Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 36 of 81
*********************
Cikin nutsuwa yake driving ɗinshi hankalinshi kwance babu wani damuwa acikin ranshi, kai tsaye nasarawa ya nufa can cikin wata anguwa wai ita ƴan majalisu, wajan wani mutuminsa yaje wanda sukai xancen zasu ƙulla wata sabga duk dai akan kasuwancin sane kasancewar shi mutumin, babban ɗan kasuwane wanda baima cika zama acikin garin nan ba, to tuni Ali keson ganin mutumin se saɓani ya shiga tsakaninsu se jiya Allah yay sukai magana ta waya wanda suka aje yau xasu haɗu wajan ƙarfe 8:00am wannan dalilin yasa yay sammako daga gida zuwa nan ɗin.
Abakin gate ɗin gidan mutumin yay parking tare da fito da wayarsa, ya kirashi cikin ƙanƙanin lokaci mutumin ya fito wanda ze ɗan girmewa Aliyu da kaɗan domin shi ze sa'an ya umar, gaban motar Aliyun ya bude ya shiga tare da sallama cikin mutuntaka sukai gaisuwar girma sannan suka soma maganar data shafesu wadda kusan duk akan harkar kasuwancin sune.
Sun kai kusan a wannin biyu sannan sukai sallama Alhaji Aminu wanda Alin yaje wajansa ya fito daga motar shikuma Aliyu yaja motar ya tafi.
Seda ya biya ta wajan Abokan kasuwancinsu na wasu garuruwan da usman ya gaiyata ɗaurin aure to suna nan basu tafi ba, se zuwa anjima wanda usman ya kama musu wani hotel anan dai duk hanyar nasarawar, ya ɗan ɓata lokaci a wajansu suna gaisawa sannan ya kamo hanyar gida bayan sunyi sallama.dasu.
Agajiye ya shigar da motar wajan adana motoci lokacin wajan ƙarfe ɗayan rana dan anata kiraye kirayen sallar azahar a wasu masallatan.
Da harya nufi hanyar sashen ammi seya tuna seya juya ya nufi hanyarshi yanajin ranshi duk babu wani daÉ—i sallama yay a babban falon gidan nashi bayan ya bude kofar falon.
Tsitt gidan yake kamar babu bil adam acikinshi.
Daman ita khadija tunda tai sallar asubahi ta koma ta kwanta bata farkaba seda yayarta anty Ruma, da sauran dangi suka shigo wajan nata sannan ta yunƙura taje bathroom ta kuma gasa jikinta sannan taɗanji dama, kaya ta sauya sannan ta fita falon anan suka gaggaisa da ƴan uwanta, cikin haka ammi ta aiko su hassana da kayan break fast, tare da yayarta da sauran ƴan uwanta waɗanda suke cousins ne sukai break ɗin sannan suka taimaka mata wajan gyara gidan abinda ya dace a fitar suka fidda, har wajan 12 suna gidan sun jima kafin suyi mata sallama akan zasu wuce, duk da yawancin su ƴammatane kuma duk anan gidan suke sedai bam bancin part dakuma ƴar tazarar tafiya.
Seda kowa ya sauka sannan anty ruma ta dawo da baya.
"Dija ina Haidar ɗinne ai ya leƙo mu gaisa dashi tunda yasan ni ba,a nan nake ba, anjima kaɗan abbansu nasma zezo mu wuce".
Rau-rau tai da idanunta.
"Nima ina nasan inda yay"
TafaÉ—awa Anty ruman haka kanta tsaye.
( Take Note: dan Allah ƴan uwa mata ku dinga rufa asirin aurenku ba komai xakana budewa ba dole akwai rufin asiri tare da riƙe sirrin juna sabida kowa yasan mata da miji se Allah, kar ƴan uwanki ko ƙawarki suzo ki kwashe sirrinki da oga na daɗi da rashin sa ki gaya musu sabida gudun husuma Allah rufa asiri amin )
Gyara tsaiwa anty ruman tayi.
"Kar dai kicemin bai ratsaki ba jiya, a ƙa'ida kowani ango yana ririta amaryarsa idan ankawota kada kicemin baki sami hakan daga wajanshi ba?".
Kukane ya tawo mata still tana kallon anty ruma.
"Wallahi anty jiya yaymin cin kaca amman tunda ya sakani acikin ruwan É—umi bai kuma waigena ba, shima kuma nasan dan uwarshi tace yayi ne da baze ba".
Turo É—ankwali gaba Anty ruma tai.
"Aikin banza yagama haukansa dan ubanshi semun saitashi waya gaya mishi É—iyan hajiya rabi suna boranci".
Tana faÉ—in haka ta kwashe da dariya.
"Nifa babban burina ki haihu dashi a farkoma kisami maza Æ´an biyu fatanmu kenan sabida arzkin ya shigo zuri'ar marigayi yusufa mai atamfa amman dan jaraba akaf dangi su kaÉ—aine masu dashi komai sedai su".
Share hawaye khadijan tai.
"Nima dai anty ada bana kawo wannan tunanin wanda umma take nunan amman tundaga ranar da mukai.kamu da kuma jiya dana shigo cikin gidannan naga yadda aka narka dukiyar bati wallahi se komai ya sauyamin tabbas anty zuri'ar abba idiris akwai kuÉ—i wallahi bakiji yadda kaina ya girma ba jiya danaji wai dani aka É—aura auren Aliyu shalelen abba wanda nasan komai na abba Aliyu ne a farko, kai Allah ya saka Alhaji babba acikin aljanna firdausi amin".
Dariya anty ruma tai.
"To ba wannan ba mudai fatanmu kiyi ciki hajiya ki aje komai ki kamashi da kirsa kinsan tafi bin malamai ci a yanzu karki sake ki nuna fushi akansa ki dinga nuna masa kefa sonshi kike kamar ki zauce insha Allah nan da Æ´an satikai zamu somajin kakarin amai".
TafaÉ—a tana buÉ—a!!!
"Anty ammanfa akwai matsala".TafaÉ—a tana kallonta.
"Tame kuma?".
Ruman ta faÉ—i a gajarce.
"Anty inaganin fa wannan infection ɗin bai barni ba, daman nagayawa umma nace mata mu soma maganin sanyi kafin na matan nan amma umma taƙi wallahi jiya tunda ya soma babu wani show se azaba gabana kamar an saka reza yanzu haka ƙaiƙai nakaji".
TafaÉ—a cikin rashin kunya da tsantsar jaraba.
"Wannan babu matsala ki dinga jiƙa kanunfari kina sha sannan xan haɗo miki wasu, daman ai gangancine yanzu ƴammata su fara amfani da maganin mata batare dasun nemi na sanyiba ayayin gabatowar biki,sabida duk maganin matan dazasu sha matsawar sanyi bai kauba tofa akwai case".
Anty ruma ta faɗa tana ƙoƙarin fita daga falon.
"Kindai ji duk huÉ—ubata karnaji karnaga kinji ko?".
Tafaɗa tana fita daga falon ta sauka ƙasa khadijan na take mata baya, ko aƙasan ma sun jima suna tattaunawa anty ruma tana kara hau da ita kan network kafin suyi sallama, akan ragowar zancen sayi a waya, tana komawa samanta kwanciyarta tai, bata tashiba seda akai kiran sallar karfe ɗaya sannan ta mike ta shiga toilet tai alwala tazo tai sallah, sannan ta shirya kanta cikin haɗaɗɗun kaya tai ɓarin turaruka ta xauna gefen gado tana latsa wayar hannunta data ɗauka a gefen madubi.
Jin kamar sallamarshi a babban falon saman yasata ƙara gyarawa sosai, tare da fesa turare cikin yauƙi ta fito muryarta kamar zuma tana amsa mishi sallamar.
Sanye take cikin haɗaɗɗen leshi wanda yaji uban stone har ƙasa anyi mata ɗinkin bubu, bakaramin kyau tai ba, abinka da farar fata, gabansa ta nufa wanda yake kokarin jan handle ɗin bedroom ɗinshi ze shiga, hannunta ta ɗora akan nashi tana ɗan jan gashin saman hannun nashi cike da salo.
"Barka da zuwa my cwt man amman wallahi nai fushi se yanzu ka dawo".
TafaÉ—a a raunane kamar xatai kuka dan tsabar kirsa.
Mamaki yarinyar ta bashi ahaka bazaka ɗauka ko (A)khadija zata iya faɗi ba, idan ka cire tsabar iyayinta wanda tun tana karama take da shi amman seya basar yana mata.kallon ƙasan ido mai cike da izza, aranshi yana jinjina kawaicinta.
Ƙarasa buɗe ƙofar yay ya shiga ta bishi a baya tana ɗan dira kafarta alamun shagwaɓa"baka cemin komai ba?".
TafaÉ—a.
HaÉ—e ranshi yay tamau tare da tsareta da idonshi wanda yay ja kaÉ—an.
"Ina neman afuwanki akan abinda nai miki jiya a ƙa'ida ya dace na zauna na baki kulawa a matsayinki na amarya kuma wadda ta kawo budurcinta cikin daraja, sedai wani uziri daya sha kaina yasa banyi hakan ba, ina fatan zaki fahimceni".
YafaÉ—a idanunshi kafe akanta.
Wani irin sanyi taji har ranta jitake kamar su dauwama ahaka.
"Na yafe maka yayana daman can ban rike kaba".
"Nagode".
Yafaɗi hakan yana nufar ƙofar bathroom tare da shiga ciki ya rufo kofar yabarta anan a dashe.
Cike da ƙwarin gwiwa itama ta fita daga ɗakin tare da shiga kicin domin sarrafa masa abinda zeci...............( Tofa anya khadija xata bar kofar Bebi muje zuwa )
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.