo tare da fitowa daga cikinta ya nufi kofar gidan tare da bubbuga ƙofa yana maka sallama.
              Cikin tsananin mamaki matar kawu Rabi'u ta turo yaronta ya duba mai doka musu ƙofarsu sabida sune a sashen farkon gidan shiyasa komai akai a ƙofar gida suke faraji.
Yaron ne ya dawo mata da cewa wai ga baƙi nan zasu ɗauki amarya, Cikin tsananin mamaki tai ɗan ƙuri da idanu alamun tana tunanin wani abu kafin ta miƙe ta shiga cikin gida tana maka buɗa.
                 "Ayyiri!yiri!! matan gida ku fito anfa ɗaura munci lefe kunga ƴan wahala sun tawo mana nan ɗaukar amarya muda inzasu kashemu bamusan kalar amaryar ba kai maza ɗalha jekace musu babu amarya anan tana can gidan tsohuwarta koya kukace jama'a?".
Cikin sauri tare da zafin zalama babar ladi matar kawu tasi'u ta tashi tsaye wadda zaninta har kuncewa yake sabida garin sauri ta tsaida É—alhatu tare da kallon sauran matan.
            "Yaya zakuce haka bayan kuka sani koda uban angon akazo yanzu dan Allah idan muka leƙa da kammu kukasan garar daza'a ƙara ninko mana kai ɗalhatu zauna ni bara na leƙa kuma kada wadda taganni da ƴan canjina tace na ƴammata".
TafaÉ—a tana yayar zani akan igiya ta yafa a saman ka kamar tsohuwar mahaukaciya haka ta danna kanta waje matar kawu sani tana take mata baya.
             Wajan drivern Alhaji mai gwall ta ƙarasa tana wani rawar jiki kamar sabuwar kamun hauka.
"Ranka shi daÉ—e ai banan bane gidansu yarinyar amman in bazaku ganeba koni kuka biya aisena rakaku".
Tafaɗa cikin zaro idanu tana kallon dalla dallan motocin dake fake a ƙofar gidan nasu aranta take ayyana wannan aure akwai kyawun maciji bada ban hatsarin wannan yaroba ai damu zamu danna kai koda tsiya koda tsiya-tsiya semun shiga amman wannan ɗa tunda naga malam yay gudun haɗa iri dashi tabbas na shaida baƙaramin *Tantiri bane ba waɗanda basa jin magana ko guda*!
                       Maganar drivern alhaji mai gwall ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin data faɗa"Hajiya ai nan gidan aka turomun koba nan ƴar gidan malam tasi'u take ba naji ance ko maryam amman dai ladi naji ance ai da ita aka ɗaura *auren* " yafaɗa cikin tabbatuwa da maganar daya faɗi ɗin.
Zanin datake riƙewa shiya sunce cikin tsananin tsoro ta dubeshi.
     "Kai sokon ƙauye dakata babu wata ladi da aka ɗaurawa aure da watsats tsan ɗanku sedai ko balki kuje can ku ƙarata".
TafaÉ—a cike tsoron gudun kada wannan lamarin ya tabbatu,Murmushi drivern ya saki tare da kallon sauran na cikin motar waÉ—anda suke yaran alhaji yanawa É—aya daga ciki magana.
"Eh tabbas da ladi aka É—aura aure bada balkiba sakamakon yadda mijinki yay munafurci wa alhaji shiyasa É—aurin auren ya koma kan É—iyarki ita waccan ai tun jiya tana gidan nata mijin".
        Cewar wani ɗan siririn mutum ɗaya daga cikin yaran alhajin daya turo yake shaidawa babar ladi haka, wata zabura tai mai kama data mahaukata tare da faɗuwa ƙasa daɓas kamar zautacciya.
"wallahi baku isaba babu shegen daya isa ya tafarmin da Æ´ata wallahi bazan bawa waccan É—an iskan yaro Æ´ataba sedai duk abinda za'ai ayi yau É—innan amman ni wallahi bazan bada Æ´ata ba"
Tafaɗi maganar tana kurma ihun daya jawo hankalin sauran matan gidan dukansu suka fito kowa yana tambayar ba'asin meke faruwa drivern Alhaji mai gwall ne ya dubi matan wajan waɗanda suke tambayar ba'asi cikin nutsuwa ya wassafa musu dukkan abinda ya faru a wajan ɗaurin aure daga ƙarshe ya ƙarasa da cewar dan Allah suyi sauri su kawo masa amarya suna ɓata masa lokaci Alhaji yanata waya.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.