Romantic Hausa Novels

Auren Bare Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Auren_Bare_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 42 of 81

*TAMMAT BIHAMDIHI*

*NAKAWO ƘARSHEN PART ONE CIKIN LITTAFINA PART TWO BAYA DA YAWA SEDAI AKWAI RIKITA RIKITA* 💃💃💃 *WADDA TAFI TA PART ONE*

*SHIN YAYA WANNAN AUREN ZE KASANCE* ?
*INA TARIHIN ALIYU* ?
_HANNUNA YA GAZA GAYA MUKU RIKICIN CIKIN WANNAN LABARIN WANDA KE GABA KUDAI MUJE ZUWA* 💃💃💃💃
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *AUREN BARE !!*🌹
    {  _HOT LOVE_  }
           

         NA
*AUTAR MANYA*

_Alhamdulilahi nagodewa Allah maɗaukakin sarki daya bani ikon gama AUREN BARE BOOK 1 Lafiya yanzu kuma zamu ɗora cikin littafin kashi na biyu na ƙarshe ma'ana book 2 wanda shi bai kai na ɗaya yawa ba sedai rikita rikitar shi tafi ta farko fatan xaku bani haɗinkai kamar wancan ina roƙon Allah yasa yadda na kammala wancan lafiya yasa na kammala wannan lafiya tare da kwanciyar hankali amin_

*HOME OF QAULITIES WRT ASS...*

     _Book 2_          *61*

Rayuwar auren Bebi da Aliyu akwai tsantsar rikici.
Aliyu ya auri Bebi batare da sanin mahaifanshi ba, bayan yariga dayay kwanan sanin Familyn su basa AUREN BARE!
Aliyu yay aure da kwana biyu still yazo ya ƙara wani auren mai cike da rikici, Shin iyayen Aliyu zasu karɓi Bebi a matsayin suruka? shin khadija xata bar Bebi suyi rayuwa da Aliyu? Shin dawace manufa Aliyun ya auri Bebi sone ko ƙi? koko ladabta?
Shin wanene Aliyu tarihin sa dabamu faÉ—a a part one ba?
Ina labarin khaleepha da dangin mahaifin Bebi?
Yaya Bebi xataji idan ta farka taga sadakin Aliyu agidansu a matsayin mijinta? Zata karɓi auren koko zata bijire?
Duka waÉ—annan amsoshin tambayoyin dama waÉ—anda basu faÉ—u ba duk suna cikin AUREN BARE PART 2 wanda ze fara zuwa nan kusa da yardar Allah.

_Assalamu Alaikum my fans fatan kuna lafiya yaya iyalai da komai ina farin cikin sanar daku na tadanar muku dubban abubuwa acikin littafina kashi na Biyu wanda zezo ana kuɗi insha Allahu, ada nai niyyar sakin sa free amman manyan dalilai na yasa na mayar dashi na kuɗi, bayan nasha gwagwarmayar baku page 60 ana kyauta, yanzu kuma ina son ku nunamin tsantsar soyayyarku a wannan labarin nawa kashi na biyu, wanda nai masa laƙani da mai dogon zango domin tafiyar miƙaƙƙiya ce bana son rage muku daɗin labarin shiyasa nace kowa ya biya #200 naira ɗinshi cikin sauki domin mu antaya cikin PART 2 mai dogon zango insha Allahu kuma kunsan rayuwar auren Ali da bebi akwai rikita rikita dan haka my fans muje zuwa_

Wanda ya shirya biyan kuÉ—inshi seya neman tanan.

*08142105218*
_Naira #200/ to 0078174806 starling bank/ evidance of payment via this number 08142105218/ pls banson card only transper sabida card yana min yawa_

*SON SO NAKE MUKU A KAFTA PART MAI DOGON ZANGO* 💃💃💃
11/14/21, 3:12 PM - Allah Akbar: *PART 2*

NA KUÆŠINE

*61*

Cikin sauri ya aminu yabi malam lado cikin gidanshi da É—an gudunshi, dakatawa malam yay ganin aminu a bayanshi yana haki.
"Aminu lafiya naga kana bina da É—an gudu koko wani abunne?".
Rissunar da kai ƙasa yay kana yace.
"Malam munji zancen aurene sama taka shine mukeson jin mike faruwa wallahi bamu da wani labari akan lamarin".
Cikin nutsuwa malam ya dubi Aminu sannan yace.
"Maza aminu kiramin É—an uwan naka kuma kam kuna da hakki yakamata a sanar daku wannan curarren lamarin, Cikin sauri ya aminu ya fita segasu da nura lokacin har malam ya shiga gidanshi ya bawa baba sadakin ta rike mai kana ya É—auko abin zama ya shinfiÉ—a masu a soro.
Zama sukai dukkansu.
Sannan malam ya dubesu.
Tass ya kwashe dukkan abinda ya faru ya sanar musu tare da É—ora musu da cewar ai yanzu aikin gama ya gama tunda an riga an É—aurawa bebi aure sayi da wani kuma.
Sosai wannan lamari ya bawa su ya aminu mamaki amman basu wani ji abin sosai ba sabida daman sun kwana da sanin halin dangin mahaifin su bebin mutane ne masu tsabar son kansu da yawa.
"Kuma dai yakamata kuyi abin da yadace akan maganarku".
Cewar malam yana kallonsu.
Sunkuyar da kai sukai sannan ya aminu ya fara magana dayake shine babba.
"Malam ginin muke son karasawa insha Allahu konan da karshen wannan shekarar ne se ayi kafin nan aikinmu ya samu".
Murmushi malam ya faÉ—aÉ—a kana yace

"Masha Allahu naji daÉ—in hakan sosai Allah ya kaimu lokacin amin".
mikewa sukai suna masa sallama tare da ficewa daga gidan.
Tabarmar ya naÉ—e tare da shiga cikin gidanshi yana wassafawa baba abinda ya faru.
wata buÉ—a baba ta saki tana cewa.
"Aidaman inxaka gina ramin mugunta tofa ka ginashi iya tsahonka ALLAH mungode maka daman indai jinin ka a arziki ike wallahi sekayi Allah daÉ—a suttura".
Tattaunawa sukeyi ita da malam akan lamarin auren har zuwa wani lokaci.
Malam ɗin ya mike ya saɓi babbar rigarshi tare da karɓar kuɗin yana cewa baba bara yaje can gidan maman ƴan biyun.
Lokacin da malam ya shiga gidan mama iya tana zaune akan tabarma tanawa mama faɗan akan me zata ɓoye mata komai ashema basu zama ɗaya ba se yanxu aminu ke gaya mata abinda ke faruwa.
Haƙuri mama ke bawa iya harga Allah itama tasan bata kyauta mata ba ayadda suke amman tsabar ruɗun dasuka shigane yasa batabi takan iyan ba.
Sallamar malam ita ta katse musu maganar tasu.
FaÉ—aÉ—a far'a mama tayi itama kuma iyan haka suna yiwa malam barka da shigowa cikin axama mama ta É—auko mishi sallaya ta shinfiÉ—a masa.
Gaisawa sukai cikin mutuntuka sannan ya dubi mama.
"To Aishatu kiyiwa Allah godiya an É—aurawa balki aure yanzu dan haka maza kiramin ita".
Cikin jin daɗi mama ta miƙe ta shiga cikin ɗakinta.
Lokaci É—aya suka fito da bebi wadda take can karshen gado tana bacci.
Ganin malam yasa ta watstsake tare da tsugunnawa a gefe guda tana gaidashi, se alokacin ma ta lura da iya itama gaisar da ita tayi sannan ta sunkuyar da kanta a ƙasa daman yau ɗin tanajin duk jikinta babu daɗi.
"Balkisu ni wanene a wajanki?".
Malam ya tambayeta cikin tsanaki.
Jimm tayi tana ayyana wannan tambayar tashi acikin ranta kafin taji muryar mama tana cewa.
"Wainikam bada bebi ake magana ba".
Cikin sanyin jiki tace.
"Kakanmu ne kai"
Murmushi malam yay tare da kallon mama.
"Waccan fa?".
Bin idanun malam Bebi tayi kana tace.
"Mahaifiyar mu mana".
"Masha Allahu balkisu nasan yanzu kin wuce yarinya karama kina da hankali kina da nutsuwa kinsan ciwon kanki kuma kinsan inda ke maki ciwo, idan har nida ita mun isa dake kuma muna da mahimmanci wajanki to ki bamu haÉ—in kai akan hukuncin da muka zartar akanki".
Dum! dum!!
Cikin tsoro take Addu'ar Allah yasa ba haÉ—in auren ta da khaleepha akai ba.
Hawaye ne ke kokarin zuba mata amman seta kanne tare da kallonshi.
"Malam babu abinda mama xata cemin nayi naƙiyi indai bai saɓa addini naba, malam koma maye nasan bazaku cutar dani ba tumma kafin naji na amince".
Cikin tsabar mamaki mama take kallon Bebi ta yadda tai maganar ka rantse wata mai hankalin kirkince.
shiko malam murmushi yay kana yace mata.
"Masha ALLAHU balkisu munji daÉ—i Allah yay miki albarka, a sakamakon auren da waÉ—ancan keson yi maki muka duba tsabb muka gano shi kanshi yaron ba É—an mafita bane gefe É—aya akwai karancin tarbiya awajanshi yasa muka yanke shawarar haÉ—aki da wani dafatan kin fahimmata?".
Cikin faÉ—uwar gaba ta É—aga ido tana kallon malam.
Bakinta yana rawa amman takasa faÉ—in komai illa binshi kawai datakeyi da idanunta.
"Mun É—aura miki aure da É—an mafita É—an arxiki kuma insha Allahu baxakiyi nadama ba Balkisu ga sadakin ki yau nina É—aura miki aure da saka hannun mahaifiyarki".
Cikin rudewa take share hawayenta bakinta ya gaza furta kowacce kalma malam mama iya babu wanda yace gada wanda aka É—aura auren sedai sun bita d idanunsu suna kallon yadda take kuka kamar ranta ze fita.
"Balkisu ko baki na'am ba mu warware?".
Cewar malam.
"A,a malam karku warware koma waye shi naji xan zauna dashi akan na zauna da khaleepha nagode da karamcinka nagode nago......
Bata karasaba ta mike bata bi takan sadakin ba tai É—aki tana kuka kamar babu gobe.
Murmushi malam yay tare da mikewa batare daya dauki sadakin ba.
"A,a malam ka rike a hannunka har zuwa lokacin da komai ze warware mungode Allah ya basu zaman lafiya amin".
Cewar mama tana kallon malam.
"To ba matsala Allah rufa asiri zuwa gobe seta tawo nan wajena in yaso shi mijin nata ya karbeta a hannuna koya kuka ga?".
Iya ce tayi magana anan wajan.
"Hakan yafi malam komai kai dai daine babu abinda xamu ce maka se godiya mungode Allah ƙara girma".
Fita yay.yana musu sallama.
Sosai iya da mama suke maida zance akan lamarin auren har zuwa lokacin da rana tayi kana sukai sallama iya ta wuce gida.
Ƴan biyu suna ɗaki dama a tsakar gidan daga mama se iya dan haka iya na tafiya mama ta mike tayi cikin ɗakin...

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.