Romantic Hausa Novels

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 52 of 81

Tofa akwai ƙura agaba
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *PART* 2

NAKUÆŠINE

                          *72*

Har mama ta kammala maganarta kansa yana sunkuye babu abinda ke É—iga daga saman goshinsa face gumi wanda yake faman gudu kamar famfo idanunshi ya kaÉ—a yayi jajur jijiyar dake saman kanshi ta tashi tai wani irin firfitowa tai ruÉ—u-ruÉ—u.
Iya ƙololuwar tashin hankali ya shigeshi a wannan lokaci wannan shi ake kira ga ƙoshi ga kwanan yunwa m'ana shine.
Da farko ganin girma da darajar waɗannan bayin ALLAH na gabanshi bayajin ze iya mayar da kyautar da suka bashi wadda tun kafin su sanshi su san asalinshi suka ɗauki ƴa guda suka bashi wannan karamcin da sukai masa tabbas, baici ace ya watsa masu ƙasa a idanunsu ba.
Abu na biyu kuma shine, usman dayay mashi shigar sauri tabbas inda yanada dama a yanzu wadda ta wuce kunyar waÉ—annan bayin Allah nagabanshi dase yayiwa usman bazata domin bafa ze amshi auren ba sedai shi yasan yadda zeyi da ita sedai kuma tsananin kunyar waÉ—annan mutane na gabanshi yasa bayajin ze iya mayar da kyautar da ALLLAH ya bashi domin bai san ribar dazeci gaba ba.
Abu nagaba fargabar mahaifanshi musamman abba wanda baya kauce maganar alhaji babba, yasan a wannan karon zasu ɓata da abbanshi abinda bayaso kenan arayuwa yana mugun son mahaifanshi baya son ganin ɓacin ransu musamman akanshi.
Yasan abba ze masa faɗa ze fushi dashi a familynsu za,ayi rikici da gutsiri tsoma musamman akan yadda yaywa dija kishiya a kwana uku da aure yasan ko abbanshi ma zece dan yaga dija marainiyace yasa yay mata hakan, sannan kuma daɗin tashin hankalin ta yaya zewa abba bayanin ya nemi aure batare daya sanar masa ba? batare daya sanarwa da kowa ba? yasan abba baze karɓi uzirin cewa usman shiya amsar masa auren ba tabbas laifin akanshi abba ze ɗora.
Wata zufar ya kuma sharcewa yana fidda huci sama-sama.
"Malam Aliyu bakace komiba muna jira daga bakinka ga dare yana kumayi?".
Cewar malam.
Maganar tsohonce ta katse shi, inda zasu lura dashi sanda ya É—ago zasuga yadda idanunshi ya kaÉ—a, duk da duhun tsakar gidan amman hasken farin wata yana haskasu.
Bai iya cewa komaiba sedai ilahirin maƙoshinsa ya bushe ƙamas domin babu alamun miyau acikin bakinshi.
"Malam inta shirya kawai zamu wuce da ita sabida dare yana yi".
Cewar usman cikin sauri.
Tayaya zasu bashi Æ´arsu babu É—an rakiya kamar yadda ake kai amarya a al'adance, babu kayan É—aki babu taron biki, sannan batare dasun haÉ—ata da kowa ba.
Yake faÉ—i cikin ranshi amman bara yaga gudun ruwansu.
"To usman Bebi fa kasan marainiyace ban sai mata komi na aure ba sabida bata isa ba, bayan haka ban sanar da wasu daga cikin Æ´an uwana ba bare arakata É—akinta, bakwa ganin hakan kamar ze xama ba dai dai ba garemu? bakwa ganin hakan kamar ze jawo mata raini wajan jama'ar gidanku, bawai ina nufin mahaifanku ba, nasan dai baza,a rasa jama'aba kunga za,a iya cewa kamar batada galihune yasa aka kawota haka".
"Mama karda ki damu ni usman nai maki alkawarin zanyiwa bebi komai wanda akewa amare insha Allahu mudai fatanmu kubamu bebi yau maganar yan zuwa ganinta kuma nida kaina zanzo na É—aukeku kuga É—akinta insha Allahu".
Saka mayafinta tai ta share fuskarta tana kallon yanayin Aliyu wanda jikinshi yayi sanyi ƙalau.
Ta cikin ƙwayar idanunshi yake kallon mama shima yana ayyana kardai matar nan kuka take? sekuma jikinshi ya kuma yin sanyi tausayin matar ya kamashi.
Can cikin ƙasan maƙoshinsa ya tattara dukkan kalamanshi da sukai saura.
Cikin gajiyawa da maganarsu yace.
"Hajiya ki daina kuka addu'a zaki mata akan Allah ya bata rinjaye akan komai, sannan ki mata fatan alkairi niba mutumin banza bane bawai yabon kaiba zan riƙe maki ita kamar ƙannena su hassana dan Allah hajiya ki daina kukan yana taɓamin zuciya senaga kamar kina tantama ne akammu, Kina zuwa unguwar yahya gusau ko yaro kika tambaya gidan Alhaji Idriss Mai atamfa!zai kaiki in kika tambayi Aliyu! kowa ya sanni nine ɗanshi na huɗu karki damu hajiya nagode da wannan karamcin naku nikuma Allah yasa kada na baku kunya amin".
Cikin tsananin mamaki usman ke kallonshi amman seya danne shima karba yay yana kuma yiwa mama bayani cikin kwantar da hankali.
Shima malam nasiha yakewa mama mai ratsa jiki.
"Haba Aishatu maye kuma na kukan! ai godiya xakiwa Allah daya kawoki wannan rana ba kuka ba haba aishatu addu,a xaki masu insha Allah komai ze tafi cikin farin ciki da albarka".
Share hawayen ta kumayi sannan ta É—ago tana kallon Aliyu still.
"Aliyu ina kuma damƙa maka amanar Bebi dan Allah ka kulamin da bebi ina son bebi ta shiga raina wallahi ba da ban waɗannan azzaluman dangin mahaifin nasuba, da babu abinda ze saka naiwa bebi aure yanzu sabida akwai tarin kuruciya da wauta atare da ita yana da kyau ta sami wayewa awasu abubuwan na aure waɗanda indai ba Allah ne ya baka hakuri da juriyaba bazaka iya da bebi ba, dan Allah kai hakuri da duk abinda zatai maka in na faɗane kai mata in bakaji daɗin abinba kaɗau mataki ko ka gayamin wallahi har nan zanzo na zaneta".
Ta ƙarasa faɗi tana hawaye sannan ta miƙe zuwa ɗaki batare data tsaya jin mi zece ba.
Kanshi dake barazanar tarwatse mashi ya dafe yana ayyana inda shima ze sami damar kukan dayi zeyi! kodan ya sami salama acikin zuciyarsa yana ganin ita mama kukanta na daÉ—ine tunda gidan miji xata kai Æ´arta shiko.kalaman daze fuskanci mahaifanshi kaÉ—ai yake haÉ—awa dan yadda mama ta bashi tausayi ta kuma kashe masa jiki bayajin ko ana muzuru ana shawo ze iya sakar mata Æ´arta domin yasan tabbas alhaji babba ze iya cewa ya saketa É—in.
"Kaga halin mata ko Malam Aliyu wai yanzu aishatu daya dace ta rarrashi Æ´arta amman ita take wannan kukan kumafa É—azu da baku zoba bakaga yadda ta É—aga hankalinta ba gani take kamar za,a shanya mata Æ´ane amman yanzu kunga kuma seda kuka zo É—in xata hau kuka oh Allah kyautawa mata".
Murmushi usman yay sannan yace.
"Malam kasan ɗa da mahaifi se Allah musamman bebi abarson kowa yarinyar tana da shiga zuciyar mutum nima haka kawai nakejinta kamar ƙanwata ta jini".
YafaÉ—a yana kallon Aliyu wanda ya sunkuyar dakai amman aranshi cewa yake.
kasan da haka mai yasa baka kwasaba seni zaka ƙaƙa bawa ita.
Amman a zahiri baice komai ba seyay kamar ma bayajin me suke faÉ—i É—in.

Lokacin da mama ta shiga ɗaki duk ƴaƴan nata sunyi barci se redio dake famanyi Bebi tana daga saitin siff ta makure waje ɗaya ta cure da hijabi kamar maijin sanyi, kallon tausayi dana bankwana mama tai mata sannan ta sunkuya tana tashinta a hankali tana share hawayen dake zubo mata dayake bata fiye magagi ba caraf ta miƙe tana kallon mama.
"Fita tsakar gida jirani".
maman ta gaya mata a hankali gudun kar sauran su farka su haÉ—u su saka mata kuka!.
Ba musu ta murje idanunta tare da bin umarnin mama, ita kuma maman ta É—auko jakar kayan bebi data haÉ—a mata ta biyo bayanta.
Tana rabe a bakin kofa taji takun mama a bayanta.
da sauri ta fito tsakar gidan baki ɗaya ganin malam a xaune da baƙi yasa taja da baya tare da rissunawa tana gaisar da malam.
Se lokacin ta shaida su waye, gabanta ne ya faÉ—i!
amman sanin babu angon nata cikinsu yasa ta soma mamakin miya kawosu da wannan daren amman setai gumm, da bakinta seda mama tace mata.
"bakiga baƙi bane ba bebi?".
"Ya usman ina yini" tana faÉ—in haka taja bakinta tai gumm gabanta yana faÉ—uwa.
"Shifa É—ayan baki sanshi ba koko bazaki gaisarshi ba?"
"An wuni lafiya" tafaÉ—a tana turo baki gaba usman ne ya amsa a sake shiko gogan takaicine ya dirar masa yana ayyana xakici ubankine.
"To usman ga amanar bebi nan ga kuma kayanta"
"Ke bebi ka Aliyu nan ɗan uwan usman kuma mijinki banson shirme da sakarci kinji ko ki.masa biyayya banda ƙazanta banda rashin kunya ragowar bayani xan turo hassana ko hussaina Allah yay maki albarka yasa nan gidan zamankine amin".
Malam ma fatan alkairi yay mata kana yaywa mama sallama ya tafi sabida dare yayi.
Shiko usman kayan bebi da mama ta kawo ya É—auka yabi malam waje.
Mama kuwa cikin sauri tayi cikin É—akinta sabida batason ganin fitar bebi.
ita ko bebi ganin mama tayi É—aki yasa itama ta dawo daga hutun wucin gadin data tafi domin komai nata ya tsaya cak.
Dama shine angon nata? mutumin dayake mata faɗa yake kokarin dukanta mutum mai zafin rai,tunda take bata taɓa ganin mutum mai ɗaure fuska irinshi ba itafa inta ganshi faɗuwar gaba da tsoro har kusan fitsari suke sakata tayaya xata xauna da mutumin da tsayinshi ma kaɗai cika mata waje yake.
Kuka! ne mai ƙarfi ya taho mata cikin firgici tsoro zulumi take kokarin fito da kukan.
Sedai jin tattausan hannunshi mai ƙamshi datai a..................

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.