Romantic Hausa Novels

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 35 of 81

Bebi tana fitowa daga wanka ta shige ɗaki ta kwanta zazzafan zazzabine ya rufeta washegari basu fita tallale ba, haka xalika ɗayan washe garin ma basu fita ba suna gida abinsu wanda zuwa wannan lokacin zazzaɓin bebi yay zafi yaudai mama ta sakata agaba domin suje ganin likita.........

_SAƘON GODIYA GA MASOYANA KUSANI IDAN HAR KUKAGA BANYI UPDATE BA SEDA DALILI MAI ƘARFI AFUWAN JINA KWANA BIYU DA KUKAI SHURU_

*NOTE EDITING AFUWAN FOR THE TYPING ERROS* ðŸ™
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
    {  _HOT LOVE_  }
           

         NA
*AUTAR MANYA*

_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._

                        *54*

Ƙarfe takwas na safiya taiwa su mama da Bebi acikin asibitin shaka tafi na sharaɗa, wajan yankar kati mama ta nufa bayan ta samawa Bebi ɗan dakalin da marasa lafiya ke zama kafin layi yazo kansu.
Kwanciya tai akan dakalin tana cure hijabinta wuri guda, bayan ta naɗe ƙafafuwanta dik ilahirin jikinta rawa yake gawani zazzafan hucin dake fesowa ta jikinta sabida zafin zazzaɓin malerian datake kwana dashi take tashi  dashi acikin ƴan kwanaki biyun nan.
Wajan mintuna goma mama tana tsaye bakin windown da nurse É—in dake bada katin ke ciki, seda layi yazo kanta sannan ta faÉ—i sunan bebi tare dana mahaifinta da shekarunta sannan aka bata katin ta'tawo gaban Bebin ta tsaya tana kiran sunanta.
"Bebi tashi muje can wajan acan zamuga likitan kinji".
Tafaɗa tare da ɗan jan ƙafafun Bebi dasuke cure cikin hijabi kaɗan.
Ɗagowa tai idanun nan nata yay jajur tana kallon mama dasu kafin kuma ta yunƙura ta miƙe tana jawo slipers ɗinta ta zirasu cikin ƙafafunta sannan tabi mama suka tafi wajan bin layin ganin likita.
Nan ɗinma sun ja lokuta masu tsawo kafin akira sunanta yunƙurawa sukai mama ta kama hannunta har zuwa cikin ɗan madai daicin ofishin da likitan ke ciki wadda ta kasance mace'ce taci farin glass tana zaune akan kujera irin mai juya mutane, Sallama mama tayi, Cikin kulawa da mutuntaka wannan likitar ta ɗan zare glashin idanunta kaɗan tana amsawa mama sallamar.
Nuna musu kujerar dake kallonta tayi tare da cewa.
"Bilkisu Musa Ko?"
Bebi ce ta É—aga kanta tana É—an matsawa gaban likitar tare da katin ta a hannunta.
"Bayan zazzaɓi sekuma me yake damunki? Kina ciwon kai? koko amai?".
Likitar ta faÉ—a, idanunta tsaye akan katin tana rubutu cikin sauri biro É—auke a hannunta.
"A,a nidai kawai zazzaɓi nake senaita jin sanyi baya nan bana jin komai".
"Okey".
Likitar ta faÉ—i bayan ta gamajin abinda Bebin tafaÉ—a.
Tajima tana rubutu sannan ta miƙowa mama katin tana cewa.
"Maleria ce ke damunta a daure asai waɗannan magungunan sannan ga allurai nan, daza,ai mata na tsawon kwana uku, Allah ya sawwaƙe".
TafaÉ—a tana É—aga murya tana kiran next daze shigo.
Godiya mama tai mata tare da kamo Hannun Bebi suka fita daga office É—in likitar.
Abakin asibitin mama ta zaunar da Bebi jikin wata bishiya ita kuma ta shiga wani chemist, mintuna biyu tazo da magungunan da aka rubuta musu acikin bakar leda, sannan tasaka bebi agaba suka hau napep zuwa gida.
Acikin napep É—inne mama kecewa Bebi.
"Ga alluran bara mukoma ko asiya Æ´ar gidan malam ya'u muka kira setai miki agida".
"Nidai mama bara kawai nasha maganin base anyi alluran ba, naji sauki".
Tafaɗa murya can ciki tana rawa alamun rashin lafiya, daman can Bebi bata kaunar allura tun tana ƙaramarta, haka xalika koda ta girman ma yanzu bata sonsa ta koɗan.
"Sefa an miki dan bazaki zo tsakar dare ki hanamu rintsawa ba nasanki da É—an banxan rakin ciwo".
Mama tafaÉ—a idanunta bisa kwalta.
"Wallahi mama bazanyi ba nikam banson allura dan Allah mama kar amin".
Mama bata kulata ba tanajinta tana faman rakin magiyar kai ai mata allura amman tai mata fumfuris taƙi tanka mata.
Adai dai bakin layinsu mai napep É—in yatsaya sakamakon dakatar dashi É—in da mama tayi.
Saukowa sukai, mama ta bashi naira saba'in tana mishi godiya, tunma kafin maman ta fito, Bebi tai maza ta sauka cikin sauri tai cikin layinsu sabida gudun kar mama tace su biya gidan malam ya'u ai mata allura.
Tana yaye bugun soro mama na biye da ita kusan atare sukai sallama.
Hassana tana tsakar gida tana É—aurin kayan miya hussaina kuma tana bakin kicin tana É—aurin alalen leda wanda zasuyi shi na abincin ranar yau.
Amsa sallamar sukai sunawa mama barka da dawowa sannan suka juyo sunawa Bebi yaya jikin, da ƙyar take amsawa sabida yadda kanta ke mata mugun ciwo.
Hijabin jikinta ta cire,ta rataye a jikin ƙofar ɗakinsu jikinta sanye da wata doguwar rigar atamfa ko ɗan kwali daman bata ɗauraba, janyo tabarmar gefen da hassana take tayi ta shinfiɗa ta kwanta tana jan numfashi kaɗan-kaɗan ido jawur take kallon mama.wadda itama take kokarin zama agefen hassana bayan ta sauke gyalen jikinta.
"Mama zansha kunun aya mai sanyi".
Tafaɗa tana juya musu baya ta kalli ƙofar ɗakinsu.
"To Hussaina ina ihsan ne ko arfa ban gansuba tunda na shigo, suzo su karmo miki gidan hadiza".
Mama ta faÉ—a tana É—an matsawa gaban Bebi tare da shafa kanta.
"Mama sunje siyo barkono amman bara nina siyo mata".
TafaÉ—a tana tashi daga kan aikinta.
"A,a zauna bara suzo É—in cigaba da aikin gabanki".
Maman tafaɗi sannan ta ɗan ranƙwafo saman bebi tana mata magana.
"Uwata bayan kunun ayan mekuma zakici, nifa wallahi duk kin sakani acikin damuwa sabida ke duk zafin ciwo bakya ƙin kai loma bakinki amman wannan karon ina naga ko ruwa baki shaba ko nama zan siyo miki na dafa miki uwata?".
Mama tafaÉ—a tana É—agota tare da É—orata saman cinyarta.
Hawayene yake faman zubo mata hannunta saman kirjinta.
"Mama nidai kunun aya zansha don Allah".
Tafaɗa muryarta tana rawa, itafa ba xafin ciwon nan ne kaɗai ya hanata cin abinciba harda cin zarafin da wannan guy ɗin yamata wanda take jin mugun zafin abin har bargonta burinta a kullum ta ganshi domin ta rama zagin ubanta dayay wanda yake ƙasa bai taka ba kuma bai zubar ba amman ze zagar abanza.
"To kuma kukan na maye nifa banson ciwo da kuka keda kike jaruma bari suzo su sayo miki kunun ayar yau har kaza xan dafa miki kici ki koshi kinji uwata banson damuwarki".
Mama tafaÉ—a cikin rarrashinta.
Cikin haka su ihsan É—in suka dawo suma da sallama suka shigo gidan sunawa mama sannu da zuwa sannan sukaiwa Bebi yaya jiki.
"Ihsan maza É—auko É—ari a saman madubi kije gidan hadiza ki sayo kunun aya kuna hamsin Bebi na hamsin maza Æ´ar albarkata ki dawo".
Mama tafaÉ—awa ihsan haka wadda ta amsa da to bayan ta mika barkonon hannunta.
Shiga É—akin tai ta É—auko kudin ta fita ita kuma arfa Æ´ar autar mama ta É—auko turmi ta haÉ—a kayan daka yaji tayi hanyar soro domin daka barkonon.
Mintuna kusan biyar ihsan ta shigo hannunta É—auke da jarkar kunun gyaÉ—a har guda biyu, nasu ta mikawa hassana tana cewa.
"Anty hassana ga namu".
Amsa hannasa tai sannan ta mikawa Mama na BEBI.
Tun kafin mama tai magana Bebi ta amshi kunun a hannun mama ta kafa kanta ta shanye tas.
Sannan ta amshi maganin da mama ta ballo mata xata sha.
"A,a keda bakici komai ba ai bakyasha magani ba".Mama tafaÉ—i hakan tana kallon Bebi.
"Nifa mama na koshi kibani nasha wallahi babu komai".
"A,a bazan bakiba ai na É—auka zaki haÉ—a da sauran biredin safene shiyasa na ballosu".
Dole tasa seda taÉ—an cusa bread sannan mama ta bata maganin tasha seta jingina ajikin bango batare data kwantaba.
"Mama É—azu Uncle usman ya kira waya wai kwana biyu bamuje kamfani ba sannan kuma baban nazir ma ya kira shima dai korafin rashin ganin namu ya faÉ—a".
Cewar hussaina wadda ta gama.É—aurin alalen zata É—ora akan wuta.
"Ke rabu dani kozaku koma senan da sati ɗaya haka kafin nan na ƙara jari tunda wannan ɗin muncinye, yaufa inaganin ma shinkafarmu zata kare kuma kuɗin hannuna na kwashe na siyo maganin Bebi".
Cewar mama wadda ta mike xata shiga É—aki.
"Mama Allah ze tallafemu karki damu".
Cewar hassana wadda ta kammala É—aura kayan miyan dake gabanta.
"Hakane daman Allah ya rufa asiri".
Mama tafaÉ—a tana shigewa É—akinta.....................

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.