Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 3 of 81
*AUTAR MANYA*👉👈
11/14/21, 3:05 PM - Allah Akbar: I just published "PART 3" of my story "AUREN BARE". https://www.wattpad.com/1108841932?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=autarmanya&wp_originator=bsm2ItCjiW55lJsHzofKCWd8CydFozsfYKQa7U9xGL1jQ%2FhrrdK5oQwC4rs2G7%2BoX4QJAH5q707c64tTT%2FmpkbNfQ2wSnU4X6BxVTXhnlwp%2BWq%2FYvdr1K7g%2BWUDCRuMu
*AUREN BARE !!*🌹
  { _HOT LOVE_ }
     Â
     NA
*AUTAR MANYA*
_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._
               *003*
Bebi ta faÉ—i maganar tana share hawayen dayake faman zubo mata kamar famfo.
Miƙewa tayi daga kan katifar datake kai tare da cire hijabin jikinta, ta ajeshi a waje guda, fita tayi tsakar gida lokacin anata faman doka kiran sallar magariba sakamakon lokacin yayi.
Mama tana kan kujera Æ´ar tsugunno tana kwashe tuwo tana mulmulashi cikin farar leda tana kuma ajeshi acikin robar da ake fita da ita tallan tuwon.
Su hussaina suna kan tabarma suna buɗe mata ledojin ita kuma ihsan tana miƙa mata,arfa kuma tana bakin rariya tana kuma wanke ƴan kwanikan da suka ɓaci.
Wucewa tayi gaban rijiya ta zira guga ta É—ebo ruwa ta zuba a buta, sannan ta shige cikin banÉ—aki ta kama ruwa.
Fitowa tayi tare da ɗaura alwala hakan nan ta kuma wucewa ɗaki, zama tayi a bakin katifa tare da ɗaukar carbi azkar ɗin data haddace da kanta, ta soma gabatarwa, tana idarwa ana tayar da sallah a masallacin cikin unguwarsu, wanda ƙarar! lasafikar cikin masallacin har cikin gidansu, shinfiɗa darduma tayi a tsakar ɗakin ta soma tada sallar, cikin nutsuwa, bayan ta idar ta jima tana addu,a akan Allah ubangiji ya kawo musu ɗauki na alkairi, sannan ta shafa, tare da naɗe dardumar, duk abin Bebi bata yarda tai wasa da addininta wanda hakan ba komai yaja mata shiba face jajurcewar mama akan su.
Sam bata yarda É—anta yayi wasa da addini, haka zalika duk talaucin su bai saka mama ta hanasu zuwa makarantar islamiyya ba, domin yanzuma haka makarantar magariba zasu tafi, wanda tun waccan shekarar su hussaina suka sauke alqur'ani mai girma, haka zalika sun sauke littattafan addini da dama, sannan kuma suna zuwa makarantar hadda ranar asabar, yanzu haka itama bebin saukarsu ya rage wata uku ciff itada shahid, makarantar bokoce kawai, basu bata muhimmanci ba, sabida rashin kuÉ—i, yasa su hussaina tunda suka kamallama aji uku a jiniya basu cigaba ba.
Haka zalika shima shahid yanzu ake shirye shiryen biya masa ya zana neko, wadda rabin kuɗin nasa ne na gawayinsa itama bebin yanzu zata zana jarrabawar shiga aji huɗu ne asakandire.
Sedai kuma itama É—in ba cigaba zatai ba sabida rashin da suke ciki.
Buɗe sif ɗinsu ta kaya tayi, wani ruwan tokar hijabi ta ɗauko wanda yasha karin guga, turare ɗan shafa, ta buɗe a ƴar kwalbarsa, ta shafa kaɗan ajikinta.
Sannan ta zira hijabin, tare da rufe sif É—in.
Gaban inda suke rataye jakunku nan su ta nufa, wata Æ´ar jakar leda ta É—auko wadda alqur'aninta ke ciki, sannan ta fita tsakar gida, duk su mama suna sallah, lokacin.
ÆŠan dakatawa tayi tare da jingina a jikin bango, cikinta yana murÉ—awa tanaji wata iriyar yunwa wadda bata da misali.
Bayan sun sallame addu'a suka shafa sannan mama ta juyo tana kallonta.
"Mama natafi makaranta".
Da kallon mamaki, mama tabita jin yau Bebi za,atafi makaranta da wuri, wadda wataran seta haÉ—ata da duka sannan take tafiya É—in.
"To ki tsaya mana kici tuwon".
Mama ta faÉ—a. tana kallon Bebi É—in.
Kamar bazatayi magana ba sekuma ta tuɓe hijabin nata.
Tare da zama a gefen tabarma sannan tace.
"Mama azubo min wallahi yau malam Hadi yace zeyi dukan makara".
Cikin azama mama ta miƙe zuwa kicin suma ƴan biyu, haramar makarantar suka yi, babban kwano mama ta ɗauka tare da zubo musu wadataccen tuwon gari miyar kuka wadda tayi daɗi duk da lami ce.
A tsakiyar iyalan nata ta zauna tare da saka hannu cikinsu, suka zauna sunaci bayan kowannensu yayi Bisimillah.
Shima shahid wanda ya shigo gidan yanzu wanda da alamar ma daga masallaci yake.
Ƙofar kicin ɗin yaje ya ɗauko nasa tuwon a roba, tare da zama a gefe yanacin nasa, kuma duk cikinsu babu wanda yayi magana.
Hassana ita ta soma ta shi tare da furta.
"Alhamdulillahi, Allah nagode maka, Allah ka ƙara bamu na kullum, Allah ka ƙarawa mama buɗi tare da dukkan musulmi baki ɗaya Amin".
Sannan ta nufi bakin rariya ta wanko hannunta, jakarta ta É—auka.
"Mama natafi makaranta".
ÆŠan kallonta mama tayi tare da cewa.....
"Ai kya dai bari Æ´an uwan naki su gama kutafi tare ko?".
Batare data ce komai ba taja ta zauna tana jiransu su kammala É—in.
Kowa fa seda ya tashi ya wanko hannunsa amman banda Bebi wadda take faman zare idanunta waje alamun bata ƙoshi ba.
"Mama dan Allah muyi gaba kada a soma ƙari bamuje ba, itafa Bebi setai biye-biyen gidansu ƙawayenta, daganan kuma sunje sunyo tsokanar su sannan su tafi".
Maganar hussaina kenan wadda ta take tsaye tana saka takalminta a ƙafarta.
"Eh wallahi mudai gaba zamuyi".
Cewar ihsan mai bin Bebi.
"To dalla kutafin mana Allah yasa niba makauniya bace ba".
Cewar Bebi tana siÉ—e hannunta sannan ta dubi mama wadda bata ce komaiba tanajin diramar yaran nata.
"Mama a ƙaramin harga Allah ko babban hanjina baije ba".
TafaÉ—a tana karya kanta kamar wata abar tausayi.
"Dama haka kika iya shegiya mai cikin zani".
Cewar shahid wanda yake ƙoƙarin ɗora robar tuwan daze fita da ita a kansa.
"To kaikuma meya ruwanka dani ne kamar ansaka baki dashi".
Takai maganar tana zabga masa wata ƙatuwar harara kamar idanunta ze faɗo waje.
"Wallahi nidai karya ƴa zanyi abanza na watsar ko shara bata iya ba se aikin cin tsiya daga ci se bacci sekin fita tallah, kiyo tsokana babu abin da ta iya".
Yafaɗi maganar yana ficewa daga gidan kansa ɗauke da robar tuwon hannunsa riƙe da bokitin miya.
Wata gigitacciyar ƙara! bebi ta ƙwala wadda seda ta saka mama zabura, cikin masifar faɗanta ta soma magana.
"Wallahi zaka dawo ne wallahi bazan yarda ba, mama kina fa kallon abinda yace min na rantse bazan yarda ba".
Tafaɗa tana Cilla ƙafarta ƙasa kamar wata ƙaramar yarinya tana faman ihun da babu hawaye!.
Ganin zata ɓata musu lokaci ƴan biyu suka wuce makarantarsu.
Itama mama tashi tayi, zuwa kicin ta ƙaro mata tuwon tare da dire mata gabanta.
"Gashi nan idan kin gama ki wuce ki tafi makaranta, ai gaskiya ya faɗa wallahi Bebi bansan irinki ba, ko shara ta ƴa mace senai da gaske, haka kikaga ƴan uwanki sunayi, se aukin ci kamar gara,kullum cikin rainuwa kike idan zan cika miki roba da abinci sekin share sannan kizo kina baki ƙoshiba tallan nan bazaki mayar da hankali kiyiba.....................,
Aikin gida kina kallon arfa ƙanwarki ce ta biyu amman haɗuwa muke tare ayi, amman ke sam sedai yau faɗa da wancan gobe tsokanar wancan, hatta ƙofar gida idan kika taho aguje! ta bugeki sekin bita kin rama wannan wace irin rayuwace Bebi?".
Mama takai maganar tana kallonta.
Sannan ta cigaba da cewa..............
"Narasa wannan hali naki jiya haka malam sadi mai kayan miya yazo har nan yana cewa kin buge Æ´arsa harda cewa Wallahi ze kai hukuma dame zanji Bebi".
Takai maganar cikin jin susar rai.
"Lah mama wallahi ƙarya.........., bata bari takai ba ta buge mata bakinta.
"Dan gidanku babbane yake ƙaryar haka na baku tarbiyar ƙaryata babba?".
Takai maganar cikin zafin rai matuƙa.
"Mama nifa bashi zanceba, wallahi salisa ƙarya takemin itace fa kullum nazo wucewa setace min budurwar habu mai itace,nikuma bana so wallahi mama kije ki mata magana idan ba haka ba zan fasa mata kai watarana".
Takai maganar tana turo bakinta waje.
"To maye idan ta gaya miki hakan tunda aishima habun mutum ne, bana son maganar banza maza gama ci ki wuce kitafi makaranta".
Mama takai maganar tana shiga cikin É—akinta.
Tana cin tuwon tana mita tana kuma ayyana yadda zataci uban salisa.
Tana kuma murguÉ—a bakinta kamar agaban salisan take.
Nikuwa nace.
"Hoho Bebi daru kenan".
Tana gama cin abincin ta dauke kwanon takai bakin rariya tare da wanke hannunta.
Aguje ta fita daga gidan tana rungume Æ´ar jakar ledar qur'anin dake hannunta.
Harta ƙarasa makarantar magariban.
Lokacin malam hadi yana tsaye hannunsa riƙe da dorina yana faman jibgar ƴan makara.
Tunma kafin ya ganta ta laɓe a bayan sadiya ƙawarta cikin sanɗa tabi gefe ta saje da ƴan ajin sabida ita aduniya babu abinda taƙi jini kamar adoketa.
Ƙasa ƙasa take raɗawa sadiya labarin irin dukan da zasuma salisa gobe a filin kaci uwaka.
Wanda ita kuma sadiyar take kuma zuga Bebi hartana zata É—auko mata wayar wutar da yayansu yake dukansu da ita.
Sam hankalinsu baya kan malam hadi wanda yake bayani sunata hirarsu yadda zasuma salisa dukan tsiya.........
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.