Romantic Hausa Novels

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 60 of 81

Cikin wannan ƙadamin su kawu rabi'u suka sauko daga cikin adai daita sahu wadda suka ɗoro kawu tasi'u cikinta wanda yake faman surutai kamar wanda ya sami taɓin hankali
"Wallahi bazan basu ladi ba! wallahi bazan basu ladi ba sedai su kasheni sedai suyi dukkan abinda zasuyi"!! Abinda yake faÉ—i kenan tun bayan dasuka daukoshi a mota bayan ya farfaÉ—o daga gajeren suman wucin gadin daya yi awajan É—aurin aure.

Kawu Rabi'u da kawu Sani sune suka riƙoshi shikuma kawu salisu ya sallami mai ɗan sahun daya kawosu sannan suka ƙaraso ƙofar gida anan suka kuma cin karo da tashin hankalin dayafi na wajan ɗaurin auren domin tuni jama'a sun fara taruwa wajan kallon yadda matar kawu tasi'u take zunduma ashariya tana bataga ɗan kan uban daya isa ya ɗaukar mata ƴaba koda kotu ze kawo ba ƴansanda ba babu wanda ya isa ya ɗaukar mata yarinya abawa ɗan giya shi alhaji mai gwall ɗin dan ubansa mai yasa bai tsaya ya bawa ɗansa tarbiya mai kyau ba? ai gashinan ya zama mujiya acikin al'umma ire-iren waɗannan maganganu taketa saki wanda har su tasi'un suka karaso wajan bata dainaba mutan gida masu dariya sunayi masu bata baki sunayi.
Zuwansu kawu tasi'un ne yasa tayi shuru tana aika masa da harara wanda ya watstsake tunda yaga motoci fake a ƙofar gidansu.
Kallon drivern alhaji mai gwall yayi tare da riƙe ƙugunshi.
"Kaima mallam iro dakai za'aci mutuncina? dakai za'a shiga rigar darajata a ƙeta min kana kallo za'a ɗaura auren wancan tsinannan yaron da ƴata ta sunna ka bari?"
Cewar kawu tasi'u wanda ya faÉ—i maganar a gaggauce alamun kamar baya cikin nutsuwarshi.
Murmushi mallam iro yayi sannan ya kalleshi
"Haba mallam tasi'u kamanta lokacin da kake shigewa falon alhaji kaci kasha kana ɓuɗa hanci kai gaka sirikinsa kana mana kallon hadarin kaji koko wannan kayan abincin da aka kawo maka da kayan lefe banda kuɗin da kaci ka tuna damu? base kallon banzan da kake mana ba kai kaga sirikinshi ai gaya nan yanzu ka zama tabbataccen suruki toni shawarata anan wallahi ka tattauro baƙauyar ƴarka kabamu mu wuce da ita sannan kajawa wannan mahaukaciyar matar taka kunne akan alhaji da ɗansa domin wallahi ruwa ba sa'an kwando bane ba, kasan ko wannan ɗan tsakurin gidan da kuke ciki bai isa ya biya alhaji irin dukiyar daka ci masaba sabida haka masalaha ta xama lafiya itace ka tarkata ka bada wannan ƴa kaga ko iya haka kaje kaita neman gafarar Allah akan laifukan ka domin wannan kaɗai isharace Allah ya nuna maka".
Mallam iro ya faÉ—i maganar yana kallon mutan wajan waÉ—anda wasu tuni suka soma yada maganganu akan irin halin mallam tasi'u na son abin duniyar jaraba.
Jin an ambaci sayar da gidansu na gado wanda shi kaɗai ya rage musu yasa tuni kawu sani wanda bai fiye magana a lamarin ba yaja matarshi gefe suka ɗan zanta ta shige gida mintuna uku segata da wata budurwa baƙa ƙirin kamar wadda ta fito daga kwatami ta mikowa kawu tasi'u ita gabanshi.
Kawu rabi'une yace.
"Ke ladi maza shige mota kutafi Allah ya baku zaman lafiya kaima tasi'u tunda an riga an É—aura auren nan kuma ni nai wakilcin komai na auren ai tazama matarshi dan haka kuyi mata addu'a kawai".
Sum sum ladi dataga motoci masu kyau ta rude ta shige bayan mota tana raba idanunta waje kamar wadda akaiwa bushara da hajji.
Tuni driver ya shiga motar yajata da ƙarfi yabar kofar gidan wanda kusan atare babar ladi da kawu tasi'u sukabi bayan motar suna haɗe baki wajan sakin kuka!
Ganin se ƙurar motocin kaɗai a wajan yasa kawu tasi'u ya juyo yana dannawa ƴan uwansa ashar yana haɗasu da jafa'i kala-kala shikuma daga bayanshi matarshi tana sauke mata nata bala'in tana ai dukshi yaja mata.
Rabi'une yay dariya tare da kallonshi.
"Haba tasi'u ai kowa ya ɗebo da zafi bakinshi kana nufin kura da shan duka gardi da ƙwace kuɗi kenan kagama cin arziƙinka muna kallo seɗan abinda ka sammana sannan kuma taka ta shafemu ina sam baze yuwuba duk irin yadda kake cin mutuncin tsire da kaza a titi yana zuwa kunnen mu dan haka kaida ka ɗauko ka kashe da kanka".
Yana gama faɗin haka yasa matansa da ƴaƴansa gaba sukai gida haka sauran ƴan uwan duka sukai gida suka bar kawu tasi'u da matarshi da ɗayar ƴar tasu suna faman koke koke a ƙofar gida.
" *kasan girman Allah bazan yarda ba kaje can wajan wanda ka kaiwa lefen jiya ka amso na haÉ—a da gonata ta gado mu sayar mu biyasu kuÉ—insu mu É—auko Æ´armmu* "
Cewar babar ladi wadda ta saka haɓar zaninta ta face hanci tare da hawayen takaici.
Cikin sauri kawu tasi'u ya saka hannu cikin aljihun wandonshi ya zaro wayarshi lambar wannan mutumin na jiya ya kira wanda yazo jiya ya É—auki kayan lefe akan ze kawo masa kuÉ—in amman tun jiya shuru kuma ya kira layin mutumin bai samu ba yaje shagonsa tun ajiyan yagani a rufe dan haka yanzuma seya kuma kira amsar dai É—ayace is swich off!!
Wayar ya doka da ƙasa yana furta kalmar "innalillahi wa'inna'ilaihirraju'un"!!!...............
*Muje zuwa*.......................

*SharaÉ—a*
Ai tawagar ƴan ɗaurin aure na tafiya maƙota sukace salamu alaikum gidan mama banda jaje babu abinda akewa mama wasu kuma nata mamakin tayaya duka wannan lamarin ya faru mama bata sanar da kowa ba, haka itama iya ta shigo tare da sadiya wadda tun jiya take kuka wai anyi bikin Bebi bata saniba haka iya ta zauna agidan mama har yamma suna mayar da magana mama kam babu abinda bakinta yake se kabbara da hamdala ranta fess sabida tanada labarin dukkan abinda ya faru *wannan shi ake kira da ƙaiƙayi koma kan masheƙiya* sunyi abun ya koma kansu dayake bata da laifi ƴaƴanta ma haka da *Sannu dukkansu zasu girbe abinda suka shuka* har dare iya tana gidan mama sabida yadda gidan yake faman karɓar baƙi ƴan jaje wasu kuma ƴan Allah sanya alkairin auren bebi.

*Yahya gusau mai atamfa esstate*

Tuni bebi ta kusan kammale farfesun dake gabanta hartana shirin zubo na kayan cikin ragon...........
# *Autar Manya*
11/14/21, 3:13 PM - Allah Akbar: *81*

Gefe guda kuma ta tsirawa tv idanu tana kallon labaran safiya wanda ake haskawa a tashar Cnn, tana kallonta tana aika farfesun dake gabanta cikin bakinta hankalinta kwance ita sam bata san wainar da ake soyawa a gidansu ba.
Tana kammale na gabanta ta jawo kular farfesun kayan cikin waÉ—anda su ta É—ibi marar yawa sauran ta tura bayanta tace anjima zata ci, cokali ta saka tacigaba da É—iban romon da É—an kayan cikin tana kaiwa cikin bakinta tana ci tana lumshe idanunta.
Cikin lokaci ƙalilan tagama cinyewa sannan ta miƙe ta gyara inda ta ɓata kana ta koma waje ɗaya ta zauna bayan ta kammale dukkan kulolin waje ɗaya.
Jin cikinta take kamar ze fashe banda ƙamshin kayan haɗin farfesun babu abinda hannunta keyi, can cikin zuciyarta kuwa mamakin tarin dukiya da wadatar wannan gida take jiba gida kamar baza,a mutu ba daman da irin waɗannan manyan gidajen a duniya? lallai inda ranka zakasha kallo ba ɗan kaɗanba, zamanta da kamar mintuna goma bayan kammala cin abincin nata ammi ta kuma dawowa falon.
Cikin nutsuwa ta dubi Bebi tare da ce mata.
"Autata har kin kammala cin abincin kenan?"
TafaÉ—a mata cike da tattali.
Waya kunyace ta rufe bebi sabida ko kusa batai tunanin ammi na iya dawowa a wannan lokacin ba kuma ai da kunya aga ta cinye rabi daga cikin kayan karin da aka kawo mata.
Amman ga mamakinta setaga ita ammin ma sam hankalinta baya kan kulolin yana ga wajanta wadda take tambayarta.
"Eh ammi na kammala nagode Allah ya ƙara girma da ɗaukaka amin".
Cikin tsananin jin daÉ—in yadda yarinyar tayi mata addu'a ammi tace.
"Amin autata nagode to maza taso kije kiyi wanka kinsan babana akwai cida zuci kar yazo yaga bakiyi wanka ba yahau sababi".
TafaÉ—a tare da tashi tsaye ta nufi hanyar bedroom É—inta.
Cikin sanyin jiki Bebi tabi bayanta salo salo tana ƙarewa hanyar wajan kallo tana ƙiyasta yadda aka kar kuɗi a wajan, kana tana mamakin ko ammi batada yara ne taji gidan tsitt.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.